New Post

Thursday, 5 January 2017

HARAMTACCEN ZAMA 51-52

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  51-52

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

Ranar suna yaro yaci suna Abdallah, ba k'aramin shagali akai ba a wannan rana, gida yaa cika da mutane, Anyi abinciccika kala-kala, nama ko ko shi kaɗai kakeso sai kaci ka k'oshi, ga gassasun kaji da soyayyun ma,
    Kayan barka ma Majeeda ta samesu harta rasa wurin ajjewa, banda kudaɗen data samu, gida cike da jama'a babu masaka tsinke, muryarta harta soma shak'ewa saboda hidima da jama'a,

    Tana cikin canja kaya text ɗin Majeed ya shigo mata,
    "Hey babe, i cant stop thinking about uh koma me nake ke nake gani, ina kewarki plz bzan ganki ba?" sai da ta ɗanyi murmushi sannan ta maida mishi,
    "miss uh more dear, hidimar jama'a sai a hankali, zaima zama abun magana idan nace zanzo"
   "plz babe, kwalliyan kawai zan gani" sai da ta ɗauka lokaci sannan ta maida mishi amsa, saboda yanda mutane keta shigowa,
   "ka duba pics a whatsapp yanzu"
   "nidai ban yarda ba, ga frnds ɗina ma zaku gaisa, sunata so su ganki"
    "Wlhy babu damar barin ɗakinnan fa, muyi waya dasu mana?"
    "Shikenan bazaki zo ba"
   "M srry nawan"
   "owk ki samamin lokaci da dare plz"

    Bata mishi reply ba wata frnd ɗinta ta anshe wayar, suka ci gaba da fira, haka a gajiye ta k'are hidimar, bata samu zuwa ba sai dai suka sha waya da dare,
   Washe gari su Aunty Zainabu suka dawo gyara mata gida saboda yanda aka ɓata ko ina, tare da wasu mutanenta da Zahra suka shiga gyaran,
       Tana can cikin bedroom ɗinta ta fara jiyo magana kamar ta hafsatul kiram sama-sama, gabanta ne yayi mummunan faɗuwa, ta tashi a hankali take tafiya zata lek'a taga kowacece, sukai kociɓus da ita tana shirin shiga bedroom ɗin,
    Sai da taja ta baya kamar wacce taga Abun tsoro,
     "Amaryar jego"
   "ke kuma haka ake dawowa babu labari?"
    "daman ayna faɗa miki mamaki zan baki" ta k'arasa inda Abdallah yake kwance ta ɗaukeshi,
     "Masha Allah, wannan kyakkyawan babe"
    Ita dai Majeeda binta kawai take da murmushin yak'e ko zama ma taa kasa yi, hafsat ɗinma ganinta take kamar wata mutum daban,
    "Ki zauna mana, kinsan ina da tarin tambayoyi sosae a baki na" duk taa ruɗe take magana,
   "tambayoyi kuma? Ay kya bari dai kisha ko lemu ne"
   "Haba gidanki nazo fa, kamar dai wata bak'uwa"
   "saiki zama bak'uwar mana tunda zuwanki na farko ne, kedai bara na kawo miki"
     "nidai ki barshi ki zauna" bata saurareta ba ta nufi hanyar fita, tana mata magana anma saida ta fita,
   Zahra ta rok'a Alfarma, ta kai mata drinks ɗin, sannan ta samu wuri inda su Aunty Zainabu suke ta Zauna, don ganin hafsatul kiram take kamar wata surukarta,
   Saida ta aiko kiranta ba don taso ba ta tashi ta tafi,

   "kin ganmu nan aiki muke ta fama dashi"
   "Shine kuma zaki barni ni kaɗai zuru"
     "kizo mu tafi falon mana kamar wata bak'uwa" ta mike zata tafi, hafsatul kiram ta kamo hannunta ta zaunar da ita, kanta ta dafe daya fara sara mata,
    "Daga ganin yanda kike kauce-kaucennan ya tabbatarmun da baki da gaskia, plz majeeda karki tabbatarmun da zargin da nake miki na HARAMTACCEN ZAMA kuke da Majeed"
    "kinga wannan ba lokacin da zamuyi maganar nan bane,"
    "sai yaushe zamu yita? Ko kina nufin wani auren kikai kika fito sannan kuka maida aurenku?"
    "keni babu wani auren da nayi, daman can wasa nake miki babu wani raba auren da mukai da Majeed" ta faɗa kanta a k'asa,
     "da gaske kike?" hafsat ta tambayeta tanason haɗa ido da ita,
    "da gaske mana"
  "k'arya kike Majeeda, akwai yanayin da mutum zaiyi wasa da kuma yanayin da mutum zaiyi magana a gane gaske ne, yanda kukai aure da Majeed babu abinda bazaku iya yi ba"

   Kuka ta fashe dashi, don kalmomin da zata kare kanta sun k'are mata, Hafsatul kiram ce kawai tasan matsalarta, kuma itace rufin asirinta, tasan zata bata shawara mai kyau,
   "ina sonshi hafsa, ina matuk'ar sonshi, bansan ta yanda akai na fara sonshi ba, anma bazan iya rayuwah babushi ba, ke kaɗai kikasan sirrinmu, shiyasa muka yanke shawaran muci gaba da rayuwanmu a haka, koda mun faɗa a gida tsinuwa ne kawai, Bama zanso abinda zai rabani dashi ba" hafsatul kiram hannunta har kyarma yake,
   "kina nufin bayan ya miki saki Ukun kuke zaune a tare?"
   "eeh don Allah ki taimaki rayuwatah karki faɗa ma kowa, wlhy bazan iya rayuwa babushi ba" duk ta rikice mata, tana kuka tana rok'arta, sai rirrik'eta take,
     "plz hafsa kicemun bazaki faɗa ma kowa ba"
     "Abunda naketa faɗa miki kenan Majeeda, anma ko sauraratah bakiyi ba, Yanzu idan kuka mutu a haka me zakuce da Allah? A haka zaku zauna kuna tara yara? Wata k'ila ni kaɗai nasan sirrinku a yanzu, kuna tunanin harku mutu Allah bazai to na asirinki ba? Duk son da kuke yima junanku bai kamata kuyi irin wannan zaman ba, kiyi tunani wannan ba soyayyah bace da zaku kai kanku da halaka, in banda abunki....."
     "Plz hakanan nidai, naji shawaranki, nidai kicemun bazaki faɗa ma kowa ba"
    "Abinda ya dameki kenan? Naji bazan faɗa ba Majeeda, sirrinki da yafi wannan ma ni mai rik'e miki ce, wannan Alk'awari ne tsakaninmu"
    Cikin farin ciki Majeeda ta rungumeta tana murna,
    "Na gode sosae Aminiyatah"
     "babu godia tsakaninmu"
Sannan ta ɗago fuskarta tana ci gaba da murmushi,

   Cak, fara'ar fuskarta ta ɗauke kamar wacce aka faɗa ma sak'on mutuwa, jikinta yahau rawa, hango Aunty Zainabu da tayi tsaye a k'ofa ta tsura musu ido,

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MARYAM KO MARYAMA 191-200[15:32, 3/24/2016] Rerbee'art sk: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 191-195 Ranar aka daura auren Maryama da Ahmad, tana zaune ta qura mishi ido ko qiftawa batayi tama rasa mezatayi, d… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 156-170[10:00, 3/22/2016] Rerbee'art: [09:42, 3/22/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 156-160 Sunzo shiga dakin maryam, caraf Maryama ta ji deen ya qanqame hannun ta juya suk… Read More
  • A YINI ƊAYA 1-2[11:20pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀     💀💀           💀💀  … Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 171-180[17:49, 3/23/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 171-175 Da dare suna zaune suna fira da Maryam taaje yi mata sai da safe, Maryama tace "namcy kin wani shgo kin kwanta … Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 191-100[15:32, 3/24/2016] Rerbee'art sk: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 191-195 Ranar aka daura auren Maryama da Ahmad, tana zaune ta qura mishi ido ko qiftawa batayi tama rasa mezatayi, d… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts