New Post

Wednesday, 15 February 2017

SANADIN K'IYAYYA 7-8

♠SANADIN K'IYAYYA♠
            (︶︿︶)
                   7-8

©Rabiatu sk msh
            NWA

Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan
  
   Aleesa na niyyar tafiya wurinshi, Ummie ta jawo hannunta ta rik'e,
   "Haba Abokiyah, don Allah karki mishi wulak'anci, mutuminnan iyakar hak'uri da kawaici ya nuna miki, na tabbatar miki da wani mugu ne, Asiri kawai zai miki ya rama abunda kika mishi"
   "Asirinshi na banza, wlhy ko ban cikin hayyacina na aura wannan kasheshi zanyi sai dai nima a kasheni" cewar Aleesa, Ummie ta rik'e baki,
   "A'uzubillahi, meya kawo maganar nan? Duk bai kai nanba" Aleesa ta harareta,
   "Ayna ɗauka zaki tare mishi ne," ita dai Ummie lallaɓata take har suka samu abun hawa, suka shige kawai babu wanda ya kulashi cikinsu,

Bayan Shekara Uku
Da haɗuwar Aleesa da kabeer, shekara ukunnan kullum yana hanyar gidansu, bai taɓa tsallake rana ɗaya baije makarantarsu ba indai yasan tana da lecture da niyyar ɗaukota, kuma so ɗaya ko kallonshi bata taɓayi ba, kullum K'iyayyarshi ce ke k'aruwa a cikin zuciyarta,
   Ɓangarensu Daddy kuma sun ansheshi hannu bibbiyu, kowa a family ɗinsu da k'annanta suna yabawa da Kabeer, harta da kuɗin neman aurensa an amsa shekara biyu da suka wuce,

*****
Aleesa ce zaune k'asa, ta ɗaura kanta saman cinyar momie kuka kawai take rusawa, tun bayan da taji ana niyyar saka ranar aurenta da Kabeer,
   "Ki taimakeni Momie, wlhy k'iyayyarshi ce zatayi ajalinah idan aka auramunshi, banison shi Momie, na kasa lallashin zuciyatah ta rage koda kaɗanne daga cikin k'iyayyar da take mishi,
    Momie ta shafa kanta cikin lallashi "Hak'uri dai zaki Aleesa, kinsan halin mahaifinku baya canja magana, kuma ni banga abun k'i ba a wurin Kabeer"
   "Nidai Momie bazan iya aurenshi ba wallahi...."
   "Idan baki aureshi ba wa zaki aura?" inji Daddy da yake laɓe yana sauraransu, ta k'ara fashewa da kuka,
   "Bawai na gaji da zamanki a gidannan bane Aleesa, anma duk mutuncin ɗiya mace yana ɗakin mijinta, kullum fa kwanaki shuɗewa suke, Shin idan bashi ba wa zaki aura?"
    Tana shesshek'ar kuka tace "ni kowama ka auramun Daddy, Anma wlhy nidai banison kabeer", ya nisa kaɗan, sosae kukan da takeyi yake bashi sosae, kuma k'iyayyar da Aleesa take ma Kabeer a bayyane take da bazai iya cewa bai ganinta ba,
   "Bazan aura miki kowa ba, anma zan iya baki dama ki kawo wanda kike so, duk da ba wannan ne karo na farkoba, anma ki sani wannan ce dama ta k'arshe dazan baki, idan har kika kasa kawo mini wanda kikeso, nan da sati Uku ki fara kallon kanki a matsayin matar kabeer"
   Tana share hawaye cikin farin ciki tace "Na gode Daddy" ta mik'e da gudu ta nufi ɗakinta tana murna,

  Anma sai dai Murnar tata ta koma ciki data fara tunanin to wa zata kawo a matsayin mijin da zata aura? Babu saurayin data taɓa kulawa da matsayin soyayya, Hadid ne ya faɗo mata a rai, tun wani wulak'anci data mishi ko a hanya bata k'ara ganinshi ba, cikin damuwa ta fara tunano abun daya faru ranar,
    Birthday ɗinta ne, tunda safe take samun sak'onni daga en uwanta da Abokan Arzuk'a, wani irin farin cikine take ciki a ranar, da misalin K'arfe 9pm, wata k'awarta Hanan ta mata waya,
    "Birthday girl ya kike?"
   "lafiya lau hanan, ya mama"
   "Qalau take, wai me aka shirya mana ne?"
    "kedai ba komi wallahi, kinsan ban shirya ma abun bane"
   "Tohh Albishirinki" cikin zumuɗi tace "Goro fari k'ar hanan faɗamun mana"
    "bazan faɗa miki ba, kedai kizo address ɗinnan dazan turo miki ki gani"
   "Haba tawan kiɗan gutsuramun ko kaɗan" tana dariya tace "Naak'iya, kedai sai kinzo"
     "Tohm bara in tashi in shirya" sannan ta yima Ummie waya, dak'yar ta lallaɓata akan zata rakata, sannan ta fara shirin tafiya tana tunanin wanne irin Albishir ne hanan zata mata?

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts