💖HARAMTACCEN ZAMA💖
♠♠♠♠♠♠♠
27-28
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari...
Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Sauri tayi ta tashi zaune, ciwon cikin ma taa daina ji.
"ki tashi kiyi break fast"
"Yaya majeeed me kakeyi har yanzu ba nasha maganin ba?"
"eeh anma ai bakici komai ba, donma kin samu an nuna miki kulawa?"
"naji anma dai ka fita zansha"
"indai kinason in fita sai kinsha koda tea ne, ko so kike a fara cewa ban kula dake?"
"wama zaisan banda lafiyan? Nidai nagode hakanan"
"Yanzu wani yasan ciwon ciki kike me zasuyi tunani?" yaja tsoki, itama shiru tayi bata k'ara cewa komi ba.
Bai hak'ura ba saida ya haɗa mata tea, sannan ya fita "Gobe in Umma ta k'ara tambayanki kice ban kaiki asibiti ba ko ban kula da cin abincinki" yanayin yanda yayi maganarne ya sakata murmushi, ko umma ce ta mishi magana?
Bai k'ara shigowa ɗakin ba, da rana yunwa ta isheta, gashi duk jikinta babu k'arfin da zata ɗaura girki, kuma tea yaa isheta hakanan, hakanan dai ta fito da nufin shiga kitchen ɗin ko zata samu abinda zataci.
A tsakiyar falon suka haɗu da plate a hannunshi shak'e da yankakkun fruit, ta ɗan kauda kanta zata wuce.
"ban ɗauka zakici abinci ba shiyasa na taho miki da fruit kawai" ta juya zata tafi
"shima na k'oshi fa" ta koma zata tafi, "tohh me kikeso a anso miki?" "ba komi fa" taci gaba da tafiyarta, rik'o hannunta yayi, tana niyyar k'wacewa suka jiyo sallamar Aunty zainab tana shigowa ɗakin da sauri ya saketa.
Kamar ta koma a ranta tace nifa shiyasa banson zuwa gidan yara, majeed yace, "sannu da zuwa Aunty" ta amsa tana niyyar zama
"Aunty kizo shigo daga ciki mana," ta matsa daga wurin Majeed suka wuce ɗakinta tare da Aunty zainabu" bayan sun zauna ne Aunty zainabu dai ta gaji da kallonta ganin dai k'arfin hali kawai take.
"Anma dai baki lafiya ko?"
"eeh anma naa warke"
"me akace yana damunki?"
"A'ah bamuje asibiti ba, ina dai jin...."
"kinajin me Majeeda? Zaki zauna da laulayi ne bazakuje asibiti ba kamar dai wacce batayi karatu ba?" maganar Aunty ma dariya ta bama majeeda,
"Aunty ciki kuma? Nikam kowah ma ya samin ido dole ne daga mace tayi aure sai haihuwa? Nidai ulcer tace ta ɗan tashi"
"ba dole bane anma don me ake auren? Karma ki fara sanyama ranki wannan, ni ba gashi ina jiran haihuwar ba Anma har yau Allah bai nufa ba"
"ni Aunty kima daina maganar nan"
"saboda me?" ta tsareta da kallon tuhuma, ta kasa magana, sai ga majeed yayi sallama ya shigo.
Suna gaisawa da majeed, Majeeda ta mik'e, "Aunty me za'a girka miki?" "kinga basai naci komi ba daman a hanya nake, garin damuna k'ara in sauri in wuce" cikin wasa majeeda tace "Aunty ko ruwa dai aka fara ai a gida kike, kuma dai yaune zuwanki na farko", "ina laifi ma da kika ganni?" majeed yace "ba laifi Aunty anma mudai yini mukeso" daria tayi sukaci gaba da fira harda majeed, sai da ya fita sannan ta jawo ledar magungunan mata masu kyau ta mik'a mata tana mata bayaninsu.
Saurarenta kawai take, ita dai ba buk'atarsu gareta ba, babu amfanin da zasu mata sai dai tayita ajiya kar tak'i amsa Aunty tayi tunanin wani Abun.
Aunty Zainabu bata daɗe ba ta tafi, Majeed ma lokacin ya bar gidan.
5:00...
Taji dai yunwar tak'i saurara mata, tun safe fa tea kawai tasha, daurewa tayi ta shiga kitchen ta fasa k'wai dai dai cikinta ta soya, sannan ta zauna falo ta cinyeshi tas tasha ruwa, sannan ta fara jin kanta.
Sai dai me, kamar abinda ciwon cikin ke jira kenan, tun kafin ta tashi daga wurin mararta ta fara wani azababben ciwo, dak'yar ta iya kai kanta ɗaki.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment