New Post

Wednesday, 28 December 2016

HARAMTACCEN ZAMA 41-42

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  41-42

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

     Suna shiga mota kamar ya mata magana kuma ya fasa, sai da suka shiga gida ya bita har cikin ɗakinta, ko a lokacin jikinta a sanyaye yake.
   Ya tsuguna inda take ya ɗaura hannunshi a saman gwiwoyinta, ta zuba mishi ido tana k'ok'arin kauda damuwarta.
    "kina tsoran za'a iya gano HARAMTACCEN ZAMAn da muke ko?" ta ɗaga mishi kai,
   "toh waya sani bayanmu dazai iya faɗa musu har su gane? Wannan tsoran naki ne da shakku kawai matsala na, plz ki daina kinji" tayi murmushi saboda yanayin daya k'arasa maganar,
     "na daina masoyi, kawai gabana ne yake ta faɗuwa"
    "ki manta komai a ranki mana, banason abinda zai rabani dake"
    "nima hakan"

Bayan wani lokaci...
SO DA SHAK'UWAne (Amrah A msh) kullum ke k'aruwa a tsakaninsu, wani kulawan sai tsakanin Majeed da Majeeda, komai a tare sukeyi, tarairayarta yake sosae kamar k'wai ɗaya a cikin miya, baya shakkar nuna mata soyayyah a gaban kowa, soyayya suke irin babu irinta a duniya,
     Majeed ne ya fito da shirin fita, yasha kyau cikin farar shadda, yana tsaye yana saka agogo itama ta fito da mayafinta,
    "tohh saina dawo masoyiyah, mezan zo miki dashi?"  ta mak'ale kafaɗa kamar wata k'aramar yarinya,
   "nifa da gske bazaka barni ni kaɗai ba"
   "haba tawan, ya za'ai naje wurin ɗaurin aure dake?"
    "tohh ka fasa zuwa mana"
   "Ɗaurin Auren Abbakar ɗin?" ya faɗa yana zaro ido,
    "inkin yarda dai na kaima Aunty zainabu Ajiyanki" ta ɗan saki fuskarta,
    "Anma bazaka daɗe ba?"
  "da an ɗaura aure zan dawo"
    "tohh shkenan muje"

   Suka fito tare, a hanya suna tafiya tana tsaidashi, komai ta gani tanaso ya sai mata, kwaɗayi dai kala-kala shi kuma ya dinga biye mata,
     A k'ofar gidan Aunty zainab ya ajeta, ta sauka sannan ta lek'o tagar da yake,
    "saika dawo," ta mishi kiss a gefen kumatu
    "tohh babe, saina dawo" ya ɗaga mata hannu yana fara'a, saida ta shiga gidan sannan ya tafi,

   Tana shiga Aunty ta taso da fara'arta tana mata oyoyo, ta zube saman kujera, Aunty ta kalleta da mamaki,
    "Halan a gajiye kike?"
  "A'ah aunty, yunwah dai"
Aunty ta zauna kusa da ita,
     "ya gidan naku?"
   "lafiya lau Aunty" sannan ta gaisheta, duk ba yanda Aunty ta saba ganinta ba,
   Ta jawo ledanta ta fiddo Apple ta faraci, sai dafe kanta take,
    "Aunty nace inajin yunwa, ko saina nema abincin?"
   "Tohh ay naga daga gidanki kike, kuma baki sanar dani zaki zo ba"
   "ni ban tsaya na k'oshi ba, ganin zan fito"
    "tohh ay yanzu zan ɗaura na dare" ta mik'e tana dafe da kanta,
    "nidai bazan jira ba Aunty, bara na dafa ko cous-cous ne"
    "sai dai indomie"
  "tohh yana iya" ta nufi kitchen ɗin, indomie ɗinma saida ta rumurmutsi wata taci hakanan kafin ta dafa, ko dahuwa bata k'arasa ba ta juyeta ta fito,
    Aunty nanan inda ta barta, ta fito tana tafiya tana rik'e kanta, ga wani irin tashin zuciyah da takeji idanta shak'i k'anshin indomie ɗin, ta daure dai ta zauna, Aunty tace,
   "wai lafiyanki?"
  "wlhy Aunty ciwon kai nake fama dashi kwanannan, da jiri" taje zata zauna, jiri ya kwasheta ta kusan faɗuwa da sauri Aunty ta taso zata rik'eta, ta daure ta ajje indomie ɗin,
    "Wai yadai majeeda" sai dai kawai gani tayi majeeda ta sulale a wurin,
   Aiko duk ta rikice, ta shiga kiran layin mai gidanta muhd anma yak'i shiga, ta kira layin majeed, taa kusan katsewa ya ɗauka,
    "kayi sauri kazo yanzu majeeda ba lafiya, kayi sauri plz" bata jira me zaice ba ta katse,
  
   Shima jin muryarta a rikice, duk hankalinshi ya tashi, bai tsaya sallama ta kowa ba ya shiga motanshi ya nufi gidan Aunty, tafiyar mintuna kaɗan ya kaishi gidan,
    Ganin halin da Majeeda take ya sakashi k'ara ruɗewa,  baisan sanda ya saka hannu ya ɗauketa ba, Aunty ta biyosu a baya suka wuce Asiti sai kwarara gudu yake, ikon Allah ne kawai ya kaisu,

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • ABDUL WAHAB 19ABDUL WAHAB 19 ©Rabiatu sk msh            ®NWA Bayan an gama sanya mata kaya a mota, fatyma kaasa rakota tayi saboda kukan tausayinta, kamar wacce zata bar garin, so… Read More
  • ABDUL WAHAB 21ABDUL WAHAB 21 ©Rabiatu sk msh            ®NWA Kuka ne yaci 'karfin khadija, duk taa tada mishi hankali a rud'e yake cewa ki fad'amin mna, da'kyar ta iya bud'a baki … Read More
  • ABDUL WAHAB 20ABDUL WAHAB 20 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Sanyashi tayi a gaba ta tsura mishi ido, don shima taaga alamun chanji tare dashi, hajia tace "Ka d'ago kanka magana zamuyi … Read More
  • ABDUL WAHAB 19ABDUL WAHAB 19 ©Rabiatu sk msh            ®NWA Bayan an gama sanya mata kaya a mota, fatyma kaasa rakota tayi saboda kukan tausayinta, kamar wacce zata bar garin, so… Read More
  • ABDUL WAHAB 19ABDUL WAHAB 19 ©Rabiatu sk msh            ®NWA Bayan an gama sanya mata kaya a mota, fatyma kaasa rakota tayi saboda kukan tausayinta, kamar wacce zata bar garin, so… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts