💖HARAMTACCEN ZAMA💖
♠♠♠♠♠♠♠
77-78
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari...
Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Lokacinda Maryam ta fahimci cikin Majeeda nanan bai fita ba, ba k'aramin kad'uwa tayi ba, ba shiri ta nemo Asiyah har ita suka koma wurin Malam, sai dai sunyi rashin sa'a ya tabbatar musu babu makawa sai an haife cikin, sai dai daga baya zaisan yanda yayi da yaron harma ita Majeedar tabar gidan,
Bayan wata biyar Majeeda ta haifo santaleliyar yarinyarta Mace, ko ban fad'a ba kunsan ba k'aramin farin ciki iyalannan sukayi ba, har Maryam taji dad'in zuwan yarinyar, tun haihuwarta ita take hidima da ita, wani irin soyayyarta take ji,
Ranar suna yarinya taci suna Maryam, shawarar Majeeda kenan, ta dage sai anyima Maryam takwara, ansha shagali sosae, tun ranar haihuwarta har washe garin suna, babu wanda bai shaida da haihuwar Maryam ba, harta da Aisha matar Majeed kullum tana gidan, don yanzu sun zama kamar en uwah,
Kullum Maryam k'arama tana wurin Maryam, tsakaninta da Mamanta sai in tana rigimar yunwa, Shaheed ma acan ya tare b'angarenta wurin d'iyarshi, ita dai Majeeda ta zama er kallo,
Tun tana da shekara guda suka yayeta, sai dai madara, ganin haka Maryam ta koma wurin Malam, da maganarsu ta baya kar Majeeda ta samu wuri tayita haifa ma Shaheed yara, ita kuma ta zama hoto, shima abu ya bada da zata zuba mishi a abinsha, tace "shi yafi komai sauk'i malam" sannan tayi godia ta tafi,
Majeeda na kwance, Shaheed ya shigo d'akin da Marece ne, tayi mamaki sosae don da wuya ya shigo idan ba dare ne ba,
"Sannu da dawowa" baice komai ba yaci gaba da k'are ma d'akin kallo, duk da daman yanzu yaa daina kulata, sannan ya zura hannu Aljihu ya ciro takarda, ta kalleshi da mamaki,
"takardar miye?" cikin yanayin da bai tab'a mata magana ba yace "in faɗa miki da baki mana, idan ni yaronki ne, Ansa ki duba" jikinta ba k'wari ta mik'a hannu ta amsa ta buɗa, Saki Uku ne reras, tana ganin haka ta kulle takardar idanunta cike da hawaye, ita kuma k'addarar da Allah ya ɗaura mata kenan,
"Mena maka shaheed?"
"kawai na gaji da zama dake, babu laifin da kikamun, ki tattara kawai ki tafi, sannan kuma karma ki sakaran tafiya da Maryam, tuntuni na barma Maryam ita" wani irin takaicine ya taso ma zuciyarta, wani irin kallon tsana take mishi,
"Sai yanzu ne na fahimceka, lallai yau na yarda ka cika namiji, watau aurena kayi in haifa maka ɗiya ka cimun mutunci? Lallai idan ance maza DUK HAKA SUKE (littafina mai zuwa), bazanyi gardama ba, saika zauna dasu halayensu da baka taɓa tunani ba zasuna bayyana, ka rusa duk wata yardar dana maka Shaheed, kaci amanatah, bazan taɓa yafe ma cutar dani da kayi ba, kuma Maryam nina haifeta babu inda zan tafi in barta"
"Da ita kikazo? Zaifi miki ma daki manta da ita, don keda ita har abada, kuma kici gaba da zama har in dawo in sameki" ya fita fuuu yabar ɗakin, anan ta zube k'asa tasha kuka sosae kamar ranta zai fita, da kanta kuma ta rarrashi zuciyarta tayi shiru, jikkarta kawai ta ɗauka tabar gidan,
Mai napep ya ajeta k'ofar gidansu, ta fito dak'yar take haɗa hanya ta shiga gida,
Momie da Umma ne a ɗakin tazo gidan, Abdallah ma ya koma gidan babanshi a can ya sakashi makaranta, dak'yar har tana ganin jiri ta faɗa falon, wurin zama a kujera harta kusa faɗuwa, ta jinginar da kanta kawai tana dafe kanta dake mata ciwo sosae, duk suka taso sukayo inda take,
Kasa basu amsoshin tambayoyinsu tayi, sai dai ta mik'a musu takardar dake hannunta, duk tare suka saki salati, sunyi matuk'ar tausaya mata, Umma kamar karta bar gidan don tausayin Majeeda, babu wanda zaiga halin da take ciki bai tausaya mata ba,
A gurguje dai....
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment