New Post

Wednesday, 15 February 2017

SANADIN K'IYAYYA 5-6

♠SANADIN K'IYAYYA♠
            (︶︿︶)
                   5-6

©Rabiatu sk msh
            NWA

Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan

   Tana shiga falon ta hango Daddy na saukowa daga upstairs, da sauri jikinta yana kyarma ta wuce ɗakin Momie, ta lafe bayan labule tana lek'enshi,
   Waje ya fita, gabanta yaci gaba da faɗuwa, Momie na tsaye tana kallonta a haka batace mata komi ba, ya daɗe a wajen kafin ya shigo, ɗakin Momien ya nufa, ta wani irin wuntsilawa ta shige bayanta,
   "Miye haka Aleesa, so kike ki nakasa ni?"
   "Momie don Allah ki bama Dad hak'uri ba laifina bane"
   "Ai daman tunda naga yanayinki nasan da abunda kikayi, kwata kwata baki da gaskiya"
   "ina fa take da gaskiya? Sakarar yarinya kawai" Daddy dake shigowa ya faɗa cikin ɓacin rai,
   "Ashe yarinyar nan bata da wayau? Yanzu a gidana zaki wulak'anta ɗan Adam Aleesa? Babban Mutum ba sa'anki ba, wannan inda a k'auyene ya isa haifarki, y'ar k'arama dake cikin ka**nki kin iya rashin Kunya"
    "wai me tayi ne Alhaji?"
  "ta faɗa miki da bakinta mana" tana can duk taa haɗa zufa can murya a mak'ale tace "Yi hak'uri Daddy"
   "ni kikama laifi da zaki bama hak'uri? Idan da gaske kike ki tashi kije ki bashi hak'uri idan da gaske kike" wani ɓacin ran ne ya k'ara baibaye zuciyarta, k'iyayyar Kabeer na k'ara ninkuwa cikin zuciyarta, bazata iya ja da maganar daddy ba, don tsoranshi take sosae ko kaɗan bai musu wasa, haka ya sakata gaba har inda kabeer yake,
   Da yake Daddy bai ganinta, wani irin harara take aikama kabeer kamar idonta zai faɗo,
   "Yi hak'uri" ta faɗa, ko saurararshi batayi ba ta juya tayi cikin gida, shima shiru yayi duk baiji daɗin yanda aka ɓata mata rai ba, yama Daddy sallama sannan ya tafi,
   Tana jiyo Daddy yana bama Momie labarin yanda akayi, ya k'ara da cewa,
  "Kuma yaron ɗan gidan mutumci ne, tare mukayi makaranta da yayanshi, gidan akwaisu da hak'uri da kawaici, gidan Manyan mutane ne, anma ita zata wulak'antashi"
   "ba komi Alhaji, yaran zamani ne sai ana musu addu'a" shiru ya mata kawai,

   Wani haushin kanta ma ta dingaji da hak'urin data bashi, ta saka hannu ta murɗe bakin don tsananin ɓacin rai, ita kaɗai keta faman murguɗa baki a ɗaki,
   "Hege Uban naci kawai" ta faɗa a bayyane,
   Yinin ranar ko fitowa batayi ba waje, ita kaɗai keta k'uncinta cikin ɗaki,

  Washe gari lecturen safe gareta, tana shiryawa Ummie ta mata waya ta fito su haɗu, cikin lokaci kaɗan ta gama saka kaya, ko break fast bata nema ba, ta lek'a dai ta gaishe da Momie, ta mata Addu'ar dawowa lafiya,
   Tun daga k'ofar gida ta k'arajin wani k'unci ya tunkushe mata zuciyah, fuskarta ko kaɗan babu walwala ta fito daga gidan, suka kaɗu da Ummie, tare suka jera har bakin titi da yake babu nisa da gidansu Aleesa,
   Yananan inda ya tsaya jiya, ba k'aramin ɓacin rai taji da ganinshi ba, ta kauda kai kawai ko kallan inda yake batayi ba, ta matsa can nesa,
   Ya fito da fara'arshi suka gaisa da Ummie, itama sai murmushi take mishi kamar wadda suka saba,
   "ina fata dai yau za'a bani damar kaiku makarantarnan" ta murmusa tana kallon inda Aleesa take,
   "banga alama ba, don yau mutuniyar taka da alama ko maganar batason yi"
  "nima naaga hakan, kinsan saraki, anma ki lallasheta plz"

  Tana jin haka, ko kallansu batayi ta tsaida wani mai napep, da sauri ta tafi ta shige tana shirin tafiya tabar Ummie ta matsa da sauri tana tsaidata, sannan ta shiga tana daria,
   "ke yanzu saiki tafi ki barni?"
  "Randa kika k'ara tsayawa wurinshi zaki tabbatar da amsar tambayarki"
  Dariya kawai Ummie keyi
     "lallai naga alama, nikam bani nakar zomon ba ay"
   "ta kusa shafarki kema kau"
Ganin da gaske Aleesar take ya sanya Ummie bata k'ara cewa komi ba, sai dariya kawai take,

    Lecture 3hours sukai, yau sai addu'ah take cikin sa'a kuwa har suka fita daga ckul ɗin bata ga Hadid ba, ta sauke ajiyar zuciya, sai dai kuma tana ɗaga kai idonta ya sauka kan sarkin nacin nata kabeer,
   Yananan tsaye jikin motarshi da Key a hannu, idanunshi na kan hanyar da suke fitowa sai washe baki yake,
   Ummie saida dariya ta kusan k'wace mata,
    "Anya kuwa Ummie mutuminnan yana da hankali? Hegen naci kamar tsohon kwarto" inji Aleesa da abun nashi ma ya fara bata mamaki
  Ummie tace "Karkiga laifinshi Aleesa, duk so ne, wlhy yana sonki sosai, baki taɓajin wak'ar Nura M Inuwa da yake cewa 'Komai mai yin so yayi karku kirashi zautacce' ba"
    "ke oho, ba So ba koma minene matsalarshi yanzu zan sauke mishi, zan nuna mishi gaskiyar wacece Aleesa,"

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts