💖HARAMTACCEN ZAMA💖
♠♠♠♠♠♠♠
7-8
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari...
Ilileee
WANI LOKACI KAFIN AURANSU...
Alhaji Sani da Alhaji salisu, y'an uwane dake matu'kar son junansu da son zumunci, kaka Abdul hameed shine mahaifinsu mahaifiyarsu khadija taa rasu da daɗewa, shi kaɗai ya rage musu shiyasa suke matu'kar ji dashi.
Alhaji sani wanda suke kira da Abba, kuma mijin Umma, yana da yara biyu, Abdul majeed wanda aka saka ma sunan kaka, da kuma 'kanwarshi zahra.
Sai Alhaji saleesu shima Yara biyu ne dashi duk mata, Aunty zainabu wacce ta girme musu su duka, da Autah khadeeja (majeeda) itama sunan kakarta ne da shiyasa ake ce mata majeeda.
Tun haihuwar majeed, kaka yake matu'kar ji dashi saboda sunanshi da aka saka mishi ga yaron shiru-shiru da saurin shiga rai, babu ruwanshi da hayaniya sai dai baison raini, kusan kullum suna gidan kaka shida Aunty zainabu da ta girme mishi da shekara 3.
Aunty zainabu nada Shekara 10, majeed nada shekara 7, k'anwarshi fatima zahra tana da 2years, aka haifi majeeda, iyayensu sunyi matu'kar murna sosae, bama kamar da tun bayan haihuwar zainabu basu k'ara samun haihuwa ba sai akan majeeda.
Ranar sunah aka saka ma jaririya suna khadija, anma za'ana kiranta da majeeda, kaka yaji daɗi sosai kasancewar sunan matarshi ne aka saka mata, tun a ranar ya k'udurta wani abu a ranshi, tsakanin takwaranshi majeed, ta takwarar matarshi majeeda.
****
Aunty zainab ce ta fito da shirin fita, taci kwalliya da goyon majeeda a bayanta, ta samu momie zaune ɗakinta tana kallo.
Tace "momie zamu tafi" momie tace "tohm a dawo lafiya, a gaida kaka Alhaji" zainab tace "zaiji momie" sannan ta fito har driver ya fito da mota, ta shiga sannan ta kwance goyon majeeda ta rungumeta ya tada mota sai gidan kaka.
Tana shiga da sallamarta, Abdul majeed dake zaune kusa da kaka ya amsa mata yana "oyoyo Aunty zainab" kaka daya cika baki da dambun naman da ƴaƴanshi suka kawo mishi Yace "Allah yasa da matata kikazo mun zainabu" tace "ni baka ma son ganina kenan sai wannan tsohuwar matar taka?" kaka Yace "Ai kinsan dolene naji da deeje, kedai kwantota ki mik'omin itanan mu gaisa" ta mik'a mishi ita majeed duk ya haɗe rai.
Tana hannun kaka sai mutsilniya take irinna jarirai tana ture majeed ta k'afarta, haushi ya kamashi ya rik'o k'afafunnata ya ri'ke, kaka ya lura dashi tun haihuwar majeeda ba wani son ganinta yake kusa dashi ba .
"majeedar zaka ɗauka ne?" saurin girgiza kai yayi.
Kaka Yace "haba takwarah na, ina lura dakai fa tun haihuwar ɗiyarnan ba son zuwa kusa da ita kake ba"
Majeed ya k'ara ɓata rai Yace "Ay nifa babu ruwana da ita kaka, tun haihuwarta ka daina ji dani da taazo sai dai kayita ɗaukanta, ko gidansu mukaje da ummana sai tayita ɗaukanta"
Kaka Yace "kai bakaso ana ɗaukar matar taka ne?" da sauri yace "ni ba matata bace, bani sonta" shiru kaka yayi bai k'ara cewa komi ba.
Kiran sallahn da akayi ne ya saka zainab ta fita ɗauro Alwala, kaka ya mi'ka ma majeed ita yace "ri'keta tohm inyi sallah" kamar bazai amsheta ba, sai da kakanma ya kwantar mishi da ita sannan ya fita alwala.
Kaka na tsakar yin alwala, zainab na shirin shiga ɗakin suka jiyo majeeda ta k'wala wani uban kuka, da gudu zainab ta k'arasa shiga ɗakin ta iske bakin majeed dai-dai k'afarta ya gartsa mata ciwo da sauri ya ɗago.
Ta tsaya tana kallonshi "meka mata majeed?" ya fara kame-kame "wallahi Aunty zainab babu abinda na mata, ita keta kukanta tana halbina da k'afafunta" tace "tohh ka ɗauketa ka rarrasheta mana" badon yaso ba, ya ɗaga ta sama duk da ba wani k'warewa yayi da ɗaukan ba, aykam saitin bakinshi ta dalalo mishi tumbuɗi.
Baisan sanda ya saketa ba saida ta kusan faɗowa zainab ta ri'kota ya fita da gudu yana kakarin amai, sai da suka nutsu suka dinga mishi daria.
Haka rayuwar majeeda da majeed take tun suna k'anana, tun lokacin data fara tafiya data samo abun ɓarna saita nufeshi ta k'wala mishi, shima haka indai daga shi sai ita ne ya dinga mintsininta kenan, kwata-kwata basu zama wuri ɗaya.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment