💖HARAMTACCEN ZAMA💖
♠♠♠♠♠♠♠
11-12
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari...
Ilileee
Sai dare Driver yazo ɗaukanta, Zahra ta rakota har wurin motar. Zata shiga kenan idonta ya hango mata Majeed babu nisa da inda take, shida wata yarinya da alama zance suke, aikam dariya ta fara harda rik'e ciki. Zahra ta fara dudduba jikinta tasan halin Majeeda da dariyan mugunta tace "wai meya baki dariya haka?" ta buɗa baki zata yi magana ta k'ara kwashewa da dariya. Zahra tace "wai miye haka?" ta soma k'ulewa, shima Majeed yana jiyota hankalinshi duk ya dawo kanta sai aika mata da harara yake ta cikin duhun, dak'yar tana rik'e cikinta tace "Abin da ya bani mamaki na gani, wai mace da zuwa wurin namiji zance".
Zahra ta sassauta murya tace "don Allah ki daina mana, kin san dai halin Yayanmu yanzu ya taso kuyi tayi, itama budurwarnan tashi ce da shegiyar k'wak'wa".
Tun kafin ta gama magana Majeeda tace "barni in faɗa wallahi, an daiji kunya mace da zuwa zance wurin namiji, ko meye ma abun so anan?"
Cikin faɗa ya taso inda take kamar zai shige mata, zahra harta ɓalla da gudu cikin gida, itama shigewarta tayi cikin mota da sauri kafin ya ida isowa tace ma Driver ya tada su tafi. Sannan ta lek'o da kanta da k'arfi tace "kayi kai kaɗai, da wannan marar aikinyin da take biyoka har gida, wlhy k'arama tun wuri ki canja masoyi wannan ba abinso bane" sannan suka wuce nan suka barshi yana cizon yatsa data gama gaggaya mishi maganganu kuma bai mata komi ba.
Har dare idan ta tuna ita kaɗai sai ta dinga daria, koda suna chatn da Ibraheem sai da Yace mata "wai ya na ganki yau kina cikin farin ciki?" Tace "Ay kullum ma cikin farin ciki nake da annashuwa indai ina tare dakai"
Yace "Hakane Masoyiyatah, anma da alama farin cikin naki na yau yaafi na kullum" tace "hakane fa, wlhy wani abune ya bani daria, anma dai bazaka tambayeni ko miye ba?"
"ko ban tambayeki ba nasan zaki faɗamin ba?😉
"hakane Masoyi, anma ka share kawai"
"na share Masoyiyah, bani labari"
"ba labari sai dai na zuciyatah"
"shi nafiso masoyiyah, bani labarin soyayyatah a cikin zuciyarki"
Anan suka bar maganar, suka ci gaba da firarsu kawai, anma idanta tuna abinda taima Majeed sai ta dinga dariya ita kaɗai, kafin shima ya tashi ramawa.
***
Sun gama fira da Ibraheem yayan k'awarta kuma saurayinta, fito ta rakashi har gaban mota suna fira kamar karsu rabu.
Daddy ne ya shigo ya kallesu Majeeda sai k'yalk'yala daria take, tana ganin haka tayi saurin shanye dariyarta ta dai-daita nutsuwarta, ibraheem ya fita har inda daddy yake ya duk'a ya gaisheshi, sama-sama ya amsa sannan ya wuce cikin gida.
A sanyaye Ibraheem ya koma wurin motarshi ya shiga, ta rik'e k'ofar motar duk taa marairaice fuska ganin canjawar yanayinshi.
Sai ga motar Majeed taa shigo gidan, ta ɗaga kai kawai sannan ta maida hankalinta wurin Ibraheem.
Zuwa yayi har inda suke sannan yayi parking motar ya fito, zai wuce Ibraheem ya mik'a mishi hannu suka gaisa sannan yayi gaba yana cewa...
"yau naaga nacin zance, saurayi na zaune saman seat ɗin mota don tsabar baiji da mace zai barta tsaye tana shan gajia" ya wucewarshi kawai.
Tasan da ita yake, kawai dai bata son ta tanka mishi a gaban Ibraheem ne ya sakata sharewa, ba daɗewa ta sallami Ibraheem sannan ta shige gidan, ɗakinta kawai ta wuce donma karsu k'ara haɗuwa, bata sanma sanda yabar gidan ba.
Da safe taje gaishe da Daddynta, harta taso zata tafi ya tsaida ita, ta koma ta zauna kanta a k'asa gabanta naa faɗuwa.
"ɗazu wanne yaro ne yazo gidannan?" sai da ta ɗanyi shiru sannan tace "Yayan k'awata ne Daddy"
"Yayan k'awarki kuma meya kawoshi gidannan?" shiru ta k'arayi har saida ya k'ara maimaita tambayarshi sannan tace "ba komi fa Daddy".
Yace "ina fatan hakanne, domin kuwa naa riga dana miki miji" da sauri ta ɗago da fuskarta "miji kuma Daddy?"
"k'warai ma kuwa, idan ma bakisan ko wanene ba yanzu zaki sani, domin kuwa tun kina k'aramarki mukayi ma Mahaifinmu Alk'awarin haɗaku aure da Majeed"
Wani irin zabura tayi "Majeed dai Abba? Ni wallahi bazan aureshi ba, na rantse bani sonshi" yace "tohh naji baki sonshi, tashi ficemin daganan, maganar aure tsakaninku dai babu fashi" nan ta k'ara fasa wani kukan, ta tashi ta nufi ɗakinta har tana tuntuɓe a hanya faɗi take ita wallahi bazata taɓa aure Majeed ba.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment