New Post

Thursday, 5 January 2017

HARAMTACCEN ZAMA 47-48

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  47-48

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   Yau taa rigashi farkawa, a hankali ta janye hannunshi daga jikinta, ta kara mishi pillow, sannan ta taho a hankali zata sauka daga saman gadon, sai dai taji ya kwanto jikinta ta baya, yana shak'ar qamshin gashinta, ta sauke ajiyar zuciya tana dariya,
    "yau na makara ko? Har kina shirinmin wayau"
   "A'ah da sauran lokaci fa, ni ɗinma na fasa fita, kai kwanciyarka"
   "nak'i wayon naki, kingama tashi na" idonshi cike da barci ya sauka daga gadon, daman basu daɗe da komawa ba bayan sunyi sallah, ba don tanaso ba ta koma ta kwanta,

   Kamar kullum saida ya tabbatar ta cika cikinta, sannan shima yaci, ya gyara mata kwanciya bayan ya aje mata duk abinda zata buk'ata sannan ya fita office,
    Duk bayan mintuna kaɗan zai kirata yaji ya take, kafin lokacin tashi yayi zuwanshi uku yaga koda abunda take buk'ata, ko kaɗan baison ta nema abu ta rasa,

    Da marece ya taimaka mata ta shirya tsaf, shima da shirinshi ya rik'o hannunta suka fito,
     "Yaya Majeed baka faɗamun inda zamuje bafa"
    "kedai kizo muje"
"plz ka faɗamin Yayanah"
     "babynmu zamu k'arasa ma sayayya" saida ta tsayar da tafiyarta tana mishi kallon mamaki,
   "Yanzu siyayyar baby har akwai abinda ya rage mana?"
    "Shine zamuje mu gano ai, idan an kawo wanda bamu siya ba" mamaki daya mata yawa ma kasa cewa komi tayi,

    Sun kwaso siyayya sosae na baby da nata itama, ɗinkuna harta fara gajiya da yinsu, kayan babynma babu abinda basu siya ba anma duk saida ya k'aro, da ɗan gadonshi mai shegen kyau, shima kala biyu kenan suka siya, duk wani abun da zasu buk'ata sun siya sun aje tun kafin watan haihuwar yayi,
    Watan haihuwarta ya kama, momie da kanta ta sake mishi maganar komawar Majeeda gida, anma ya rufe ido ya bata ha'kuri kawai, haka Umma ma taso ta koma wurinta anma ya hana, sai dai ta tura mata Zahra tana taimaka mata, sunajin daɗin canjawarsu,

****
Tun cikin dare ta fara jin cikinta na juyawa, ana zungurinta, haka ta daure tayi sallahn Asubah tana ta k'arfin halin kar Majeed ya gane batajin daɗi, duk da Zahra nanan saida ya tabbatar ta cika cikinta, da duk wani abunda ya saba mata, sannan ya fita office,
     Haka ta takure wuri ɗaya tanajin ciwon na k'aruwa, ko Zahra ta shigo sai dai ta daure kawai tana murmushin yak'e, harta gama duk abinda take ta dawo ta zauna tayata fira,
    Sai haɗa zufa take ciwo na cinta ita kaɗai, tun tana iya maida ma Zahra harta kasa, ta fara k'ara tana rik'e cikinta,
      Zahra duk ta ruɗe ta kira layin Majeed, yana dai dai kiran Majeedar sai gashi ta kirashi, yayi saurin ɗauka tun kafin tayi magana ya rigata,
   "Zahra Abun yaazo ne?"
"eeh Yaya kayi sauri kazo tana wahala sosae"
   "ganinan yanzu" tun kafin su gama waya ya fito daga office ɗinshi, cikin hanzari ya shige motarshi ya nufi gidan,
   Kafin suje Asibitin Umma ta rigasu, kusan tare sukaje da Aunty Zainabu, haka aka shigar da Majeeda, idanunshi duk sunyi jajir saboda tausayinta, kamar ya tayata kukannan yakeji,

    Ya kasa zama, ya kasa tsayuwa, yana jiyo kukanta har cikin ranshi, duk yanda Umma taso ya Zauna ya nutsu ya kasa, saima ya matsa nesa dasu yaci gaba da safa da marwanshi,
    Tasha wahala sosai har kusan la'asar bata sauka ba, har ana niyar ai mata aiki, cikin ikon Allah sai ga kai ya fara fitowa, dak'yar bayan tasha wahala, ta silalo k'aton jaririnta namiji,
     Kyakkyawan gaske dana kasa tantance da wanda yake kama a cikinsu, dogon hancinshi da gashin girarshi duk na Majeed ne, sai ɗan k'aramin bakinshi da fararen idanuwanshi na Majeeda, gashin kanshi mai sulbi ya kwanta, kamar na babanshi,
   Bayan ankai Majeeda inda zata huta akace su shiga, tunda Majeed ya ɗaukeshi sau ɗaya ya gani ya maida ma su Umma, ya koma wurin matarshi don duk damuwarshi tana a kanta

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • ABDUL WAHAB 28ABDUL WAHAB 28 ©Rabiatu sk msh            ®NWA                    … Read More
  • ABDUL WAHAB 27ABDUL WAHAB    27 ©Rabiatu sk msh           ®NWA                 Shi kuwa … Read More
  • ABDUL WAHAB 27ABDUL WAHAB    27 ©Rabiatu sk msh           ®NWA                 Shi kuwa … Read More
  • ABDUL WAHAB 26ABDUL WAHAB 26 ©Rabiatu sk msh           ®NWA A firgice ta farka, tana fad'in innalillahi wa inna ilaihir raji'un, du'kar da kanta tayi yaa daina mata ciwo, fara tariyo d… Read More
  • ABDUL WAHAB 25ABDUL WAHAB 25 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Da'kyar ta share hawayenta, ni'kab dinta ta ciro ta maida, kanta na 'kara tsananta mata ciwo kamar zai rabe biyu Haka ta fit… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts