New Post

Sunday, 18 December 2016

HARAMTACCEN ZAMA 19-20

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  19-20

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

  Cikin jin haushi tace, "Anma dai in ba'a kawoni da ɗaki a gara ba an kawo ni da cous-cous ko?"
    Baiko ɗago ya kalleta ba Yace "Anma a gidana kike zaune, indai zaki zaunamin a ɗaki, dole ne kimin girki, bayan wannan babu wani abu" ba tace mishi komi ba ta koma kitchen ɗin don yanzu batason magana tayi nisa tsakaninsu yanzu zasu fara faɗa.

Bayan wata biyu...
   Majeeda ce sanye cikin doguwar rigar material, ta ɗaure kanta da ɗan kwalin, ta jawo Abayarta har k'asa ta saka, sannan ta ɗaura nik'ab a fuskarta, ta janyo hand bag ɗinta sannan ta fito waje. Driver nanan yana jiranta, ta buɗe sit ɗin baya ta zauna yaja motan sai ALQALAM UNIVERSITY dake cikin garin katsina.

   Kullum shigarta kenan tunda ta fara shiga makarantar, kamar wata matar aure shiya saka har yanzu batayi koda k'awa babu ruwanta da kowah.
      Sai marece sosae ta koma gidan, bata lura da motanshi ba ta saka kanta cikin falon, maganganu ta fara jiyowa.
     "haba Aisha, ba nace karki zomin gida ba? Karki manta fa akwai banbanci tsakanin gidanmu da gidana".
   "akwai banbanci, anma kasan ko inane zan iya zuwa don in ganka, tunda kai ba son zuwa gidanmu kake ba"
     "naji, anma kincemin inzo banzo ba? Ki k'ara hak'uri mana lokaci kaɗan ya rage a fara maganar aurenmu"
    "kullum haka kake cewa, ni dai tunda nazo ka bari ko gaisawa muyi"

Wani abu ne ya tsaya ma majeeda har wuya, kamar ta kama majeeda ta shak'e takeji, a ciki-ciki tayi sallama ta shiga ɗakin duk suka juyo suna kallonta, ta k'urama majeed ido kawai, taa daɗe bata ganshi ba, don tunda ya fara zuwa aiki ya daina zaman gida, girki ma idan taayi a kitchen take bar mishi.
   taa rigashi ɗauke idanunta, ba tare da tace komi ba ta shige ɗakinta.
      Ibraheem ya faɗo mata a rai, yanzu yaa daina kiranta, ko kiranshi tayi sai yaga daman ɗagawa, koya ɗaukama bazasu wani daɗe ba zai kashe wayan, shiyasa itama ta daina damunshi, yanzu hankalinta akan karatun kawai ta maidashi.

   Cikin ɗakinta haushin Aisha ne kawai ya cika mata ciki, daganan tana jiyo maganganunsu tak'i tashi ta tafi duk da maganar da majeed ke mata, tashi tayi ta tafi falon bayan ta cire hijabin jikinta, ta gyara ɗaurin kwallabin sannan ta fito.
    Shiru suka k'arayi suna kallonta, ita kam kamar ma batasan dasu ba, ta k'arasa gaban kallo ta kunna, ta rik'o remote ɗin ta zauna kallo.
      K'asa-k'asa Aisha taci gaba da mishi magana duk hankalinshi na kan majeeda, ta k'ure k'arar ma yanda bazasu ji ba, duk a takure yake anma Aisha taa kasa ganewa, kawai ya juya zai tafi ɗakinshi itama ta mik'e zata bishi.

Majeeda ce tasha gabanta,
       "kinfa fara wuce iyaka malama, don tsabar rashin kunya ki biyo mijina har gidana, kinga ban tanka ba shine zaki bishi har ɗaki, ubanme zaki yo a ciki?"
   "Akan mijin da bai damu dake ba baya sonki kike tada jijiyoyin wuya? Abinda ranki ya baki shi zamu yo"
    "k'arya kike wallahi ki shigo har gidana kina faɗamin magana, banza mai k'wak'war namiji har gidanshi, ai naga mugun son da yake miki ne ya saka sai dai ke ki biyoshi"
    "laaah, ni kike faɗa ma magana? Kana jinta fa majeed"
       
Duk suka maida kallonsu ga majeed ɗin, "Da bakizo gidanta ba taa faɗa miki? Kinga muje in maida ke gida"
       Majeeda tsayawa tayi tana kallonsu har suka fice, lallaima yaa fifita wannan banzar a kaina kenan, har saida ta jiyo ta mata gwalo, haushi kamar ta fasa ihu.
    Lallai don yaga yanzu babu aurenshi a kaina ne harda shigomin da wata a gida, wallahi bazan yarda ba nima sai na rama.

   Bai wani daɗe ba ya dawo, anan ya wuce ta inda ya barta, ya wuceta inda take tsaye yana tafiya da kakkausar murya cikin gargaɗi yace, "babu ruwanki da kowacece zatazo wurina, babu ruwan wani da harkar wani" ya wuceta sannan ya k'arasa maganar.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts