New Post

Wednesday, 15 February 2017

SANADIN K'IYAYYA 13-14

♠SANADIN K'IYAYYA♠
            (︶︿︶)
                 13-14

©Rabiatu sk msh
            NWA

Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan

www.babymsh.blogspot.com

  Kwana biyu anata shirye-shiryen biki, duk yanda Aleesa taso a janye maganar aure anma babu mai saurararta, duk irin tijarar da take sauke mishi, harce mishi tayi H.I.V ne da ita, anma ya nace shidai sonta yake,
   Ana gobe ɗaurin aure dubara ta gama k'are mata, ga k'iyayyarshi dake k'ara yawaita a zuciyarta, ji take kamar ta haɗiye zuciyah ta bar mishi duniyar duk don tsanar data mishi, wayarta ta ɗauka ta tura mishi text kamar haka,
   Zagi sosai ta dinga mishi harma da wanda batasan anayi ba, sannan ta k'ara da cewa "Wallahi idan har bazaka janye maganar aurennan ba nice zan zama ajalinka, k'ara in kasheka nima a kasheni, da inyi zaman aure dakai, banza mai naci kawai"
   Wayar na hannun wani Abokinshi text ɗin ya shigo, ya bala'in tsorata da kalamanta, a rikice ya nuna ma kabeer message ɗin, murmushi kawai yayi cikin nuna rashin damuwa,
   "wannan ba sabbin kalmomine dana taɓaji daga bakin Aleesa ba, ballantana su tsorata ni, barazana ce kawai, da kuma yarinta dake damunta"
   "Yarinta kuma kabeer? Yarinyar da har degree taa gama kacemun wani yarinta, kada fa So ya rufe maka ido ka kai kanka a halaka, wlhy bazan taɓa yarda tunda ta furta komai zata iya aikatawa, yanzunnan zan samu su baba k'ara a janye maganar aurennan, tunda dai iyakar k'iyayya taa nuna maka, "  da sauri ya fara k'ok'arin tsayar dashi, anma bai saurareshi ba ya fita da wayar a hannu,

****
Tana kwance bayan taa gama tura mishi text ɗin, kanta ne ke mata ciwo bayan kukanda takesha kullum, ga kuma zullumin da take ciki na auren kabeer, gobene kuma lokacinda Abba ya bata zai cika, sai dai a ɗaura masu aure kawai,
   Sak'one ya shigo wayarta, har sauri take ta buɗe tana tunanin kona Kabeer ne, amma bashi bane, text ɗin Hanan ne,
    "ki fito ina harabar gidanku wurin Ajje motoci, kiga wani abin mamaki" tsoki taja, ita Hanan abun mamakinta duk ban haushi ne dasu, tanata tunaninta dai ta fito harabar gidan da sauri ta k'agara taga yau kuma me tazo mata dashi,
     Tsaye ta ganta jikin mota, tun kafin su gaisa tace,
    "Menene zan fito in gani da bazaki iya shiga ki nunamunba"
   "daɗina dake zumuɗi Aleesa, shiga ki gani mana" tana nuna mata cikin motar, ta buɗe kawai ta shiga, da sauri da fito ko zama batayi ba,
   Hanan ta kwashe da dariya "lafiyanki kamar wacce taga abun tsoro?"
    "Hanan dagaske Hadid ne cikin motarnan ko kuma Gezau yakemun?"
   "shine dai Aleesa, ki tabbatar da kanki mana"
   Da sauri ta koma cikin motar, farin cikinta ya kasa ɓoyuwa, sai murnar ganinshi take, shi kuma duk yaa haɗe rai ya kauda fuskarshi gefe ɗaya,
  
   "Hadid daman kananan? Nasha wahala wurin nemanka Hadid, anma yanzu ma wuri bai k'ure mana ba, don Allah taimakonka nake nema"
   "kinga malama, ni wallahi banmasan gidanku zamuzo ba da babu abinda zai kawoni, tuni na fiddaki cikin rayuwatah"
   "Haba Hadid nasan kana sona, don Allah koda wasa ne ka taimakeni in gabatar dakai a wurin Daddyna, wallahi auren dole za'amun, kaaga dai gidanmu cike da mutane duk bikina ne sukazo, don Allah ka taimakeni, ka manta da duk wani abu daya faru tsakaninmu" shiru kawai yayi yana saurarenta yanda taketa rok'onshi, wani irin haushinta yakeji, sai kuma ya tuna da abunda ta mishi, bai manta da marinshi da tayi ba, ga kuma wulak'ancin data mishi a ranar birthday ɗinta, yanzu yaa samu damar dazai rama duk abunda ta mishi,
    "Ya isa haka Aleesa, wannan rok'on da kikaimun ya goge duk wani laifi da kikamin a baya, saboda har yanzu akwai sauran soyayyarki a zuciyatah"
   "da gaske kaa amince Hadid?" ta faɗa cikin farin ciki, ya ɗaga mata kai yana murmushin mugunta,
   "na gode sosae da wannan farin cikin daka bani, insha Allah yau ɗinnan zan kaima Daddy maganarka"
   Ya ɗaga kai cikin gamsuwa, bai wani daɗe ba sukai sallama zai tafi, tana fitowa daga motan ta hango Daddy naa tsaye yana hangenta duk ya gama haɗe rai,

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • HAFSATUL KIRAM 23-25[2:03PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 28-30[11:20AM, 4/20/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &n… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 23-25[2:03PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 31-32[6:39PM, 4/21/2016] Rerbee'art: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &nbs… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 26-27[12:44PM, 4/19/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &n… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts