New Post

Thursday, 5 January 2017

HARAMTACCEN ZAMA 45-46

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                 45-46

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   Tun daga ranar Majeed ya k'ara ninninka kulawan da yake bama Majeeda, tana ɗauke da cikin ne kawai anma komai yi mata yake, su Umma ma kullum cikin aiko mata ciye-ciye suke, ba'a ɗaukar lokaci zatazo ganinta,

  Cikin nada wata bakwai momie tace zata maida ita gida, ya marairaicema Aunty Zainabu,
   "Aunty Zainabu yanzu mena gaza wurin yima majeeda? Ynzu kun tafi da ita wata nawa kenan bazan ganta ba? Plx Aunty don Allah ku barmun matata"
    "Aiken momie ne fa ya zance mata knan? Haihuwar farko ce yama za'ay ka iya kula da majeeda"
  "Tohh Aunty idan na samo mata mai aiki fa?"
     "har k'ara hakan, anma dai ka barta ta koma gida gsky" duk ya rasa yanda zaiyi da Aunty Zainabu kamar ya fasa mata kuka, ya kalli majeeda,
   "kinason kije gida ki barni anan?" kallon Aunty Zainabu tayi sannan ta maida kallonta ga Majeed,
     "Idan kace A'ah bazan je ba"  Aunty Zainabu ta kalli Majeed tana ɗaukar jikkarta,
   "Nasan ma A'ahn zakace, ni naa daina zuwa gidanku inga rashin kunyarnan"
     "Hak'uri za'ai Aunty"
  "oho, ku kuka sani dai"

   Majeeda ta fara k'ok'arin tashi saboda yanda cikin yayi girma,  "Aunty bara in rakaki
"yi zamanki, Allah dai ya raba lafiya" su duka amsa da "Ameen",
   Ya dawo kusa da ita bayan Aunty ta tafi,
     "Ban kyautah ba ko Majeeda?"
    "A'ah itama Aunty ai taga kana kula dani sosai"
   "Bazan iya jurar rashinki ba koda na kwana ɗaya ne"
   "nida babynmu ma bamuso muyi nisa dakai"
     "Yauwah tawan" ya kwantotah jikinshi, ya fara shafar cikinta,
    "babyna nason hutu, muje ku kwanta" ya fara k'ok'arin ɗaukarta, ta rik'o hannunshi,
   "nifa na gaji da kwanciyarnan, yanzunnan fa ka taso ni zuwan Aunty"
     "Tohh ay nafison kina kwanciya ku huta"
   "nidai hakanan, likita ma yace ina motsa jiki ai"
  "tohh naji kuɗan zauna"

   Ta kamo hannunshi ta rik'e cikin sanyin murya tace "Yauma bazaka kaini wankin kan ba?" ya k'ara damk'e hannunta cikin nashi,
    "ki gane mana, nifa banso ku wahala ne"
   "nidai gsky yayi datti sosae"
  "tohh zan wanke miki, shknan?" ta rik'e bakinta tana daria,
      "ina ka taɓajin namiji da wanke kai?"
    "A gidan Majeed da Majeeda" ya bata amsa yana murmushi,
   "meye a ciki? Nima fa ina wanke nawa"
   "hakane tohh muje toilet ɗin"
   "toh ina zuwa" ya tafi da sauri ya kai mata doguwar kujera a toilet ɗin, ya haɗa ruwa mai ɗumi sannan ya taho ɗaukarta,
  
   Harta k'ok'arta ta mik'e, tana tafiya dak'yar,
    "Yanzu sai dai kin tashi kin bama babynmu wahala?" ya taho zai kamata,
     "nidai ka barni plz, nan da toilet ɗin"
   "naji taho in rik'e ki tohm" dak'yar ya barta ta tafi ita kaɗai, ya gyara mata kujera ta zauna,"

    Hannunshi ya ciko da shampoo ya lafta mata, sannan ya fara gogawa a hankali kamar wanda baison taɓa kan, ta saka hannuwanta duka biyun a kumatu tana kallon ikon Allah ta mirrow,
   Kusan 15mnts kumfa bai gama haɗewa ko ina ba, ta saka hannu ta shafi kan,
    "Yaya majeed a haka yaushe zai wanku?"
    "zai wanku mna, bazan dai miki yanda zakiji zafi ba"
   "wankin kai ma har zafi ne dashi? Nidai bara inyi da kaina,
    "in barki kisha wahala kenan, indai kin gaji a bari sai gobe" haka tana ji tana gani ya dinga lallaɓawa a hankali yana wanke mata, daya murza sau ɗaya sai ya kwaraya ruwa, dak'yar ta mishi dubara tana wankewa yana zuba mata ruwa,
 
   Babu inda bai jik'e ba a jikinsu kafin ya gama wanke mata kan, sai da duk suka sake wanka sannan suka fito,
    Akazo wurin drying, da hand dryer yake busar mata da kan yana sharcewa, haka ya dinga soka comb ɗin yana zarewa, ba don ya shartu ba ya tattara mata abinta ya k'ulle,

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MAKASHINKA 65-66```MAKASHINKA...```           65-66 ©Rabiatu sk msh ƘARSHE Sadeey Sai zagaye ɗakin take cikin fargaba, a zuciyarta kuma addu'ar samun nasara kawai take, kasa haƙ… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 21-40[10:39, 3/10/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣Soyayyar whatsapp❣ @OHW 21-30 Tana bude datar messages da yawa suka shgo mata, anma naashi ta fara dubawa, da wayarta glaxy s5 wadda Abokinta A… Read More
  • MAKASHINKA 61-62```MAKASHINKA...```           61-62 Washe gari... Aka mik'a shamsuddeen a gaban kotu, *A KOTU* An cika a kotun kowa yana jiran yaji ya wannan shari'ar zata kasance, Bayan alkali y… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 1-20[10:36, 3/9/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣Soyayyar whatsapp❣ @OHW 1-10 Kishingide take saman lumtsumemiyar kujerarta 2seater da remote a hannunta! Masu aiki nata yi mata hidima, daya dga… Read More
  • MAKASHINKA 63-64```MAKASHINKA...```           63-64 ©Rabiatu sk msh Damuwah ta ƙara yima sadeey yawa, kwana ukku ta ina zata samu hujjojin da kotu zata gamsu baida laifi? Ya Anwar ta kir… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts