New Post

Thursday, 5 January 2017

HARAMTACCEN ZAMA 49-50

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  49-50

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

  Awa shidda tayi aka sallameta, Asibitin cike da family ɗinsu, haka suka cika motoci suka nufi gidan Majeeda da Majeed,
      Anan ma saida Umma taso ta tafi da ita gidanta tayi wankan Arba'in, anma Majeed yak'i amincewa, shida kanshi ma yayi driving don kar Umma tace dole sai an kaita can,

  Murna sosae su Abba sukai da jaririnnan kasancewarshi jikansu na farko, duk da a yanzuma aunty Zainabu na ɗauke da juna biyu,
   Kyautar tsantsararren gida Abba ya musu, zasu koma bayan suna,
      Kullum gidan cike da Mutane kamar a ranar ne suna, su Majeeda ba zama sai hidima da jama'a kullum Majeed cikin k'orafi yake bata bashi lokaci,

   Zahra takai mishi abinci yace ta turo mishi da Majeeda, fitowarta wanka kenan, saida ta ɓata lokaci wurin shiryawa, nanma dak'yar k'awayenta suka barta ta tafi, jaririn na kukata ɗaukeshi kawai suka tafi ɗakin babanshi,
    Tana shiga ya maida k'ofar ya kulle, da dubara ta ajje babyn, tun kafin tayi magana ya haɗa bakinshi da nata, sun daɗe a haka tun suna a tsaye har suka zauna gefen gado, kukan babyn ya saka suka tsagaita, ya zauna yana kallonsu ta saka mishi abincinshi a baki,
   "ko kewata bakiyi ko?"
  "Fiye da kaima Yaya Majeed"
     "ban yarda ba, tun haihuwar yaronnan kika daina kula dani, baki damu da cina ba, baki damu da kizo kiga yanda na tashi ba, idan bana kiraki a waya ba bazaki kirani ba"
   "ka yarda dani Yaya Majeed komai nake kana cikin Raina, ni kaina na k'agara a gama hidimarnan" ya mik'a hannu ya ansheshi bayan yaa gama sha,

    "Na kaasa koyon barci ba tare dake ba"
      "nima haka dear, yanzu ai na kwana biyu ne kawai"
   "Yayimin yawa fa,"
  "kaaci abinci?" kai ya girgiza mata, da sauri ta tafi ta zubo mishi, ta zauna ta bashi saida ta tabbatar ya k'oshi sannan ta k'yaleshi, taa daɗe har saida aka mata waya tayi bak'i sannan ta koma ɓangarenta,

   Tana ganinsu ta saki fara'a,
   "laah! Asiyah kardai ku cemun kune sai yau"
    "donma kin ganmu kenan, mu da ba'a faɗa nawa ba?"
   Fatima tace "ke kike maganarmu, yanda suke da hafsatul kiram ma ko ita bata faɗa mata ba" sai da gabanta ya faɗi da suka ambaci hafsatul kiram, na'urorin jikinta ne suka dakata da aiki na wani lokaci suna magana ma anma ko saurarensu ba tayi,
   Sai da Asiya ta taɓota, sannan ta dawo daga tunaninta duk ta rikice, ta fara murmushin yak'e,
   "Wa? hafsatul kiram? Kema kinsan bata k'asarne, kuma na rasa numberta tunda ta canja sim"
     "itama haka tace sanda na faɗa mata haihuwarki, halan tunda ta tafi bakuyi waya ba?" kai Majeeda ta ɗaga ma Fatima, sai kuma ta zaro ido da taji abinda tace,
    "kika faɗa mata na haihu, ya akai kika faɗa mata?" duk suka tsaya suna kallonta ganin yanda duk ta rikice lokaci ɗaya, Aunty Zainabu dake tattara wankin baby ta kalleta shek'ek'e,
    "miye don An faɗa mata?" ta k'ara washe hak'oran yak'e,
   "Ba komi Aunty kawai dai naso in bata mamaki ne"

   Fatima tace "kinga barama na mata waya ta fara miki k'orafin rashin kiranta tun yanzu" Majeeda sai k'ok'arin dai daita nutsuwarta take, ita tsakaninta da Allah ko tunawa da hafsat bata sonyi, tana cikin tunani Fatima ta mik'o mata wayar,
    "Aminiyatah!!" inji hafsat,
  "Na'am, Amaryar Umar shikenan an manta da mutane babu wani zumunci"
     "Haba! Ni zance miki haka, har ki sake aure bazaki sanarmin ba?"
  "Wai Aure? Ni ɗin?"
  "tohh daa wa?"
    "kinga besty zan kiraki, kinsan hidimar jama'a, yaushe zaki dawo?"
    "nan kusa, amma bazan faɗa miki ba nima, ki gaishemin da baby" a sanyaye tace "zaiji" sannan ta saki ajiyar zuciyah bayan ta kashe wayar,

   Basaina faɗa muku ba, kunsan nutsuwa taa k'are ma Majeeda a wannan rana, haka ta yini da tunani sosae, duk taa shiga damuwa,

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • ABDUL WAHAB 36ABDUL WAHAB 36 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Kwana biyu tayi suna jinya ita da Abdul, ko motsi zatayi ji yake kamar yayi mata, kulawa sosae yake bata, yaa tattara ya daw… Read More
  • ABDUL WAHAB 32ABDUL WAHAB 32 ©Rabiatu sk msh          ®NWA Kusan kwanan zaune yayi yana fad'ama Allah damuwarshi. Tunda safe yana shirin tafiya office wayar hajia ta shigo mishi, ya d'auka … Read More
  • ABDUL WAHAB 33ABDUL WAHAB 33 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Har dare yayi bai dawo gidan ba, yana tunanin rigimar sadeey ya rasa ta inda zai b'ullo mata ta yarda da son da yake mata. H… Read More
  • ABDUL WAHAB 34ABDUL WAHAB 34 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Fatyma ta dafa kafad'arta cikin tausayawa tace "shi yayanmu ne yake miki hakan? Cikin jin haushi tace "A'ah ni nakeyi mishi,… Read More
  • ABDUL WAHAB 35ABDUL WAHAB 35 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Mi'kewa tayi zumbur kamar antsikareta, idonta harya fara canja kala, dai-dai sanda Abdul yaturo 'kofar d'akin ahankali yashi… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts