New Post

ABUBUWA BAKWAI (7) ABIN KULA GA DAN'ADAM

1. Duniyar da za a barta, me ya kawo hadama? 2. Dukiyar da za a lissafa daya bayan daya, me ya kawo tarata? 3. Rayuwar da zata kare, ina wani farin ciki? 4. Yarintar da tsufa zai zo mzta, me ya kawo takama? 5. Ana sauraren mutuwa, ina wata walwala? 6. Jikin da zai zama gawa, me ya jawo dagawa? 7. Karshe dai makomarsa kabari, me zai sa alfahari? Wanda ya manta da wadannan a ina ya bar hankalinsa? Allah yasa mu dace, yayi mana kyakkaywan karshe. Ameen!

KADA KA RAMA CUTA GA WANDA YA CUCEKA!

Kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka, kai kayi hakuri. Zaka samu abu biyu sakamakon hakan; * Na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. * Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

KADA KA BARI ZUCIYARKA TA ZALUNCEKA!

Kada ka sale zuciyarka ta zalunceka, tabbas zaluncin zuciya ga gangar jiki yake komawa, idan akayi wasa ya zamanto ya shafi rayuwa. Assasa bak'in tunani, yawan zargi da rashin tabbas akan wani aiki, zato, shakku ko kokwanto akan wani al'amari batare da tantance gaskiyarsa ba, shine zaluncinzuciya akan dan Adam. Maza ka hana zuciyarka don akwai hadurra dubu akan hakan.

MAHAKURCI MAWADACI

Tabbas ba kowane dandanon magani ne ke da dadi ba, amma babu shakka shine abu mafi dacewa ga dukkan mara lafiya. A lokuta da dama rayuwa takan dakeka da guduma ta jefaka acikin wani mawuyacin hali, kayi ta fama amma tayi maka tutsu. Amma idan kayi hakuri sannu ahankali zata kwaranye. Hakika ba duk abinda rai yake so yakan samu ba, amma bukata bata taba sauyawa ba kuma bata taba karewa ba. Don haka ka shirya bukatunka da kyau ka bisu daya bayan daya sannu a hankali, kayi gwa- gwarmaya, sannan kayi juriya. Tabbas mafarkinka zai zama gaskiya.

KO KA SAN?

Rayuwa bakin alqalami ce tana bukatar kaifi sannan tana son tsini. Kaifin don ka yanki magauta, tsinin kuwa don ka soki makiya. Haka zalika rayuwa kamar randar ruwan sanyi ce ta kasa tana bukatar tanaji da adani, kodn wata rana ka shayar da masoyanka. Da kyau ka lura da abu biyu a rayuwa; 1. Ka lura da mai zaginka mai aibantaka wata kila wata rana zai iya zama masoyinka mai yabonka 2. Ka lura da masoyinka na kusa mai yawan ambaton alkhairinka, wata kila wata rana zai iya zama makiyinka mai zaginka.

Friday, 12 July 2019

MEYE SANADI? 1

♡ *MEYE SANADI?* ♡
           ♡♡♡♡♡♡
              ♡♡♡♡
                  1
©Rabiatu sk msh
     ®NWA

WATTPAD; Rerbee'art_sk

Wannan littafin nawa, ƙirƙirrare ne, banyi shi don cin zarafin wani ko wata ba, ina maraba da gyara a duk inda yake indai ba na cin fuska bane.

Dole na gaishe da  ƙawayen albarka, RAZ nawa, bazan taɓa gajiyawa da faɗan yanda nakejin ku a zuciyatah ba, ku ne ni, nice ku (Amrah A msh, Zahra BB) Aminan ƙwarai

Bismillahir rahmanir rahim

Wayarta dake hannunta, ta maida gefe bayan ta gama duba abunda takeson gani, sannan ta ɗaga idanunta ta fara ƙarema yalwatacce, kuma ƙayataccen ɗakin da take ciki kallo, anya ta yiwa kanta adalci kuwa idan ta ƙarar da rayuwarta ita kaɗai a cikin makeken gidannan? Tabbas duk warin da zatayi, bata tunanin maƙotanta zasu iya jiyowa ballantana har gawarta ta samu gatan da za'a mata sutura,
      Kasancewar unguwarsu, unguwa ce da babu ruwan wani da wani, bata son ko bayan mutuwarta gawarta taci gaba daa rayuwa a wannan gidan, wannan dalilin ne ya sakata jawo mukullin ɗaya daga cikin motocinta, da wayarta, sannan ta zuba duk wani abunda ta tanada a cikin but ɗin motar, da kanta ta buɗe gate ɗin kasancewar ko mai gadi bata dashi, sannan taja motarta ta doshi hanyar daji bayan ta rufe ko ina.

Tafiyah tayi mai ƴar nisa,  sannan tayi parking dai dai wurin wani icce, sai da ta ƙara jawo wayarta, ta duba hotan sosai sannan ta maida ta aje, ta buɗe but ɗin motar ta fito da wani madaidaicin (Stool) mai kyau, ta ajje, sannan ta ɗauko igiya, ta taka Stool ɗin ta ƙulle igiyar a jikin wani ƙaton reshe, kaman yanda ta gani a jikin hotan, har lokacin babu wani tsoro a ranta ko fargaba, babu kuma tunanin zata fasa abunda tayi niyya

*** ***
Abokinshi yayi ma Rakiya ganin wani fili da yake son mayarwa gidan gona, hakanan yanayin wurin ya burgeshi har yaji yana son zagaya wurin sosai,
    Yana tafiya yanayin wurin na mishi daɗi, har baisan lokacin da yayi nisa sosai da inda yabar Abokin nashi ba, ko wayar da yakeyi ce ta ɗauke mishi hankali? Sai da ya gaji da surutun da take mishi, yana niyyar sauke wayar ya hangota da er tazara tsakaninsu,
    Abun da ya hangone ya tabbatar mishi lallai ƙoƙarin kashe kanta take,  ta taka Stool ga igiya tana ƙoƙarin saƙalawa a wuyanta, da saurinshi ya ƙarasa inda take.
     "Ke! Ke!! Dakata mana, meye haka kike ƙoƙarin yi?",
     Wani irin malalacin kallo ta bishi dashi baki a buɗe ba tare data bashi amsa ba.
      "Awk fahimta, na gane! Ƙoƙarin kashe kanki kike, anma saboda me kina yarinyarki?"
    Wannan karon ma bata bashi amsa ba, duk da shirin da ya ɗanyi ganin da tambaya ya ƙarashe maganar shi.
 
Ganin hakan ma duk baiyi ba, ya ɗan dai daita natsuwarshi,
    "Sauko" yana ƙara mata alama da hannu,
   Ta ƙwalalo idanu tana kallonshi da mamaki,
       "sauko nace"

Sai yanzu tayi magana, karo na farko,
       "Malam wai lafiya, me ruwanka dani?"
     "kashe kanki kikeson yi ko wahala kike son bama kanki? Waya faɗa miki haka ake ma igiyan? Da taji nauyinki zata warware ki faɗo a ƙasa ke kaɗai babu mataimaki,"

     "idan da gaske kashe kanki zaki sauko ki gani in gyara miki"
    Ta wurga idanunta,
"kaga alamun wasa ne a tattare dani?"
   Sannan ta sauko ta koma gefe ta goya hannayenta,
    Tana tsaye ya taka stool ɗin ya gyara ƙullin ta da yima igiyar sosai, sannan ya sauko,
    "Yauwah kinga hakan yayi"
   
Sai da ta dai-dai ta saman kujerar, ta runtse idanunta, sai ga muryarshi ta ƙara dukan kunnuwanta,
      "yanzu duk taimakonki da nayi baza kimin koda godia ba?"
     "koda yake, wake neman godia daga wurin matatta? Ci gaba kawai"
      Ta sake rufe idanuwanta,
     "Yauwah, faɗamun sunanki ma idan na tashi  miki addu'ah"
   Ya ɗan riƙe haɓa (chin) alaman tunani,
      "wacce Addu'ah kuma, bayan tun duniya kin san makomarki? Duk wanda ya kashe kanshi wuta ce zai shiga ko?"
    Ya ɗago yana kallonta, yanayin jikinta duk yaa fara yin sanyi,
    Ya ɗan buge bakinsa da hannu,
    "Awwh Sorry ci gaba"

Shiru tayi da alama ta lula duniyar tunani,
      "kici gaba, ko kina buƙatar wani taimakon nawa ne?"
    Ya koma daga bayanta, ya ɗan saka ƙafarshi kaman zai ture stool ɗin, da sauri ta saka hannayenta a wuya ta riqe igiyar tana jan firgitacciyar ajiyar zuciya, ya mai da stool ɗin yanda yake.
         "Mutuwa babu daɗi ko? Ki kwantar da hankalinki, bazan janye Stool ɗinnan ba, idan nayi hakan ahh kaman nina kasheki, bazaki ɗauramun laifin kisan kai ba"
    Ya ƙarasa maganar yana ware hannuwanshi.

Cikin zafin rai taja wani siririn tsoki can ƙasan maƙoshinta, sai kallonshi take tana maida numfashi, kaman ta shaƙeshi ta huta takeji, ya ɓata mata shirinta na yau, idanunta kaman su ɓalle saboda hararar da take aika mishi, kafin ta sauka kawai, ta faɗa cikin motarta, ta jata da gudu ta bar wurin.

Ta fasa kashe kanta ne?
Meye Sanadin da take son kashe kanta?
Wacece ita ɗin?
Zata ƙara haɗuwa da wannan saurayin daya kawo mata cikas?

Muje zuwa domin amsa dukkan tambayoyinku

Rabiatu sk msh

Popular Posts

 
]]>All content on thisblog are copyright protected and cannot be reproduced on other websites without permission.