New Post

Sunday, 18 December 2016

HARAMTACCEN ZAMA 15-16

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                 15-16

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

Ci gaban labari
    A hankali majeed Yace "miye mafita? Nifa tsakanina da Allah bazan iya zama dake a matsayin mata ba" tace "nima haka wallahi, kuma indai zamu zauna a inuwa ɗaya sai munyi faɗa" yace "hakane ya zama dole musan abunyi" tace "tohh me zamuyi?"

    Yace "mu rabu kawai kowa yayi sabgarshi, tunda kowa ɓangarenshi daban" ta zaro ido "idan fa suka gano?" yace "tohh waye zai faɗa musu? Kinga saima in samar miki admission kici gaba da makarantarki" tace "hakane tohh sakeni"

    Ba wani tunani ko damuwa a fuskarshi Yace "na sakeki saki ɗaya" itama ba da wani abu a ranta ba tace "saki ɗaya ai ana komawa" kafin ta rufe "baki yace "na sakeki saki biyu" tace "ai wallahi saki biyunma ana komawa, ka cikashe kawai" Yace "na sakeki saki uku.

    Wani ihun daɗi ta saki saboda tsananin farin ciki, ta tashi tana tsallen murna, harta tafi ta dawo.
       "Anma babu ruwan kowa da harkar kowa? Babu aurenka a kaina, babu faɗa a tsakaninmu, ko nuna iko da shisshigi" yaja tsoki yana juyar da fuska
      "ke duk wannan ya dama, salon kuma shegen surutunki ya kai ki faɗa ma wani"
     "Anma haka zamu zauna ba tare da kowa ya sani ba?
       "nafa gaji da ganinki wurinnan malama, babu abinda ke tsakanina dake, ki ɓacemun da gani"

Kamar ta maida mishi da bak'a, ta tuna idan tayi hakan faɗa ne zasu ci gaba, ta taɓe baki kawai ta shige ɗakinta, cikin ɗokin ta kira ibraheem ta faɗa mar.
     Kiranshi ta dinga yi anma tak'i shiga har ranta ya soma ɓaci don yanda ta k'agara ta faɗa mishi tasan sai yaa fita murna, cikin haka sai ga kiran hafsatul kiram babbar Aminiyarta kenan.

  "Ran Amarya ya daɗe tare dana angonta"
   "wacece Amarya? Yanzu duk k'wak'warki dai bazaki kirani da wannan sunan ba" inji majeeda.
     Bayan hafsatul kiram tayi dariya tace "Tohh ina angon naki? Na kasa hak'ura ne na kira ki, duk da nasan kunanan tare yana jinya" ta faɗa cikin tsokana don tasan zata k'ular da majeeda.
    "banson iskanci fa hafsa, ina auren yake da har zai samu zuwa kusa dani ma?"
   "saman kanki mana, da aka ɗaura miki jiya".
     "tohh wallahi na saukeshi yanzunnan, karma ki ɓatan rai ina cikin farin ciki?"
     "kamarya majeeda?" ta faɗa da mamaki"

Da yake majeeda ta yarda da hafsatul kiram sosai, kuma tasan duk rintsi bazata taɓa faɗama wani sirrinta ba, kuma tana cikin son ta faɗa ma wani, nan take ta kwashe komai ta faɗa mata.
   Shiru tayi kamar wacce tayi suman zaune sai da majeeda tace "ko kin kashe wayar ne?"
   "kin kashemin bakin magana dai? Yanzu auren naku kuka kashe a washe garin amarcinki? Kuma zaku zauna a gida ɗaya? Haba majeeda kamar dai....."
      "kinga rik'e mamakinki da duk maganganunki, da kuma sirrina, kinsan don na yarda dake ne na faɗa miki ko? Babu wani abin dana sanin insha Allah"
   "Allah ya yarda, anma duk kin sakemin jiki"
   "tohh a warware lafiya, ki gaishe da Ya umar" bata jira me zata ce ba ta kashe wayar.

  Layin ibraheem taci gaba da neman, sai sintiri take a tsakar ɗakinta, can taji taa fara ringing, ta samu kujera ta zauna tana jiran ya ɗaga anma har ta katse shiru.
    Sai da ta mishi kira biyu ana ukun ne ya ɗaga da alama barci ya tashi.

   "na kwanta barci da tunaninki, banyi mafarkin komai ba bayanki, gashi na farka da zazzak'ar muryarki, plz in fara jin sautin lallausan murmushin masoyiyah ta" sai da ta mishi murmushin sabo da yanda kalamanshi suka mata daɗi tace, "ba murmushi na kaɗai zaka farka dashi ba, harda Albishir ɗin da zaiyi maka daɗi sosai"
  "faɗamin da sauri masoyiyah, tunda kafin ki faɗa ga tukuicinki" ya sakar mata daddaɗan kiss a kunne

Ta rufe ido ta buɗe cikin nishaɗi, "Yaimin daɗi sosae masoyi, karfa ka sakani mantawa da albishir ɗin"
     "sai in k'ara miki wanda zai saka ki tuna"
  "banma manta bafa, anma duk da haka naa biyoka bashi, yanzu miye yayi mana katanga da zama mallakin juna?"
     "Auren ki da majeed mana" inji ibraheem
    "tohh k'ara kwantar da hankalinka, don indai aurena ne yanzu....."

Maganar ta mak'ale mata saboda ganinshi tsaye a k'ofar falonta, yana wurgo mata wani mugun kallo

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MARYAM KO MARYAMA 21-40[10:39, 3/10/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣Soyayyar whatsapp❣ @OHW 21-30 Tana bude datar messages da yawa suka shgo mata, anma naashi ta fara dubawa, da wayarta glaxy s5 wadda Abokinta A… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 21-40[10:39, 3/10/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣Soyayyar whatsapp❣ @OHW 21-30 Tana bude datar messages da yawa suka shgo mata, anma naashi ta fara dubawa, da wayarta glaxy s5 wadda Abokinta A… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 61-80[14:07, 3/12/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 61-70 Maryama ce kwance tana chat da abn qaunarta wani irin farin ciki takeji dk sanda suke tare, murmushi tayi tace Ma… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 41-60Rabiatu sk novels [11:59, 3/11/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 41-50 Washe gari yaa kama ranar monday, suka shrya maryam da maryama suka fito zasu tafi school, Mary… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 21-40[10:39, 3/10/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣Soyayyar whatsapp❣ @OHW 21-30 Tana bude datar messages da yawa suka shgo mata, anma naashi ta fara dubawa, da wayarta glaxy s5 wadda Abokinta A… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts