New Post

Wednesday, 15 February 2017

SANADIN K'IYAYYA 19-20

♠SANADIN K'IYAYYA♠
            (︶︿︶)
                 19-20

©Rabiatu sk msh
            NWA

K'ARSHEN PART ONE

  Kallonta yake sai faman girgiza kai yake yana hawaye, duk hak'urinshi da kauda kai a abu yau saida ta sakashi kuka, bai taɓa tunanin k'iyayyar da take mishi yakai haka ba,
   Ganin kallon da yake mata ya saka ta ɗaura wuk'ar a hannunta ta lumata sosae anma bata yanka ba,
   "Kamar baka yarda da abinda na faɗa maka ba," da sauri ya nufo inda take cikin tashin hankali, kafin ya k'araso taa jaa wuk'ar ta yanketa sosae jini ya fara zuba, sannan tayi saurin ɗaurata a mak'ogwaranta,
   "karka kuskura ka k'arasomunnan, kana k'ara saka k'afarka wallahi saina aikata abunda na faɗa"
  Yaja baya ya tsaya, kuka kawai yake kamar k'aramin yaro, gaba ɗaya ya tsani kanshi, ga jini yana zuba a hannu da goshinta anma babu damar dazai taimaka mata,
  Ta k'ara ɗaura wuk'ar a wuyanta,
    Yayi saurin mik'a hannunshi kamar zai rik'eta duk da nesa suke, muryarshi na rawa,
   "Shikenan Aleesa, shikenan zan fita, don Allah karki yanka" ya faɗa yana jaa da baya, sai kuka yake,
  A haka yabar ɗakin, sannan ta sauke hannunta, ga zafin da hannunda ta yanka yake mata, ga jinin dake zuba har a goshi, wani irin jiri takeji, anan ta sulale ta kwanta,

****
Saukar ruwan data fara ji a fuskarta ne, ya sakata buɗe ido a hankali, gaba ɗaya kanta yaa mata nauyi dishishi take gani, a hankali ta k'ok'arta ta tashi zaune, sannan ta ɗaga idonta taga waye a kanta?
  A razane ta k'arasa buɗe idonta tana kallonshi,
    "Ɗan sanda kuma? Waya kawoshi?" ta fara k'are ma ɗakin kallo cike yake da en sanda, ga Daddynta tare dasu da mahaifin Kabeer,
   Ta mik'e tsaye tana tunanin meya kawosu? Bakinta ma ya kasa furta komi, Ganin yanda Daddy ya haɗa kai da bango yana kuka sosae abinda bata taɓa gani ba, ga wani irin kallon tsana da Mahaifin kabeer yake mata,
   Ta mik'e tsaye dak'yar, sannan ta hango mutum kwance cikin jini, ga wuk'ar data gama mishi barazana da ita jiya nan an yayyankeshi da ita sannan aka luma mishi a ciki, jikinta na kyarma take kallon gawar Kabeer harta kusa faɗuwa,
   A hankali ta nufi inda gawar take shi ɗinne dai, ta ɗago fuskarta maganarta ma dak'yar take fita,
   "Daddy waya kasheshi?" a zuciye yakai mata wani wawan mari da har saida ta rasa jinta na wani lokaci,
   "Akwai sa'anki anan ciki da zaki maida mu wawaye? Kin cuceni, kin cuci kanki Fatima (ya faɗi sunanta na gaskia), bazan taɓa yafe miki ba akan hakan" da sauri ta rik'e baki,
    "Na shiga Uku Daddy don Allah karka tsinemun, wallahi bani na kasheshi ba"
    "kina tunanin akwai sakaran da zakima wannan maganar ya yarda dake? Ai kin faɗa da bakinki Aleesa, idan kinje can station kin musu bayani, kuma daga yau karki k'ara tunanin kina da wani uba a duniya"

Hannu biyu ta ɗaura saman kai tana kuka "Naa shiga uku ni Aleesa me yake shirin faruwa dani?" maganganunsu da Kabeer ne na daren jiya suka ringa faɗo mata, Sharrin da take niyyar k'ulla mishi sai gashi ya dawo a kanta, tasan idan duk duniya zata taru babu wanda zai yarda da ba ita ta kasheshi ba, shiyasa idan zaka gina ramin mugunta ka yishi gajere, ita dai ga abunda SANADIN K'IYAYYA ya jawo mata, da kuma illar auren dole,

Waya kashe kabeer? Shin Hadid ne ko kuma shida kanshi ya kashe kanshi don ya maida ma Aleesa abunda tayi niyyar mishi? Ko kuma wani ne can daban? Aleesa ta kasheshin da gaske? Wanne hali zata shiga gaba? Ina labarin ɗaukar fansar hadid?  Tambayoyi da yawa.... Ku biyo ni a Part 2 don jin amsoshinsu, wanda ni kaina a yanzu ban sani ba saina koma  ɗauko rahoto😳

Alhamdulillahi,
   Godiya ga Allah (S.W.T) daya bani ikon kammala wannan tak'aitaccen littafin, kuskuren dake ciki Allah ya yafe mana,

   SADAUKARWA
wannan tak'aitaccen labarin sadaukarwa ne hazik'an marubutannan, MRS UMAR, da kuma MAMAN ADNAN (ummieluff), Allah ya k'ara basira, Ameen

RAZ
A friends like you can never replace, deep in my heart you will always stay, Allah ya barmu tare cikin haɗin kai da k'aunar juna, Ameen😍

Ina godia ga duk masoyana, da kuma makaranta littafinnan, Allah yabar k'auna, ga wanda ke neman part one ɗinnan daga farko zasu iya dubawa a blog ɗina

  www.babymsh.blogspot.com

Gaisuwa da jinjina ga dukkan marubuta Online, Allah ya k'ara basira, Ameen

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts