💖HARAMTACCEN ZAMA💖
♠♠♠♠♠♠♠
5-6
©Rabiatu sk msh
®NWA
©Rabiatu sk msh
®NWA
Washe gari tunda safe baba haule tana gama haɗa musu break fast ko tsayawa karyawa batayi ba ta fita ta tari napep sai gidansu Abdul majeed.
Har lokacin 'yan biki basu gama tafiya ba anata hada-hadar haɗa musu break, baba haule ta raɓa ta gaishe su sannan ta wuce ɗakin Umman Majeed.
Tana falon d'akinta tana waya cike da kwanciyar hankali da alama mai wayan tana tayata murnar bikinne, sai data gama wayar cikin fara'a suka gaisa da baba laure.
Umma tace "Anma dai baba haule lafiya da sassafennan" kanta a 'kasa tace "Rashinta ne ya tado dani tunda sassafennan, don jiya bamu yi barci da kwanciyar hankali ba" Umma ta 'kara sassauta murya cikin tashin hankali tace "meya faru baba haule?" gyara zama tayi ta faɗa mata duk abinda ya faru.
Ran Umma ya ɓaci sosai ta fara faɗa "lallai yarannan anyi mararsa mutunci, mu zasu bama kunya? Ana tunanin in anyi auren zasu daina faɗa anma suyi biris da maganarmu! Bari inje in samu Alhaji in faɗa mishi"
Baba haule tace "tohh shikenan hajia ni daman gani nake tun wuri gara a raba auren nasu tunda basu so, kar wata rana a wayi gari sun kashe kawunansu ma"
Umma tace "su kashe kansu mana, ya fiye mana dai da ace su ba 'kananan yara ba sun sanyamu karya Alk'awari" baba haule tace "tohh Allah dai ya kyauta".
Koda Umma ta jema Abba da maganar shima faɗa ya dingayi, ya ciro wayarshi ya kira 'kanenshi mahaifin majeeda ya sanar mishi, shima faɗa ya dinga yi suka ce su haɗu gidan, bazasu yarda yara su maidasu k'ananan mutane ba harsu tada Alk'awarin mahaifinsu.
Majeeda ta fito daga wanka, tana shafa mai ta jiyo k'arar motoci, da sauri ta zura doguwar riga ta fito daga bangarenta jin kamar maganar mahaifanta.
Hangosu tayi kuwa kowannensu fuskarshi babu walwala, gabanta ya faɗi tabbas akwai matsala, a sanyaye ta fito daga ɗakinta kamar marar gaskia, ta samu wuri ta rakuɓe tana gaishesu.
Umma kawai ta amsa mata, sai ga majeed ya fito da shirin fita, shima saida gabanshi ya faɗi ganinsu su duka a falon, a sanyaye kamar ita shima ya koma gefe ya zauna 'kasa, shi baima samu kowa ya amsa mishi gaisuwan ba.
Shiru ɗakin yayi na 'yan mintuna sannan Abba Yace "sannunku kunji, sannunku da abinda kuka aikata" duk suka k'ara sunnar da kawunansu kamar mararsa gaskiya.
Abba Yace "Tohh wlhy ku buɗe kunnuwanku kuji, ku baki isa ku maidamu k'ananan yara ba, mune nan mu muka haifeku, Alk'awari muka ɗaukar ma mahaifinmu kuma akanku bazamu karyashi ba wallahi"
Daddyn majeeda Yace "in banda shirme da shiririta irin nasu ai idan ana shiga kabari a fito tohh za'a aurennan a kwance"
Abba Yace "bawai kunga daman muna ɗaga muku k'afa ba, tohh wallahi kuka kuskura kuka raba aurennan sai dai ku nemi wasu iyayen badai mu ba" duk suka ɗago a tare suna kallon Abba.
Daddy Yace "wallahi nima ba a gidana ba, kuma zan tsine miki ne duk ranar da kika k'ara faɗa da mijinki"
Umma tace "ita kaɗaice mai laifin? Baza'a ɗaurama ɗiyata laifi ba a barshi ga k'wareta, nima kau ina shirin tsine mishi duk ranar daya k'ara dukanta"
Gaba ɗaya komi ya kwance musu, sauraren iyayensu kawai suke har suka gama faɗansu suka tafi babu mai wani kuzarin magana duk sun kasa motsawa daga inda suke, har iyayen nasu suka tafi.
Sunfi rabin awa babu wanda ya motsa daga inda yake, babu wanda ya cema kowa wani abu, duk wani kuzarin dake jikinsu ya saki.
A hankali majeed Yace "miye mafita? Nifa tsakanina da Allah bazan iya zama dake a matsayin mata ba" tace "nima haka wallahi, kuma indai zamu zauna a inuwa ɗaya sai munyi faɗa" yace "hakane ya zama dole musan abunyi" tace "tohh me zamuyi?"
Yace "mu rabu kawai kowa yayi sabgarshi, tunda kowa ɓangarenshi daban" ta zaro ido "idan fa suka gano?" yace "tohh waye zai faɗa musu? Kinga saima in samar miki admission kici gaba da makarantarki" tace "hakane tohh sakeni"
Ba wani tunani ko damuwa a fuskarshi Yace "na sakeki saki ɗaya" itama ba da wani abu a ranta ba tace "saki ɗaya ai ana komawa" kafin ta rufe "baki yace "na sakeki saki biyu" tace "ai wallahi saki biyunma ana komawa, ka cikashe kawai" Yace "na sakeki saki uku.
Nikam mamaki ne ya kamani da wannan ɗanyen hukunci da suka yanke a tsakaninsu, anya kuwa zaman nasu zai yiwu a haka?
Kafinnan waye Abdul majeed? Wacece majeeda? Menene tarihin auren nasu? Idan kuka biyoni a sannu zan warware muku🚶🏻♀🚶🏻♀
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment