♠SANADIN K'IYAYYA♠
(︶︿︶)
3-4
©Rabiatu sk msh
NWA
Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan
Sun gama lecture sun fito, A hanyarsu ta komawa ne, Ummie ta kasa hak'uri saida tayi mata magana,
"Waini Aleesa wace kalan K'iyayyace wannan kike nunama maza? Kinsan dai abunda kike baki kyautawa ko?"
"Ni menayi na rashin kyautawa? Bakimun adalci ba idan kikace ina nunama maza k'iyayya Ummie, Soyayyah daice bani da lokacinta, hadid kuma da kikaga inama haka ke kanki kinsan halayenshi basu dace dani ba, ko kaɗan baida tarbiyya, son mata ga shaye-shaye, sai kuma guy ɗinki na ɗazu, wlhy tun kafin in ganshi bazan ɓoye miki ba k'iyayyarshi ta shiga zuciyatah, kawai na tsaneshi"
"tofah! Wannan wacce irin tsanace?"
"kawai dai, kinga mu daina maganarshi ma plz,"
“Ya Allah kasa ko a hanyama kar in k'ara ganinshi”
Ummie tace "Ameen" duk jikinta yayi sanyi,
Firan exam ɗin da zasu fara ta shiga 200lv suka ci gaba dayi, har sukazo k'ofar gidansu Aleesa, aka fara ajjeta sannan ya wuce da Ummie da yake gidansu na gaba,
Earpiece ta saka a kunnenta, tana saurarar wak'ar Rihanna (Complicated), tana son wak'ar sosae sai rausayar dakai take cikin nishaɗi, zata shiga fallo suka haɗu da Momie ta tsaya ta cire earpiece ɗinnan sannan ta mata sannu da gida,
"ina kika tsaya tun ɗazu kin bar mutum yana jiranki?" ta tattaro duk mamakinta tana kallon momie,
"ni kuma?"
"Akwai wata ne bayan ni dake? Baki ganshi ba da kika shigo?"
"ni banga kowa ba momie"
"tohh kije yana can waje yana jiranki"
"tohh" kawai tace tana niyyar shigewa ɗakinta, hakanan taji batason fitar, duk da daman ba fira take ba,
"ina kuma zaki?"
"zan ajje jakarne"
"ajiye tanan, banson jira, bawan Allahnnan ya daɗe yana jiranki", duk taa ɓata rai, ta jefar da jikkar da fito,
Yana hango fitowarta ya fara washe baki, tuni wani k'unci ya ziyarci zuciyarta, guy ɗinnan ne na ɗazu, wannan wane irin rashin zuciyah ne? Wani abu ya tokare mata zuciyah, babu abunda bata ayyanah ba a ranta kafinta isa inda yake,
"Barka da fitowah gimbiyar Matah, ay kin wuce inata magana bakiji ba, da alama kina cikin nishaɗi shiyasa ma ban takuraki ba" tayi matuk'ar daurewa kafin ta buɗe baki ta mishi magana,
"Don Allah nikam wanne rashin zuciyar ne ya kawoka gidanmu?" murmushi mai kyau yake, duk ba bakyaun ne dashi ba,
"Har kin lura da rashin zuciyar tawa kenan? Ay tuni na mallaka miki ita shiyasa ma nake bibiyarki, don kin sacemun abunda yafi komai muhimmanci a sassan jikina"
"Tohh sannu bunsuru" Aleesa, ta faɗa da alama ko maganar batason yi,
K'ok'arin shanye rashin jin daɗin maganarta yayi, "Kabeer ne sunan"
"ban tambayeka ba, kuma ban buk'atar sani, na tsaneka dakai da sunan naka harda shegiyar zuciyar, ka fita hanyata, idan baso kake na maka rashin mutuncin da baka taɓa tunani ba"
"Haba Hajia Aleesa! Ay halinki ma sam bai kama dana masu wulak'anci ba"
"zan ko ara in yafa! Ka fice mana daga gida, don k'aramin ganin (dodon jatau) da kallon fuskarka, don Allah kalleka, ko kyaun gani babu anma a haka kakeso na, mtsww"
'tsayawa wurinnan ma tare dashine babban horon da za'amun a rayuwa, nima na tsaya da har nake maida mishi magana', ta juya kawai zata bar wurin da sauri ya tsaida ta, "Zan tafi, anma don Allah ki tsaya ki amsa" batace mishi komi ba taci gaba da tafiya, ba shiri yasha gabanta,
"haushi ya kawota iyakar wuya" ta kalli hannunshi, bandir ne guda biyu na dubu-dubu,
"Don Allah ki amsa, nasan kinfi k'arfinsu, anma don Allah ki amsa"
Bata ce mishi komi ba ta raɓashi zata wuce, ya k'ara shan gabanta, ga wani irin haushinshi da takeji idan tana ganinshi a gabanta, haka ya dinga nace mata saita amsa, mik'a hannu tayi kawai kamar abin k'yama ta amsa, ta kalleshi sai daɗi yakeji, sannan ta saita goshinshi a dun'kulen ta jefa mishi, har saida yayi baya ya kusan faɗuwa, ba k'aramin buguwa yayi ba dafe da goshinshi yake kallonta idanunshi sunyi jajir,
Ta nunashi da yatsa,
"karka taɓa tunanin abun hannunka zai burgeni, baka ganni da yunwa ba, ni kaina sai inyi kyautar fiye da wannan, yanda na tsaneka, haka na tsani duk wani abun daya shafeka, kuskurenka na k'arshe shine sake, sako k'afafunka cikin gidannan," ta juya taci gaba da tafiya,
Ya fara magana, abun mamaki fuskarshi sam babu damuwa, murmushi ma yakeyi,
"Alhamdulillah, bazan iya fasalta farin cikin da nake ciki ba, addu'ar dana daɗe inayi ne Allah ya amsa Aleesa, Mata da yawa sun nunamun soyyaya, ban taɓa cin karo da wacce takemun k'iyayya ba, Mata da yawa dukiyatah sukeso Aleesa, sai yaune naci karo da wacce kuɗina ma basu burgeta, banso ki soni don wani abu dake tare dani Aleesa, ki soni don Allah kawai, naji daɗi da dukiyatah bata burgeki,"
Tsabar takaici ma kasa ce mishi komi tayi, kallon wanda ciwon hauka ya kama kawai take mishi, ɗaga kanta tayi can saman bene, daddy ne tsaye yana hangen duk abun dake faruwa, tuni hanjin cikinta suka kaɗa, ba shiri ta shige gidan da gudunta,
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment