New Post

Friday, 6 January 2017

HARAMTACCEN ZAMA 59-60

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  59-60

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

A gurguje..

Bayan shekara ɗaya
Abubuwa da yawa sun faru cikin, ɓangaren Majeeda ta gama makarantarta, hankalinta kwance ta fara mantawa da Majeed duk da abu mai wahala ne ta iya cire tunaninshi a ranta, anma tana k'ok'arin hakan,
      Abdallah yayi wayau, yana ɗan jagwalgwala magana, babu inda bai zuwa yawo koda gudu ne, kakanninshi kowanne ɓangare ji suke dashi, duk da ba'a yayeshi ba anma kusan kullum a gidansu Umma yake yini, ba k'aramin tausayin yaron sukeji ba, Aunty zainabu ma ta haifi ɗanta namiji, Abdul k'adir,

***
Anata shirye-shiryen bikin Majeed da Aisha, anyi hidima sosae duk da angon ba wani nutsuwa gareshi ba, mahaifinta ne ma ya matsa akayi saboda yanda ta guji auren kowa ita dai sai Majeed kullum tana gidansu, duk yanda Majeeda taso ta danne zuciyarta ta halarci bikin kasawa tayi, sai dai ta kulle kanta a ɗaki tayi ta kuka,
   An ɗaura aure, can kaduna state aka kai mishi amaryar don yanaso yayi nesa da gida,

   Dare yayi Amarya na can bedroom ansha lulluɓi ana jiran ango, kamar daren farkonshi da Majeeda shi kaɗai ya shigo da ledar kaji da drinks a hannu, ya tura k'ofar ɗakin zai shiga,
    Daren farkonshi da Majeeda ya faɗo mishi, yanda suka dinga faɗa kamar sun cinye junansu, baisan sanda ya saki laidar ba ya dawo da baya, kujera ya samu a falo ya zauna yana sharar hawaye, ba kaɗan ba yake kewar Majeeda,
     Shiru-shiru Aisha ba ango,  tun tana tunanin yana hanya ya kusan zuwa harta daina ta fara tunanin abinda ya tsaidashi,
   Har k'arfe ɗaya babu Ango, hankalinta fa ya tashi ta fara tunanin ko ina ya shige, shawarar kiranshi a wayane tazo mata, ta ɗauko wayarta ta kirashi, can falo ta dinga jiyo ringing ɗin wayar anma ba'a ɗauka ba, haka ta dinga kira tana katsewa, ta fara tsorata, cikin sadaukarwa ta lallaɓa ta fito falon,

Can ta hangoshi saman kujera yayi tagumi da alama tunani yake, ta daurema zuciyarta ta k'arasa inda yake, sai da ta ɗan taɓoshi sannan yasan da zuwanta,
      "Majeeda ko?" ta tambayeshi tana kallonshi da raunanniyar murya,
    "bazan miki k'arya ba Aisha, naa kasa mantawa da Majeeda, wlhy komai nake ita nake tunawa" cikin sigar lallashi tace,
    "ba abune mai sauk'i haka ba hniee, anma insha Allah nayi maka alk'awarin maye maka gurbinta, zan zame maka mace ta gari, zan maka dun abinda zai faranta maka in guji wanda zai ɓata maka, zan nuna maka soyayya fiye da wacce kake tsammani, ina sonka da yawa hniee"
   "ngde Aisha, kiyi hak'uri kinji, insha Allah zanyi k'ok'arin daina tunaninta"
    "ba komai fa hniee, taso muje ka kwanta, tunanin ya isa haka," haka taci gaba da lallashinshi da kalamai masu daɗi har sai da ta tabbatar hankalinshi ya kwanta,

   A daren ranar Majeeda tayi kukanda bata taɓayi ba tunda tazo duniya, yanzu ne ta k'ara tabbatar ma kanta da taa rasa Majeed, daman Momie ta faɗa mata namiji ba'asha mishi alwashi, shknan har yayi aurenshi,
   Ga wani ciwon kai daya matsa mata ko barcin ta kasa, ita kaɗai a ɗaki Abdallah na wurin momie yayi barci tace a barshi tunda ba tashi yake ba, sai faman shafa confo take a kai,
    Abubuwa sun mata yawa kamar ita kaɗai damuwa ta k'are mawa, ga faɗan Abba kullum maganarshi ta fiddo miji tayi aure, kamar tana zaune a saman kansu,
   Tohh ita wama zata aura? Ita da ba fita take ba ballantana wani yace yana sonta, inma fitar dole ta kama mata da dogon hijabinta da nik'ab take tafiya, ta saɓa Abdallah a kafaɗa kamar matar aure, dole aji shakkar mata magana,
   Yanzu haka sauran sati ɗaya lokacin da daddy ya bata ya cika, koya aura mata duk wanda yaga dama, ta riga ta hak'ura da koma wanene, tunda ta rasa Majeed bata da wani sauran zaɓi,

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MAKASHINKA 9-10```MAKASHINKA...```          9-10 ©Rabiatu sk msh Tananan zaune har 10pm, saiga momie ta fito, har zata wuce ɗakin Abba ta hangota ta taho inda take tana mata kallon mamaki M… Read More
  • MAKASHINKA 13-14```MAKASHINKA...```             13-14 ©Rabiatu sk msh Khadija bata matsa ba sadeey sai tasan abinda ke damunta ba, ita a ganinta ma ko aljanune suka taɓata, da … Read More
  • MAKASHINKA 7-8```MAKASHINKA...```             7-8 ©Rabiatu sk msh~ A ƙofar ɗakin ta tsaya, tace "bari inyi sauri in shirya ko ya Anwar? Yace "naji anma kiyi sauri plz &#… Read More
  • MAKASHINKA 11-12```MAKASHINKA...```           11-12 ©Rabiatu sk msh~ Zama tayi tana kallonshi cikin jin haushi da ƙara ƙuluwa, duk da haka bai bar dariar ba, saida yayi mai isheshi … Read More
  • MAKASHINKA 5-6```MAKASHINKA...```            5-6 ©Rabiatu sk msh~ Har washe garin dawowarta duk bata cikin nutsuwarta, duk yanda ta ƙagara ta gama karatunta ta dawo nigeria sai ta… Read More

1 comment:

  1. Tnx,Allah ya kara baki ideas,pls am eager to read the continuation.post it here if you have already typed it.

    ReplyDelete

Popular Posts