New Post

Wednesday, 15 February 2017

SANADIN K'IYAYYA 15-16

♠SANADIN K'IYAYYA♠
            (︶︿︶)
                   15-16

©Rabiatu sk msh
            NWA

Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan

www.babymsh.blogspot.com

    Da sauri ta raɓa ta gefenshi zata wuce, ya daka mata uwar tsawa ba shiri taja burki, yaja hannunta k'iii har ɗakinshi don kar yayi magana mutane suji,
    "Wane ɗan iska ne kikazomun dashi cikin gidannan?"
    "Hadid ne Abba, shine wanda zan aura ɗin" ta faɗa bakinta na kyarma,
   "wannan tantirin ɗan iskan Aleesa?" ya faɗa cikin mamaki, don har ganin Hadid ya taɓayi da wata a mota suna shafe-shafe, harya gwada yi mishi nasiha, bai saurareshi ba duk da ganinshi babban mutum anma saida Hadid ya karta mishi rashin mutunci,

    "ba'a gidana ba Aleesa, daman shi yake zugaki kina mana yanda kikaga dama ko? Ke yanzu har kinyi tsaurin idon da zaki tura ma Kabeer sak'on barazana ko?" dagajin yanda yake maganar abun na matuk'ar mishi ciwo a zuciyah,
    "Suɓutar bakine Daddy, anma wlhy nidai bazan iya aurenshi ba....."
   "ke kika sani, nidai bazaki taɓa sakani inyi k'aramar magana ba, sannan kuma sak'on da kika tura mishi bazai taɓa sakawa a fasa aurennan ba, nida kaina na kai maganar nan police station, don abun naki ya fara fin k'arfina" kukanta ne ya k'ara tsawaita, ya k'ara daka mata tsawa,
    "ficemun a ɗaki" da gudu ta ɗita ɗakinta tana kuka ta faɗa saman gado, ta iske Ummie tazo, ita taɗan kwantar mata da hankali sai dare ta tafi,
  
    Daman abunda take jira kenan, zuciyarta a k'ek'ashe ta nemo number Hadid ta fara kiranshi, bata daɗe tana ringing ba ya ɗaga, kuka kawai ta fashe mishi dashi, duk ya rikice,
   "lafiyanki kuwa Aleesa? Meke faruwa dake?"
  Cikin muryar kuka tace "ka taimakeni Hadid kazo mu gudu, Daddy bazai taɓa yarda da aurenmu ba, don Allah ka gudu dani ko bazaka aureni ba ka kaini can wani wurin"
   "Haba Aleesa ki kwantar da hankalinki mana,....."
   "taya hankalina zai kwanta? Gobene fa ɗaurin Aurennan, wallahi k'iyayyarshi zata iya jamun in aikata komai, don Allah ka ceci rayuwatah" jin rok'on da take ta mishi, gashi a hakanma zaifi samun damar dazai rama abun data mishi, harya gama tunani a ranshi fyaɗe kawai zai mata ya yasar da ita tsakar gari,
   "shikenan ganinan tafe"
  Cikin farin ciki ta kashe wayar, daman ta riga da taa gama haɗa kayanta, tun kafin yazo ta ɗauka jikkar ta fito a sulale, cikin sa'a mai gadi bainan harta fita babu wanda ya ganta

   Kusan Awa ɗaya tana jiranshi a bayan gidansu, harta fara k'osawa saiga motarshi ta taho, da sauri ta tafi zata shiga tun kafin ya gama parking duk a tsorace take,
   Fitowa yayi ya zagayo inda take zai buɗe mata, sai kawai ji yayi abu yaa bugi kanshi, wasu manyan k'arti guda huɗu kowanne da mugun makami, tuni Aleesa ta fara matse fitsarin dake k'ok'arin zubo mata, akan idonta k'artinnan suka dinga jibgarshi,
   Ba k'aramun buguwa yayi ba, akan idonshi Daddyn Aleesa yazo yaja hannunta, ashe daman ya lura da fitarta, shiyasa ma ya saka ayi gadin wanda zaizo ya tafi da ita bayan ya bada umarnin duk wanda aka gansu a tare a mishi mugun bugu,
   Hadid kallon Daddyn Aleesa ya shigayi duk da azabar da yakesha, bai manta da fuskarshi ba, wata wutar ɗaukar fansarce ta k'ara ruruwa a cikin zuciyarshi, daman cike yake da haushin Daddynta,
   Laifukan da Aleesa da mahaifinta suka mishi ba masu yafuwa bane, Bayan marin data mishi a cikin jama'a, da kuma wulak'ancin data mishi, ga tozarcin da mahaifinta ya mashi, da kuma wannan dukan daya saka aka mishi sanadin Aleesa, dolene ma ya ɗauka fansa,
   Wani irin kallo ya bisu dashi har suka shige gidan yana jan Aleesa tana faɗuwa, shi kuma ya faɗi sumamme,

   Suna shiga gidan ba tare da kowa ya sani ba, Daddy ya jefata ɗakinta ya rufe, har saidata bugu a k'asa, ta zube nan tana rusar kuka har barci ya kwasheta,
   Washe gari ɗaurin aure, anata neman amarya babu ita, ga ɗakinta a rufe, don tsananin ɓacin rai Daddy da safe ya mayar da ɗaurin auren, babu ma wasu mutane masu yawa aka ɗaura, kuma ba'ayi wani shagalin biki ba, ita dai daman ko k'awayenta babu wacce ta sani sai ummie,
  Ba'a fiddo Amarya ba sai da dare ana shirin kaita....

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • ABDUL WAHAB 36ABDUL WAHAB 36 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Kwana biyu tayi suna jinya ita da Abdul, ko motsi zatayi ji yake kamar yayi mata, kulawa sosae yake bata, yaa tattara ya daw… Read More
  • ABDUL WAHAB 35ABDUL WAHAB 35 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Mi'kewa tayi zumbur kamar antsikareta, idonta harya fara canja kala, dai-dai sanda Abdul yaturo 'kofar d'akin ahankali yashi… Read More
  • ABDUL WAHAB 37ABDUL WAHAB 37 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Tsayawa yayi daga baya yana sosa 'keya yace "sannu da zuwa hajia," ta amsa mishi tana mishi kallon marar gaskia. Sai data za… Read More
  • ABDUL WAHAB 34ABDUL WAHAB 34 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Fatyma ta dafa kafad'arta cikin tausayawa tace "shi yayanmu ne yake miki hakan? Cikin jin haushi tace "A'ah ni nakeyi mishi,… Read More
  • ABDUL WAHAB 38ABDUL WAHAB 38 ©Rabiatu sk msh            ®NWA Tun daga ranar ta koma rufe 'kofarta da makulli ta barshi a jiki, bata fitowa ko falon d'akinta sai Abdul bainan, ta k… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts