New Post

Wednesday, 15 February 2017

SANADIN K'IYAYYA 11-12

♠SANADIN K'IYAYYA♠
            (︶︿︶)
                 11-12

©Rabiatu sk msh
            NWA

Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan

www.babymsh.blogspot.com

   Tana shiga falon bak'in, daga ganin yanayinta Kabeer yasha jinin jikinshi, yasan yauma cikin ɓacin rai take, ta nema wuri ta zauna ba tare da tace mishi komi ba, kamar ma batasan akwai wata halitta a wurin ba,
   "Ranki shi daɗe an dawo lafiya? Ya gajiar makarantar? ya hanya?"
   Wata banzar kallo ta watsa mishi "nayi maka kama da wacce zata amsa maka duk wannan tambayoyinne? Kokai makaho ne da bazaka iya gani ba?"
   "Allah ya huci Zuciyarki, ai tun ɗazu daga makarantarku nan na taho, baki kula ba har wayarki na kira ban samu ba"
   Taja tsoki tana k'ara mishi wani kallon sama da k'asa "Ai indai aikinka ne naci da duk number da nayi saika nema, ni kuma bazan gaji da canja layi ba,"
   "wai menene ma ya kawoka gidanmu?"
   "Haba Aleesa yanzu bazanzo ganinki ba sai wani abu ya faru? Ga biki nata matsowa ya kamata mu shirya yanda kikeso ya kasance ko"
   "kai wannan ya dama"
  Sai kuma ta canja yanayinta ta ɗan rage zafin da tazo dashi kamar wacce ta tuno wani abu,
   
    "Yauwah daman inason muyi magana" duk ya tattara hankalinshi da nutsuwarshi gareta, farin ciki ya kasa ɓoyuwa a fuskarshi ganin yau Aleesa ce keson magana dashi kuma ba tare da tana masifa ba,
   "ki faɗa kawai Aleesa duk wani lokacina naki ne"
   "Naji anma bazaka faɗama kowa ba?"
   "Haba Aleesa nida na daɗe inason ki faɗi wani abunda kikeso in miki, sai wannan er k'aramar Alfarmarce zata gagareni in miki? Ki faɗa koma minene na miki alk'awarin zan miki"
   "ba wani babban Abu bane, so nake ka janye maganar aurennan, kaasan dai ba sonka nake ba"
   "na daɗe da sanin hakan, anma bayan wannan babu wani dalilin? Don k'ara kicemun in baki rayuwatah zan iya mallaka miki, anma bazan iya hak'ura da aurenki ba"
   "koda na faɗa maka cikine dani?" ta faɗa tana kallon yanayinshi, aykam gaba ɗaya hankalinshi ya tashi,
   "Ciki kuma Aleesa?"
  "sai kaa buɗe murya kaa gama faɗa kowa yaji sannan zangane kasan me nace," ta faɗa tana harararshi,
   "kaa san dai babu kyau aure da ciki, kuma kisan kai ma babu kyau, don haka tunma kafin kowa yaji k'ara ka janye maganar aurennan"
  
  Ya daɗe yana tunani, duk rikice yake kamar wanda yaji sak'on mutuwa, dak'yar ya iya buɗe baki ya fara magana,
   "Tohh anma Aleesa kinsan inajin Kunyar Daddynku, kidai nema wata buk'atar banda wannan, anma zuciyatah bazata iya jure tayi nesa dake ba"

  Tuni ya gama bata haushi, harta fara murnar samun nasara sai kuma gashi zai k'ara ɓata mata rai,
    "Shikenan tunda bazaka janye ba, zan samu su Daddyn  in faɗa musu da bakina cikinne dani, sannan kuma ince kaine kamun"
   Duk ya fiddo idanunshi a waje yana mamakinta,
   "Ni kuma Aleesa?"
  Ta ɗaga mishi kai cikin jin daɗin samun nasara 'k'warai ma kuwa"
   "son gaskiya nake miki Aleesa, kuma a dai dai wannan lokacinne ya kamata in tabbatar miki da son da nake miki, duk wani abunda ya shafeki kamar nine ya shafa, wlhy har a zuciyatah nake faɗa miki, zan karɓi abunda yake cikinki, zan zame mishi gata, ban damu da sanin koma wanene ubanshi ba, nine zan zama mahaifinshi tunda inason mahaifiyarshi,"
   "wai kai wane irin dak'ik'ine da bakasan me yake maka ciwo ba?"
  Yayi murmushi "indai akan sonkine ki kirani da koma menene"
   "koba taurin kai da naci ba? Wlhy Ajaline yake kiranka don zan iyayin komai Sanadin Kiyayyar da nake maka" cikin ɓacin rai tayi maganar anma saida ya tsorata, don yasan komai zata iyayi akan k'iyayyar da take mishi,
   Har takai k'ofa ta kusa fita, ya ɗaga muryarshi,
   "Na yarda da tarbiyarki, nasan bazaki taɓa kusantar zina ba,"
  Kamar yanda ya zata ko saima k'ara saurin da tayi tabar ɗakin, tana k'arajin wani haushin,

  ©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts