New Post

Monday, 19 December 2016

HARAMTACCEN ZAMA 25-26

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  25-26

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

    Da Asuba, ciwon mara ne ya farkar da ita, tun cikin barci ta fara juye-juye harta farka, ta dafe cikinta ko motsi batason yi, tanason ta ɗauko maganinta anma ta kasa tashi saboda yanda ya matsa mata.
      Dak'yar ta samu ta mik'e ta jawo jikkarta ta fara laluben maganin sai dai kwalinshi babu ko ɗaya, kamar ta fasa kuka ga wani irin azababben ciwo, haka tana duk'ewa ta samu ta haɗa ruwan zafi a toilet taje tayi wanka anma duk da haka kamar ana k'ara tunzuro ciwon cikin gashi ita kaɗai a ɗaki.
     Dak'yar ta iya k'arfin halin kwaso kuɗi a jikkarta ta fito mai gadi ya siyo mata, da yake a ɗan duk'e take tafiya rik'e da cikinta ga azabar ciwo, bata lura dashi yana shigowa falon ba ita kuma zata fita harta kusan kai mishi karo, da sauri ta dawo da baya, kanta a k'asa tabi gefenshi zata wuce, shima gefen da zata wuce yabi suka kusan haɗewa a tare, kuma kowannw ya koma ɗayan gefen, da suka kasa wucewa dai ya saka hannuwanshi biyu saman kafaɗarta, sannan ya juyar da ita ya wuce.

    Wani irin murɗawa cikinta yayi anan ta duk'e-duk'e rik'e da cikinta, ta daɗe a haka kafinta iya mik'ewa tana ɗagowa suka haɗa ido da majeed, duk ta daburce tace, "yadai?" yaɗan saki fuskarshi "ba komi", sannan ta juya ta wuce a wahalce.
     Bata iske mai gadi ba, da alama bai gidan gashi duk taa gama jigata, haka ta lallaɓa ta koma ɗakinta, tana faɗawa gado ta saki kukanta marar sauti ga ciwon sai k'aruwa yake, ta dinga murgina saman gado harta sauko k'asa.

    "Ga maganin" taji ya ambata, ta ɗaga fuskarta tana kallonshi rik'e da laida a hannu, ya ajje robar faro da cup a kusa da ita, ta mik'a hannu ta ansa maganin, irin wanda takesha ne da pad guda biyu, ta ɓallo guda ɗaya ya mik'a mata cup ɗin ruwa ta haɗiye dak'yar sannan tace "na gode" ta koma ta sulale k'asa tana jiran ciwon ya lafa, a haka barci ya kwasheta duk taa k'udundune wuri ɗaya.
    Tausayi ta bashi ganin yanda tayi kwanciyar duk taa takura, lokaci ɗaya har taayi ramar dole, sai lokacin ya tuna ko break fast batayi ba ya bata magani, da sauri ya tafi kitchen ya ɗauko flask da kayan tea ya ajje mata.
     Tananan kwance inda ya barta tana barci, anma da alama batajin daɗin barcin ciwon cikin ma bai gama sakinta ba sai rumtse ido take tana rik'e ciki.
        Bazai juri ganinta a k'asa ba, ya saka hannu ya tallabota, kamar yaa ɗauka jaririya, ya dire ta saman gado, tun lokacin da yaa ɗaukota ta farka, anma ta kasa buɗa idonta wani irin kunyarshi maa takeji.
   Megasa Yaya majeed zaina taɓani koya manta yanzu babu aure tsakaninmu? tunaninta ya katse saboda yanda mararta ta k'ara juyewa, tai wani irin k'ara batasan lokacin data k'ank'ame hannunshi da hannu ɗaya ba, ɗayan hannunta na rik'e a cikinta har lokacin da yake yana tsugune saitinta.
   Wani irin tausayi take bashi ganin yanda takeyi, fuskarshi kamar zai tayata kukan, ya kalli hannunta dake sak'ale a nashi, zara-zaran yatsunta masu kyau sosai da taima ado da jan lalle, baisan sanda yaci gaba da murzasu a hankali ba yana kallon kyakkyawar fuskarta, sai runtse ido take, ga ciwon ciki, ga wani irin yanayin da takeji hannunta rik'e a hannun majeed.

   Kallonta yaci gaba dayi, sai yanzu ne yake k'are mata kallo, ya saka hannu ya yaye mata yalwataccen gashin kanta mai sulɓi daya rufe mata fuska, fara ce tas, irin farinnan mai kyau, gashin girarta gazar-gazar mai kyau kamar an zana mata shi, gata da manyan idanu masu kyau da ɗaukar hankali, girar idonta bak'a wulik koda a rufe suke idanunta k'ara kyau suke, da dogon hancin ta wanda ya dace da kyakkyawar fuskarta, idanunshi ne suka sauka a kan ɗan 'karamin bakinta (pink lips), ya tuna yanda take motsashi idan tana mishi masifa, sai yaji ta burgeshi ma idan suna faɗa kyau yake mata.
   Yanzunma motsashi ta dingashi kamar zata tashi, dimples ɗinta na lotsawa, a hankali yakai ɗayan hannunshi zai shafi gefen fuskarta, kamar ance ta buɗa ido, ya sauka cikin nashi da sauri ya mayar da hannun

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts