New Post

Thursday, 5 January 2017

HARAMTACCEN ZAMA 55-56

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  55-56

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   "Aunty dgsk sabon gidan zaki kaini?"
   "da gaske mana, idan ba can ba ina zan kaiki?" shiru tayi sannan hankalinta ya fara kwanciya,
    "da tunanin me kikeyi?"
"ba komi Aunty, mu tafi" tana maida mata murmushinta, suka fito suka tafi, sai jan Aunty take da labari don ta tabbatar ba haushinta takeji ba, ita kuma taci gaba da biye mata,
   Bata ankara ba ta gansu hanyar gidansu Majeed, ta ɗago fuskarta cikin wani hargitsin tana kallon Aunty, tun kafin ta mata magana ta rigata,
    "Zamu biya ki musu ban kwana ne" sannan ta saki ranta, hankalinta kwance suka shiga gidan, kai tsaye ɗakin Abba suka wuce

   Kowah ya haɗu a ɗakin kamar ana wani taro, Daddynta da Momie, Umman Majeed da Abbanshi, harda Zahra ma, Majeed ta hango shima zaune, anma bata ga alaman damuwa a fuskarshi ba don shima ba'a mishi maganar ba, kuma bai taɓa kawowa a ranshi zasu san da maganar ba,
   Ganin haka itama bata damu da ganinsu ba, don bataga alamar Aunty taji maganar da tayi ba, suka samu wuri saman carpet ita da Aunty suka zauna, suna satar kallo ita da Majeed,

   Abban Majeed ne ya fara magana "bamu zauna nan don ku mana k'arya ba, ko mu saurari wani shirme naku, kun riga da kun gama kaimu k'arshe, ku faɗa mana tsakaninku da Allah wanne irin zama kuke tsakaninku"
  Ba wani shakku a ran Majeed yace "irin zaman da kukeso muyi Abba, mun daina faɗa, ina bata duk wani hakk'inta na aure, ka tambayeta kaji" tun kafin a tambayeta ta amshe
   "sosae ma kuwa Abba, yana kulawa dani, muna zaman mu lafiya"

Daddy ya jefa musu da tambayar da duk saida ta kusan katse musu en hanji,
   "Bayan kun raba auren naku kenan?" duk suka fara muzurai irinna mararsa gaskiya, dak'yar Majeed ya iya k'arfin hali,
     "Raba Aure kuma daddy kamar wasu mararsa hankali, mema zaija mana raba aure?"
   "Wa kake tambaya cikinmu?" inji Abba,
    "daman ina hankalin yake? Ban taɓa tunanin zaku iya aikata hakan ba, kun munafunce mu, kuma kun cuci kanku..." Majeed da har yanzu baisan yanda akai ba, yayi saurin cewa
   "Abba mufa ba abinda muka aikata, idan ma wani ne yakeso ya haɗamu daku wallahi sharri ne"
    "waye zai muku sharrin cikinmu? Koda yake, daman kun daɗe da maidamu shashashai tunda har kuke tunanin bazamu gano zaman da kuke ba" Abba ya mik'a hannu ya ansa wayar Aunty Zainabu data ɗauka kusa dasu, ta kunno recordn ɗin maganar Majeeda da hafsa yanda kowa zaiji,

   Majeeda kamar ta zunduma da gudu, tama kasa zama kamar wacce zafi ya kama, hawaye ne kawai ke kwararo mata ta ko ina, tunda take bata taɓa shiga tashin hankali haka a rayuwarta ba, tama kasa ɗaga kai ta kalli kowa, Majeed ma tunda ya ɗukar da kanshi bai k'ara ɗagowa ba, zufa kam rigarshi harta jik'e,
   Ɗakin yayi shiru, sai sautin kukan Majeeda dake fita a hankali,
   "Shima wannan ɗin sharri ne?" Abba ya tambayesu,
  "Anma na rantse Abba babu abinda ya shiga tsakanina dashi..."
  Wani irin k'wallo Daddy yayi da ita,
    “shi cikin Abdallahn a ruwa kikasha cikinshi? Ko har yawon iskanci kike fita?" tai saurin rik'e bakinta, tana dafe inda daddy ya sa mata k'afa saboda zafin da yake mata, idanunshi sunyi jajir da ɓacin rai,
   Sai lokacin takai kallonta ga Momie, ta duk'arda fuskarta tana share hawaye da alama kuka take, wannan wane irin tashin hankali ne yau take gani?

   Abban Majeed ma cikin rawar murya da alama dauriya yace,
   "kun cucemu, kun karya duk yarda da mukai daku, Alk'awari ne mukai ma mahaifinmu, Anma a sanadiyyarku mun kasa cikawa, Allah ya gani munyi iyakar k'ok'arinmu, anma kun nuna mana baku isa ba, HARAMTACCEN ZAMA?, bansan a ina kuka samo wannan tarbiyyar ba, kuma kunyi kaɗan kuce mune muka baku ita, me kukeso jama'a suce a kanmu? Mun muku auren dolene kuka maida kanku haka? Wlhy k'arya kuke duniya ta zagemu a kanku, bazamu taɓa yafe muku...."
   Umma tace "duk meya kawo hakan Alhaji? Yanzu kuma inka musu baki ya kakeso su zama?"
    "harna yaushe kuma? ZAMAN DADIRO fa, wallahi zaifimin daɗi ace mutuwa sukai da inga wannan rana" duk k'arfin halin da Abba yake  da kuka ya k'arasa maganar,
   Can ciki Majeed shima Yace "Ayi hak'uri Abba, kuskure...." wani irin Mazga da Abba yakai  mishi a baki har saida yayi jini, cikin tashin hankali ya buɗe bakin sai gashi har hak'ori ya fita,

   Hakan baisa Abba ya saurara mishi ba, saima ya tashi ya rufeshi da duka ta ko ina, daddy na rik'eshi anma kamar yana k'ara mishi k'arfi, shiko Majeed ko motsawa baiyi ba, yana zaune yanda yake Abba na jibgarshi, dak'yar daddy ya k'waceshi ya matsa sai huci yake,
    "ka k'yaleni in kasheshi in huta da wannan bak'in cikin nashi, ai duk laifinshine, shine babba kuma sakaran banza, inama amfanin haihuwarshi?"
   "A'ah Yaya, idan har akwai laifinshi tohh nata yafi yawa"
      "laifinta data buɗa baki ta sakeshi? Idan har ya daraja maganarmu bai saketa ba zata saki kanta ne? Ko zata ma kanta ciki ne? Shine lalataccen ɗan iskan da yayi sanadin komi, ita tana da raunanniyar zuciya, da kalamai en kaɗan zai iya galaba a kanta" yana gama faɗi ya shige bedroom ɗinshi,  Umma ta tashi ta bishi,

  Haka su Daddy suma suka fita, Aunty Zainabu taja Hannun Majeeda suka tafi anan kowa ya watse akabar Majeed kamar wani zararre,
   Saida Zahra ta dawo ta mishi magana sannan ya mik'e ya tafi yana tangaɗi ko kallon gabanshi baiyi harya shige ɗakinshi

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts