New Post

Sunday, 22 January 2017

HARAMTACCEN ZAMA 81-82

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  81-82

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

Qarshe🤗

www.babymsh.blogspot.com

   Bayan ta samu wuri taa zauna, Abban Majeed yayi gyaran murya ya fara Magana,
      "Wannan karon ba Umarni bane muke baku, shawara ce muka yanke kuma duk saida amincewarku, abinda ya faru mu ɗauka k'addara ne, yanzu kuma dama ce garemu, mu cika Alk'awarin da mukai ma mahaifinmu, muna fatan wannan karan bazaku bamu kunya ba"
   Momie ce ta nisa, tun kafin kowah ya fara magana "Gaskia ni ban yarda da wannan hukuncin ba" su duka suka juyo suna kallonta, taci gaba da magana cikin fahimta,
      "Su duka yanzu ba k'ananun yara bane, kun manta abunda wancan haɗin ya haifar? Shiyasa ni ban cika magana ba, anma gaskia wannan lokacin bazan yarda a k'ara musu dole ba,  su koma halin da suka shiga wancan lokacin ba" Daddy ya katseta
    "Waye yace dole za'a musu? Suna da damar da zasu faɗi ra'ayoyinsu, karki manta da Alk'awari ne muka ma Mahaifinmu, ba don haka ba koda kansu suke so bazamu taɓa k'ara amincewa ba, kuma yanzunma idan har basu so bazamu k'ara tilasta su ba" shiru tayi bata k'ara magana ba,
   Abbah yace "ku muke saurare", Majeeda kanta a k'asa tun tana kuka a hankali harta fara shesshek'a, Majeed ma sai dai tashi yayi ya fita, fuskokin iyayen nasu duk ta nuna rashin jin daɗi, sunyi jugum kowa ya kasa motsawa, message ya shigo wayar Aunty zainabu, ta ciro ta tana ganin daga Majeed ne ta buɗe da sauri, da k'arfi ta karanta yanda kowah zaiji,
    "Ki tayani godia Auntynmu, kunyarsu ta hanani furta komai, sun nuna mana soyayyar da babu abinda zamu biyasu da ita, Allah ya saka musu da mafificin Alkhairi, ya k'ara musu tsawon kwana" kowa a ɗakin saida ya murmusa, sunyi farin ciki sosae, Majeeda ma murmushin jin daɗi take, ta mik'e da gudu ta fita, kunya bata barta ta jira kowah ba, ta shige motarta ta wuce gida,
   Cikin lokaci kaɗan aka fara hidimar biki, shagali sosae akayi wanda ko bikinsu na farko ba'ayi ba, cikin sati biyu aka gama komai aka kai Amarya ɗakinta,

   Bayan en rakiyarta sun gama tafiya, ta shek'a wankanta, tayi kwalliya ta fitar hankali, ko ina jikinta k'anshi yake, ga wata doguwar riga data saka ta daifi babu, irin shigarda tasan Majeed yafiso, sai dai ta ɗaura zani daga sama,
     Yana shigowa tsaye yayi a k'ofa yana kallonta, duk'arda kanta tayi sannan wata irin kunya ta saukar mata, ya ware mata hannuwa alaman tazo ya rungumeta, cikin zolaya tace "yau kuma ina laidan da za'a jefeni da ita?" daria yayi,
    "rufamun asiri zaki jamun ɗauri," itama tayi dariya,
   "nayi alwala fa, kai kawai nake jira"
    "tohm ranki shi daɗe"
  Ya shiga yayo alwala, ya fito, Sallah sukayi raka'a biyu kamar yanda manzon Allah ya koyar damu, ya daɗe yana kwararo musu addu'ar zaman lafiya, sannan sukai godia ga ubangiji,
    Ya rausayar da kanshi yana kallonta, rayuwarsu ta bayace ta dinga dawo mishi, wata irin soyayyarta na k'ara ratsashi, itama kamar hakan takeji, ta hure mishi idanu,
    "ka faɗa mana"
  "na rasa mezan faɗa ne, kullum k'ara kyau kike, bazaki taɓa tsufa ba"
   "kaima hakanne, babu wanda zaice kana da kaman Abdallah"
   "bazan iya bayyana miki farin cikin da nakeji ba da dawowarki gareni, wallahi ban taɓa sanin ina sonki da yawa haka ba saida na rasa ki, HARAMTACCEN ZAMA, ya k'are, Allah ya bamu ikon farantama juna har k'arshen rayuwarmu"
     "Ameen" ta faɗa

GODIYA
   Ta tabbata Ga Allah daya bani ikon kammala littafinnan lafiya, tsira da Aminci su k'ara tabbata ga annabinmu Muhammad (S.A.W), kuraren da suke ciki Allah ya yafe mana, Ameen,

Bani da bakin godia gareku Masoyana nesa da kusa, inajin daɗin yanda kuke nuna soyayyarku ma littafinnan, Allah yabar k'auna, sai kunjini a sabon littafina K'IYAYYA, anma bayan na dawo daga jigawa wurin kishia😊 labarin A HANYAR JIGAWA, yananan tafe ba daɗewa domin nishaɗinku,
   domin gyara ko shawarwari
      +2348032133670

SADAUKARWA
   wannan littafin sadaukarwa ne ga dukkan jikokin Alhaji sani katibu, duk sunayensu ne a ciki
     Manyan gobe, Allah ya raya mana ku ta farkin addinin musulunci, ya zaɓa muku abokan zama na gari, Ameen

IYAYENA
Allah yaji k'anshi mahaifinmu da rahma ya gafarta mishi, Allah ya k'ara tsawon kwana momienah, Allah ya saka miki da gidan Aljannah, hak'ik'a Uwah ce ta gari, ina sonta fiye da rayuwatah!

   NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
    Ina Alfahri daku, Allah ya k'ara ɗaukaka, ya k'ara mana haɗin kai,

Godiya ta musanman,
   Da taimakonka ne na fara littafinnan harna k'areshi, ILILEE, nama rasa ta yanda zan gode maka, Allah ya k'ara basira, Ameen

AMINAN JUNA
   K'awaye na gari, babu kamarku a zuciyatah, RAZ, k'aunarku dabance a cikin zuciyatah, kalmomi bazasu iya bayyana farin cikin da nakeji kasancewarku cikin rayuwatah ba, Amrah A msh and Zahra bb, Allah ya bar tare.

   Beelybadaru, kina raina a koda yaushe😊

  En uwanah writer, gaisuwa mai yawa a gareku, Allah ya k'ara basira ya k'ara mana haɗin kai baki ɗaya,

    Duk group ɗin da nake ciki da wanda suke samun littafina, ina mik'a gaisuwa mai yawa gareku, Ma'assalam

Taku har kullum
    Rabiatu sani katibu mashi🙋🏻

Related Posts:

  • HAKKIN KISA 66-70☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽             66-70 ©Rabiatu sk msh       … Read More
  • HAKKIN KISA 71-75☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽             71-75 ©Rabiatu sk msh       … Read More
  • HAKKIN KISA 56-60☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽             56-60 ©Rabiatu sk msh       … Read More
  • HAKKIN KISA 61-66☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽             61-66 ©Rabiatu sk msh       … Read More
  • HAKKIN KISA 76-80☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽             76-80 ©Rabiatu sk msh       … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts