New Post

Sunday, 18 December 2016

HARAMTACCEN ZAMA 17-18

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                 17-18

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

  Shirun da Ibraheem yaji tayi ya saka ya dinga "hello, masoyiyah, kina jina?"
      "ina jinka masoyi zan kiraka yanzu," sannan ta katse kiran tana k'ok'arin dai dai ta nutsuwarta.
   Ta kalli majeed tana mayar mishi da irin kallon da yake mata "Meya shigo dakai ɓangarena? Ka mantane sharaɗinmu na babu wanda zai shiga harkar wani? Kuma bazaka zo inda nake ba"
     "ke har kina da bakin magana? Baki manta da sharaɗinmu ba meyasa kike k'ok'arin faɗa mishi sirrinmu?"
         "ni ban faɗa mishi ba ko kaaji naa faɗa?"
   "kina shirin faɗa dai, wannan ba k'aramar magana bace da idan kin faɗa ma wani yaɗuwarta bazai kawo matsala ba, har yaushe kike tare da Ibraheem da kika yarda dashi har zaki faɗa mishi wannan sirrin namu? Ke kin kasa rik'e sirrinki ta yaya kike tunanin wani zai rik'e miki? Wallahi karki kuskura ki faɗa ma wani wannan maganar"

   Jikinta yaa riga da yaayi sanyi, taama kasa maida mishi, ya juya ya bar ɗakin, taja tsoki "daman gulmace da sa ido ya shigo dakai kenan" ta harari k'ofan tana murguɗa baki kamar yana ganinta, sannan ta tashi ta shige ɗakinta.

   Yinin ranar bak'i ta dingayi masu zuwa ganin gidan Amarya, kowah yazo sai ya zagaya gidan ana lellek'a ɗakunanta, ba k'aramin haɗuwa da tsaruwa gidan yayi ba, ga dukiyar da iyayenta suka zuba mata a ciki.

  Ba ita ta zauna ba sai 9 na dare bak'inta suka gama tafiya, duk taa gaji ga yunwa bata samu taa girka komai ba, baba haule dai taa koma gida,
     Kwanciyah tayi ta jawo wayarta miss calls ɗin Ibraheem ne babu iyaka, itama ta kirashi bai ɗaga ba, ga yunwar dake yatsina mata y'an hanji, mik'ewa tayi kawai ta nufi kitchen ta ɗaura girki, da yake an haɗa mata komi.

   Fried cous-cous ta dafa dai-dai cikinta, sai k'amshi ne ke tashi, tananan tsaye harya gama dahuwa ta sauke ta jawo plate zata zuba kenan ta juyo wayarta na ringing a ɗaki, ta ajiye da sauri ta tafi ta ɗauka wayar.
   Ibraheem ne, ta zauna gefen gado sannan da ɗaga kiran.
     "Da fatan ma'abociyar kyakkyawan murmushin nan tana cikin nishaɗi"
   "sosai tunda ina tare da muryan masoyinah"
     "kawai ɗazun ina cikin ɗokin jin albishir daga gareki, saiki yankemin waya, halan angonki ne ya kiraki?"
      "shiya shigo dai, anma ai bai isa don ina waya dakai in katse saboda shi ba"
   "Hmm, kin manta da mijinki ne? Kina kulawa dai don baniso muna shiga hak'k'ik aure da yawa" sai can ya tuna kuma.
       "Yauwah aurenki yanzu ma... me kike cewa?" sai da ta ɗan daburce duk taa rasa me zata ce sannan tace "yanzu ne yake k'ara damuna masoyi, anya bazamu gudu muyi aurenmu?"
    "Aure akan aure kenan? Nifa banda matsala da iyayena Masoyiyah jiran fitowarki kawai nake, basai mun gudu ba kinji tawan"
     "tohh" kawai tace mishi a zuciyarta tunani take anya bazata faɗa mishi ba? Kuma sai taji tsoran kashedin da Majeed yayi mata haka kawai ta fasa faɗa mishi.

Majeed yana ɗaki shima babu inda yaje, sallah ce kawai take fiddashi, sai juyi yake akan gadonshi saboda yunwar da yakeji tunda rana, daya juya sai yayi tsaki "Yanzu mutum ya tafi restaurant yana haɗuwa da idon sani akama yi mishi surutun ya fara fita cin abinci"

    Gani yayi zaman bazai mishi ba, ya tafi kitchen ya duba ko zai samu abinci.
    Cikin sa'a kuwa ya hango tukunya saman cooker gas, ita ya fara buɗawa, abinci ya gani kuwa da zafinshi k'amshi sai tashi yake, ya jawo plate ɗin daya gani a wurin ya juyeshi tass sannan ya fito falo ya zauna ya fara ci.

Sai da ta gama wayanta da ibraheem daman yunwa duk taa addabeta, ta fito ta wuce shi a falo ta nufi kitchen ko kallon inda yake batai ba, shima ko sanin taa wuce baiyi ba.

Ta duba inda ta ajiye plate babu, kodai bata ɗauko ba? Ta janyo wani plate ɗin dai ta taho zuba abinci, tana buɗa tukunya wayam babu komi, fiddo idanu tayi waje cikin mamaki ta ɗauka tukunyar tana girgizawa kodai bata gani dai dai bane, anma wayam babu komai.
   Toh waye zai shigo har gidanta ya kwashe mata girki? Kodai aljanu ne, can ta tuna fa ay ba ita kaɗai bane a cikin gidan, toh shi kuma mezai dameshi da girkinta? Tunani dai ta dinga yi taga bazai mata ba, ta fito daga kitchen ɗin can ta hango shi ya saka plate a gaba yana kwasar girki.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • ABDUL WAHAB 10ABDUL WAHAB 10 ©Rabiatu Sk msh           ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION Sauke numfashi Abdul yayi sannan ya jingina da kujera, wayarshi ya ciro ya fara neman raheem, tun k… Read More
  • ABDUL WAHAB 6ABDUL WAHAB 6 ©Rabiatu sk msh~           ®NWA Tunda suka fito sadeey bakinta bai qarayin shiru ba, sai yaba kwalliyan Abdul d'inta take, hotuna kam taayi mishi ba adadi d… Read More
  • ABDUL WAHAB 7ABDUL WAHAB 7 ©Rabiatu SK msh        ®NWA Da sauri Abdul ya kashe wayarsa, duk ya tsure cikin duhu yake ma khady alamar ta taimaka mishi, tayi sauri ta danna wayarta tayi kamar ita aka … Read More
  • ABDUL WAHAB 8ABDUL WAHAB 8 ©Rabiatu SK msh           ®NWA Kauda fuskarshi yayi gefe, nan take yanayin khadija ya canja ba tare da taace mishi komi ba ta juya tabar wurin, da sauri yab… Read More
  • ABDUL WAHAB 9ABDUL WAHAB 9 ©Rabiatu sk msh           ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION Tun daga ranar kullum Abdul neman hanyar da zai 'kara ganin khadija yake, gashi cikin rashin sa'a Ya… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts