♠SANADIN K'IYAYYA♠
(︶︿︶)
17-18
©Rabiatu sk msh
NWA
Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan
Abba da kanshi ya saka Aleesa a motah ba tare da neman Rakiyar kowah ba, tana kuka tana komai, har cikin ɗakinta ya kaita, don tsananin jin haushinta ko nasiha bai tsaya mata ba,
Anan ta duk'e tana kuka, donma karta taka ginin gidan kabeer, saita haye can saman hadaɗɗen gadon da aka kai mata, tana ci gaba da kukanta don tsananin k'iyayyar da take mishi, ta manta ma acikin gidan take,
Wani abu ta tuna, da sauri ta mik'e ta nufi kitchen, tana dudduba kayanda aka kawo mata, saida tasha wahala duk taa birkita kayan, sannan ta samo wata er k'aramar wuk'a mai kaifi sosae, ta dawo ɗakin zuciyah nata mata huɗuba kala-kala, wani iri takeji a zuciyarta komai ma haushi yake bata, ta rink'a dukan kanta da hannunta tana kuka, ji take daman ta mutu kawai ta huta da tsanar data mishi,
Ta mik'e ta fara jifa da kwalaban humra da aka jera mata dana turaren wuta, suka dinga fashewa suna zubewa, ta jefa wani tsakiyar madubi shima duk ya tarwatse, har ya dawo mata kusa da ido wurin ya fashe, jini ya fara zuba, duk da haka bata saurara ba ta fara waigen ɗakin tana neman abunda zata fasa,
Tunda ya shigo gidan ya fara jiyo k'arar fashe-fashen da takeyi, daman shi kaɗai yazo don duk Abokanshi haushinta sukeji saboda k'iyayyar da take nuna mishi shi kuma yana nace mata, en uwanshi ma babu mai sonta, saboda ik'irarin da tayi na kasheshi, duk basu so auren ba,
Cikin tashin hankali ya k'arasa cikin falon duk ta mishi kaca-kaca, ga jinin dake zuba a goshinta, a rikice ya fara ɗosana k'afarshi don karya taka kwalaban da suka fashe, ya nufi inda take,
"karka kuskura kazomun inda nake,"
"Haba Aleesa ya zakice kar nazo inda kike? Don Allah karki illata kanki"
"Don Allah Aleesa kiyi hak'uri kinji, nasan na aikata miki laifi, anma kiyi hak'uri karki jima kanki ciwuka koma me kikeso zanyi" wani murmushin takaici take mishi,
"Ai kaa riga da kaa makaro Kabeer, tunda ka aureni kaa gama illatamun rayuwah, idanda abun daya rage kamun kawai karka k'ara nuna mummunar fuskarka a gareni, na tsaneka! na tsaneka!!, na tsaneka kabeer, idan har kanasona meyasa ka k'wacemun farin cikina? Don Allah ka rabu dani?"
"Haba Aleesa, taya zan iya rayuwa ba tare da ganin fuskarki ba? Wallahi ina sonki Aleesa, ki bani dama koda sau ɗayane in gwada miki irin sonda nake miki"
"Wai wannan wanne irin naci ne? Anya babu taɓin hankali a tare dakai? Mutum sai shegiyar k'wak'wa"
"kiyi hak'uri...."
"Ka wuce ka fita nace!!" ta faɗa da wata irin tsawa muryarta na rawa,
"Ka tashi ka fita tun kafin ɓacin rai ya sakani yin abunda mu duka zamuyi nadama daga baya, ka tashi ka fita kawai"
"Ya za'ai in fita in barki cikin wannan halin? Kimin Alk'awarin bazaki aikata ma kanki komai ba"
"Bazaka fita ɗin ba kenan? Ina zuwa" ta ɗaga filo ta ɗauko wuk'ar data samo kitchen ta nunashi da ita,
"hak'urina ya fara k'arewa, ka fita kawai nace,"
Ya zaro ido yana kallonta, "me zakiyi Aleesa?
"SANADIN K'IYAYYAR da nake maka babu abunda bazan iya aikatawa ba!"
Ya fara ja baya yana kallonta,
"Don Allah kiyi hak'uri, ki fahimceni Aleesa, nasan bazaki iya kasheni ba,....."
"k'warai ma kuwa, anma zan iya kashe kaina"
Ya k'walalo idonshi yana kallonta ta harareshi,
"komai zan iyayi don in bak'anta maka, idanna kashe kaina wa za'a tuhuma? Idan duk duniya zata taru babu wanda zai yarda akan bakai ka kasheni ba, tunda kowa yasan abunda ke tsakaninmu, harma a rink'a cewa donka huce haushin abinda nake maka ne, kai maganganu dai gasunan"
Tunda ta fara magana kallonta kawai yake ya kasa ko motsi,
"Ya zakaji idan na mutu gaba ɗaya? Kuma ace kaine ake tuhuma da laifin kasheni? Kodan in dasa maka wannan bak'in cikin zan iya kashe kaina, don haka kai nake jira, ka tashi ka fitarmin a ɗaki, kuma duk ranar dana k'ara sakaka idona saina aikata abunda na faɗa,"
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment