New Post

Sunday, 18 December 2016

HARAMTACCEN ZAMA 21-22

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  21-22

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

   Kwana biyu tayi tana tunanin yanda zata rama abunda Majeed ya mata anma taa gaza samun mafita, gashi kullum sai ya raba dare kafin ya shigo gidan, tunda safe kuma yake fita, ita yaa maida ita er gadin gida duk da baiyi mata shamaki da fita ba.

   Yauma da marece sosai ta dawo daga lecture, suna hanya drivern ta ya ɗaukota, da yake hanyar gidansu majeed ne, hakanan taji tanaso taje gaishe dasu, ta cema drivern ya biya da ita.
    Ya ajjeta ta fito har zata tafi kuma ta dawo "malam balah zaka iya tafiya, zan ɗan daɗe ne" yace, "tohh hajia" sannan ta shiga gidan da sallamarta. 
     Zahra taci karo da ita, aikam ta buga uban tsalle da gudu ta taho rungumeta "Oyoyo Matar Yayanmu"
     "Aifa sis kamar a bakinki aka raɗa wannan suna, ina umma?"
    "tana ciki ki shiga bari inzo"
     "tohm naa bari".

Ta yaye labulen ɗakin Umma ta shiga haɗe da sallama, ta ɗago tana amsawa tana ganin Majeeda ce ta k'ara faɗaɗa fara'arta tana mata sannu da zuwa, sai yanzu ne ma wata kunya ta k'ara nannaɗeta, ta duk'a har k'asa tana gaida Umma ta amsa mata.
      "Ina majeed ɗin ko ba tare kuke ba?"
    "Daga makaranta ne yace Driver ya kawoni, anma zaizo ɗaukana Umma"
     "Tohh Allah kawoshi lafiya, kuna dai zaune lafiya ko?"
     "Alhmdlh Umma"
  "ki faɗamin gaskia dai naaga duk kin rame" wai taa rame fa, tace a ranta, tana tuna randa taje gida momie cewa ta dinga yi taayi k'iba taayi haske, alamar dai tana mata zargin ciki ne da ita, da yake momie ce sai ta ce mata "momie ni kece uwah ta farko da akama ɗiyarta auren dole kuma tazo ganin gida a ce mata tayi k'iba" momie tace "watau ma auren dole aka miki ko? Kina nufin har yanzu baku zaman lafiya da mijin naki?" tace ma momie, "ba haka nake nufi ba momie".

      Umma ce ta katse mata tunani "Yadai kikai shiru Majeeda? Indai da matsala ki faɗamun in tsawata mishi"
     "ba wani matsala Umma, kawai kwana biyu banji daɗi bane" ta k'ak'alo k'arya.
   "tohh Allah ya k'ara lafiya kundai je asibiti ko?"
   "Ai naaji sauk'i Umma"

     Zahra ce ta shigo ta janye ta suka koma can ɗakinta da fira, itama tsokanarta take kodai sun samu rabo,
    "nikam sis kamar Abinda kowa ke jira kenan, duka yaushe aka gama hidimar bikin ko hutawa bamu yi ba?"
       "Abinda kowa ke jira mana kenan, in hutawa ne kam ai kinyi, anma burinsu Abba kenan kullum ganin en jikokinsu"  sai da gabanta ya faɗi, tayi shiru tama rasa abin cewa, tohh ta inama zata samu cikin tunda ba auren garesu ba?.

   Haka ta yini cikin gidan duk tayi sukuku kuma, har bayan isha'i taa rasa yanda zata tafi kuma gashi tace ma Umma Majeed ne zaizo su tafi, yanke shawarah tayi kawai ta kira malam balah, shi ɗinma ta dinga kiranshi anma wayanshi a kashe.

Wurin 9 Umma ta lek'o ɗakin Zahra, "wai ina majeed ya tsayane?"
        "Umma inajin dai wani abunne ya rik'eshi, anma zan tafi kawai kar dare yayi sosai"
    "A'ah ya zaki tafi ke kaɗai? Ki mishi waya dai yayi sauri yazo ku tafi" ita kam ko number wayarshi ma bata da, yama za'ayi yazo ɗaukanta.

   Har 10 tayi ta rasa dabarar da zatayi tabar gidan Umma, su duka suna zaune a falo, gabanta sai faɗuwa yake, tun farko ma meya sakata yin k'arya.
      Sa'a tayi wayarta ta fara ringing, tayi saurin maida wayan silent sannan tayi kamar taa ɗauka sannan ta ɗan matsa daga inda su Umma suke ta fara magana yanda zasuji.
     "hi, lafiya lau ya aiki?" ta ɗanyi shiru sannan tace, "A'ah ya za'ai na tafi kace na jiraka?"
     "Ayyah! Tohh a dawo lafia, sai ka dawo gidan" tun kafin ta zauna Zahra tace "Halan ina ya tsaya?"
      "wai kinji fa gaisuwar wani baban ɗan wurin aikinsu sukaje Mashi, anma suna hanya kuma motan a cike take, yace inje a napep" Umma tace, "Ayyah!Allah yaji k'an musulmi, sai kiyi sauri dare na k'arayi, tace "tohh shknan Umma"

Zahra ce ta rakata har bakin titi, sun daɗe suna tsaida abin hawa duk da mutane a ciki gashi batason hawan mashin, dak'yar suka samu wani mai napep ta shiga sukayi bankwana da zahra.
    Har ya tada zai tafi Yace "hajia ina za'a kaiki?" tace, "G.R.A"
     "kiyi hak'uri hajia bazanje can yanzu ba ina ɗan sauri ne" babu yanda ta iya ta fito daga motan gashi dare ya fara nisa 10:3., ta juya ko burbuɗin Zahra babu, ga unguwar babu mutane.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • A YINI ƊAYA 13-14[8:20pm, 27/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 11-12[11:36pm, 23/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 15💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹             &… Read More
  • A YINI ƊAYA 19-25[10:42am, 13/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 16-18[4:45pm, 2/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts