New Post

Thursday, 5 January 2017

HARAMTACCEN ZAMA 53-54

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  53-54

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   Wani wahalallen miyau ne ta haɗe da k'yar, tayi tsuru-tsuru da ita kamar wadda aka dasa, buɗe baki tayi zatai magana ta kasa ta bar bakin buɗe tana kallon Aunty Zainabu,
   Jikinta bai tashi kyarma ba saida Aunty Zainabu ta doso inda suke, tana tafiya tana kallonsu fuskarta babu annuri, bata ankara ba sai dai taji ta fara jik'ewa da zufa ta ko ina,
   "Aunty wallahi zan miki bayani, don Allah ki dakata, abinda kikaji ba haka bane"
   Bata tankata ba harta k'araso inda take,  tuni taa gama sandarewa, sai dai taga ta duk'a inda take, ta ɗaga filo ta zaro wayarta, sannan ta juya tabar ɗakin, ba tare data tanka musu ba

   Wata munafukar ajiyar zuciyah ta saki sannan ta juyo inda hafsatul kiram take itama duk taa haɗa zufa, tama fita ruɗewa, (wanda suka karanta littafin hafsatul kiram sun santa da saurin ruɗewa, abu kaɗan ke sakata kuka), tuni hawaye suka wanke mata fuska, harta so ba Majeeda dariya,
     "Akwai matsala fa" inji Majeeda,
   "Matsalan me kina ga batace komi ba, da alama bataji mu ba"
   "Zanyi fatan hakan hafsat, anma nifa hankalina bai kwanta ba da irin kallon da take mana" duk sukai shiru kowa ya rasa abun cewa,

  Sun daɗe a haka babu wanda ya iya cewa komi, k'arar shigowar text ne ya katsesu a wayar Majeeda, duk saida suka firgita, sannan ta daure ta duba, kamar wata marar lafiya,
     "I don't say it enough, but wanted to let you know that I love you."
   "luv uh too i swear, ina ka shige?"
    "cikin zuciyarki...lol ina hanya hope kowa dai ya gama tafiya, ina kewar matata da yawa"
   Ta sauke ajiyar zuciyah, addu'ah ta shiga yi Allah ya kawoshi gidan da wuri, tare da Addu'an Allah yasa Aunty Zainabu bataji su ba.

   Firarma kasawa sukai ita da hafsat, da gudu ta tafi toilet ta zazzagar da fitsarin data kusan saki shigowar Aunty, tana dawowa ta zari jikkarta,
   "Tohh Aminiyah, nidai zan tafi"
   ta tashi da sauri tana gyara ɗaurin zane, "ina kuma zaki tafi ki barni cikin wannan bala'i?"
    "Haba, ki kwantar da hankalinki mana komai zai dai-daita insha Allah, zamuyi waya Ya Umar yana waje"
   "kema fa hankalinki tashe yake taya zan kwantar da nawa?" dafa kafaɗarta hafsat tayi, suka fito tana kwantar mata da hankali,

   Sai dai me? Falonta wayam babu furnitures nata, komai an kwashe kamar sabon gini, duk suka saki baki suna kallo har Aunty Zainabu tazo ta bangajesu ta wuce bedroom ɗin nata tana sauri,
    Kayan sawarta ta dinga kwashesa tana juye mata a akwatunanta, hafsat na ganin haka ta mata sallama ta tafi, bata samu maa ta amsa mata ba,
    Tafiya tayi da sauri inda Aunty take ta rik'e mata hannu,
    "Aunty ina za'a kaimin kayan kike kwasarsu?"
Bata tankata ba taci gaba da kwashewa, sai da ta gama kwashe komai, ko k'yalle bata bari ba ta jasu tayi waje dasu, Majeeda ta k'ara shan gabanta,
    "Aunty don Allah ki faɗamun ina zaki kaimun kaya?" k'ara shareta tayi taci gaba da jan kayan,
   Duk ta ruɗe kuka kawai take kamar wacce ake zare ma rai, ta kwanta nan k'asa kamar k'aramar yarinya tana gunjin kuka,
     "Don Allah ki rufamun Asiri Aunty yanda naki ya rufu, ki taimakeni karku rabani da Yaya Majeed, shine rayuwatah, don Allah Aunty ki tausayamun" idan Aunty Zainabu ta tankata ku da kuke karatunnan kun tanka, haka taci gaba da kuka har muryarta ta soma sik'ewa,

  Tana ji tana gani suka kwashe komai na ɓangarenta,  harta Abdallah goyeshi tayi a bayanta, ta wurga mata mayafi,
    "ki tashi mu tafi nace"
Da tafiyar gwiwa ta gangaro inda Aunty take ta rik'e k'afafunta,
   "ki kasheni ma kawai Aunty, zaifimun sauk'i da rayuwa babushi, don Allah karki Rabani da Yaya Majeed Aunty, ina sonshi" ta k'ara fashewa da kuka hannuwanta rik'e da k'afafun Aunty Zainabu,

   Ji tayi Aunty ta k'yalk'yale da daria,
   "lallai Majeeda bansan sanda soyayya ta rufe miki ido ba haka, ranar da za'a kawoki kin cika ma mutane kunne, 'don Allah karku kaini, bazan iya rayuwa dashi ba,' yau kuma kece da cewa bazaki iya rayuwah babushi ba, Sabon gidan da Dadd ya baku zaku koma, ko wani kike ba ajiyar kuɗin da za'a sake miki wasu kayan?"
   Wata doguwar ajiyar zuciyah ta saki tana jan numfashi, ta ɗago kanta tana kallon Aunty cikin shakkun maganar data faɗa, murmushi taga tana mata,

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MAKASHINKA 39-40```MAKASHINKA...```           39-40 ©Rabiatu sk msh Taaji daɗin furar tasha ta sosae suna ci gaba da firarsu. Sai da maraice yayi sosae sannan Shamsuddeen yazo yafiya da … Read More
  • MAKASHINKA 43-44```MAKASHINKA...```           43-44 ©Rabiatu sk msh Tun daren ranar take saka ran kiran daddy bai kirata ba, har barci ya ɗauketa suna cikin waya da Shamsuddeen daddy bai… Read More
  • MAKASHINKA 37-38```MAKASHINKA...```          37-38 ©Rabiatu sk msh Da sauri kaka ta ɗebo ruwa a buta ta nufota dashi tana mata sannu, suma duk tsayawa sukayi suna mata sannu. Shamsuddeen da s… Read More
  • MAKASHINKA 41-42```MAKASHINKA...```          41-42 ©Rabiatu sk msh Tun daga ranar soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, koda yaushe suna tare, wani bai iya ɗaukar lokaci bai ga wani ba.… Read More
  • MAKASHINKA 43-44```MAKASHINKA...```           43-44 ©Rabiatu sk msh Tun daren ranar take saka ran kiran daddy bai kirata ba, har barci ya ɗauketa suna cikin waya da Shamsuddeen daddy bai… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts