New Post

Wednesday, 15 February 2017

SANADIN K'IYAYYA 9-10

♠SANADIN K'IYAYYA♠
            (︶︿︶)
                  9-10

©Rabiatu sk msh
            NWA

Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan

Www.babymsh.blogspot.com

   K'arfe 10 dai dai suka isa wurin partyn, sunci kwalliya sosai kamar masu zuwa gasar sarauniyar kyau, suna takunsu ɗai-ɗai har suka shiga daga ciki, wurin cike yake da course mate ɗinsu, da sauran en makarantarsu dai, kowa ya gama k'ure adakarshi,
   Aleesa ta fara k'are musu kallo tana hangen inda zata gano Hanan, saiga Hadid ya fito yana murmushi, ya fara rairo mata "Happy Birthday to you" gaba ɗaya wurin suka amsa, suna tayata murnar zagayowar haihuwarta,
   Tun ganinshi yanayinta ya canja, Hadid ya mik'a hannu ya amsa loud speaker zai fara magana,
    "Ina farin cikin gabatar muku da tauraruwar mata, kuma tauraruwa a cikin zuciyar Hadid watau Aleesa, ina miki barka da zuwa wannan wuri, tare da tayaki murnar zagayowar ranar haihuwarki," duk wurin ya kaure ta tafi,

   Cikin ɗaga Murya Aleesa tace "waye ya haɗamun birthday partynnan?"
   Hanan dake can gefe tace "Hadid mana, kina da masoyin daya fishi?"
   Murmushin mugunta kawai tayi bayanta girgiza kai, ta fara taku zuwa inda yake, Ummie ta rik'o hannunta, kallonta kawai tayi ta saketa, shikam sai murmushi yake ganin tana k'arasowa gareshi,
    Hannu kawai ta saka ta ture birthday cake ɗin da ba k'ananun kuɗi aka kashe wurin tsara su ba, da sauran drinks ɗin komai ya zube k'asa, sannan ta nunashi da ɗan tsaya,
   "A rasa wanda zai haɗamun birthday party sai kai? Mayaudari, mai bin en mata, mara aji ma da kowacce bi kake," sannan tayi shiru don tsabar k'uluwa ma taa rasa me zatace,
   "Duk yanda zaka gwada bazan taɓa sonka ba Hadid, baka cikin jerin mazan da zanso, nacin yaa isa haka, ka gwada sa'arka wani wurin" tunda ta fara magana ya fara huci, ɓacin rai kamar zuciyarshi ta fasa k'irji ta fito, cikin hargagi ya fara magana,
    "Da wuri haka Aleesa? Ki rubuta ki ajje ni Hadid saina rama duk wulak'ancin da kikamun, bazan taɓa k'yaleki ki shani a banza ba, sai kinga SANADIN KIYAYYAR, da kika nuna mun"
   "kanka dai akeji, namamajo kawai" wata irin tsawar ya k'ara daka mata cikin ɓacin rai, ta k'ara harararshi son ranta sannan taja hannun Ummiee suka bar wurin,

***
Sauke ajiyar zuciyah tayi bayan ta gama tunano rabuwarsu da Hadid, gashi yanzu ya gama makaranta batasan inda zata k'ara ganinshi ba,
   Dubara ce tazo mata, numbers ɗin Abokanta ta ringa kira tana tambayar ko akwai mai numbershi, anma cikin rashin sa'a babu wanda yake da, wannan fa shine ga k'oshi ga kwanan yunwa,

Kullum cikin neman Hadid take harya rage sauran sati ɗaya bikinta da Kabeer kamar yanda Daddy ya saka ranar, kullum damuwarta k'aruwa take, gaba ɗaya taa rame sosae kowa ya ganta zai san tana cikin tashin hankali,
   Yau a gajiye ta dawo daga makaranta, tun daga can Kabeer ke biye da ita, ko kallanshi batayi ba har ya gama parking motarshi, ta shige cikin gidan kawai,
  Cikin jan jiki ta gama duk abinda take, tana sane da yana waje yana jiranta, ko falo ma tak'i fita don kar Momie ta tilastata fita wurinshi, saima ta nema wuri ta kwanta ta fara sharar barci hankalinta kwance,

   Can cikin barci take jiyo muryar Haisam Autah yana mata magana kamar mai shirin fasa mata kunne "Aunty Momie na kira, Aunty, Aunty kije inji Momie" ta mirgina cikin barcin muryarta cike da gajia yace "Mezan ma Momien?"
   "wai uncle Kabeer ne yake jiranki, tun ɗazu" cikin masifa ta tashi Zaune
   "kuma shine zakazo ka tadani a barci na? Ficemin daga ɗaki, kuma ka faɗa mishi yabar gidannan, inba haka ba saina ɓallamaka kunnuwan nan"  da sauri ya juya ya nufi ɗakin momie, yana rik'e da kunnuwanshi,  sai gashi sun dawo tare da momien,
   "Kikace a gayamun bazaki zo ba?"
   "nifa A'ah momie, cewa nayi yanzu na dawo daga makaranta duk na gaji ya tafi sai anjima"
   "tunda kin maidashi yaronki ba? Ki tashi ki fita tun kafin Daddynku ya dawo ya haɗamu harni harke, tun yaushe kika dawo daga makarantar, kinsan kuwa ko awanshi nawa yana jiranki? Ki tashi ki fita nace" tayi k'asa da kanta,
   "zan tashi momie"
  "ki tashi nace inanan ina jiranki" ba don taso ba, ta tashi ta zari mayafi tayi gaba tana tunanin kalar masifar da zata sauke mishi,

  ©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts

 
seo