☠HAK'K'IN KISA☠
👽👽👽👽
11-15
©Rabiatu sk msh
®NWA
Wahala sosae Abdul ya shata a hannun hukuma, cikin kwana biyu ba aikin da sukeyi saina dukanshi akan dole saiya amsa laifinshi na kisan Hajna, yayi bak'i sosae ya rame, ga tunanin Hajna da bak'in cikin rashinta, abunda yafi damunshi kenan watau mutuwanta.
Tuni daman en uwan Maman Hajna sun k'ara tunzurata ta shigar da k'ara kotu, Abba kuwa ya daina zuwa inda yake, kuma ya hana kowa na familynsu yaje ya ganoshi, sannan kuma yak'i ya ɗaukar mishi lawyer, gaba ɗaya cewa yake ya gama fidda hannunshi akansa. Allah sarki Abdul, kullum cikin kuka yana tunanin yanda rayuwa ta canja mishi lokaci ɗaya.
KOTU
Ranar talata 6june, kotu ta cika mak'il domin sauraren k'arar Abdul da mahaifiyar Hajna ke tuhuma da laifin kashe mata ɗiyarta a daren Amarcinsu.
A lokacin da aka shigo da Abdul mutane da yawa sun tausaya mishi, wasu kuma suna mishi Allah ya qara maganinshi kenan, HAKKIN KISAN dayama matarshi ne ke wahalar dashi, anma fa ko babu zuciyah a k'irjinka dole ka tausayawa yanayin da Abdul ya shiga.
Saida alk'ali ya tsawatar sannan aka tsagaita da surutu, mai gabatar da k'ara ya tashi ya gabatar da k'arar da aka ma Abdul sannan ya koma ya zauna.
Alk'ali yayi gyaran murya "ina lawyern mai k'ara?"
Ya mik'e tare "Sunana Barrister Alqaseem muhd, nine lauyan wanda ke k'ara"
Sannan ya koma ya zauna, Alk'ali ya kalla Abdul "ko kana da lauya?"
Ya girgiza kai bayan ya share hawaye "bani dashi Ya mai shari'ah"
Ya gyaɗa kai sannan yace "lawyern mai k'ara ko kana da tambayoyin da zaka ma wanda ake tuhuma?"
"Ina dasu Yamai shari'a"
Ya mik'e zuwa inda Abdul yake.
"da farko zanso ka faɗamun wanne irin aure kukayi da marigayiyar matarka daka kashe?"
Saida wani abu ya soki zuciyarsa, 'shikenan har Hajna ta zama margayiya' ya tsani ynda ake dangantashi da kisanta, shirun da yayi ya saka Br. Alqaseem ya k'ara cewa.
"ina nufin auren zumunci aka muku, ko kyautarta aka maka ko kuma auren soyayya kukai?"
"Auren soyayya mukai da ita"
"zaku kai tsawon wanne lokaci a tare kafin kuyi aure?"
"zai kai shekara 3"
"tun sanda kuka fara soyayya kake da k'udurin kasheta ko sai daga baya ka canja ra'ayin kasheta?"
Tuni k'afafuwanshi suka fara gardamar ɗaukarshi, k'irjinshi na bugawa da sauri daman can k'arfin hali yake, "Ban kasheta ba, wallahi bani na kashe Hajna ba, soyayyar tsakani da Allah nake mata, ban taɓa tunanin cutar da ita ba" yana magana yana gunjin kuka.
"anma dai ka tabbatar a raye aka kaita gidanka ko?"
"eeh"
Ya juya wurin Alk'ali, "iyakar tambayoyin dazan mishi kenan yamai shari'ah, idan kotu ta bani dama akwai tambayoyin dazan ma mahaifiyar marigayiya Hajna"
"kotu ta baka dama,"
"idan mahaifiyar Hajna na kusa kotu tana son ganinta"
Da sauri ta taso cikin zumbuleliyar hijab ɗinta da cazbaha a hannu tana ja, bayan tayi rantsuwa akan zata faɗi gaskia, Br. Alqaseem ya gyara tsayuwa.
"Hajia maimunatu, ko zaki faɗa mana dangantakar dake tsakaninki da marigayiya Hajna"
"y'atah ce ta cikina, nice na haifeta"
"kina nufin a hannunki ta girma?"
"a hannunah take tun tashinta"
"shin Hajna tana da wata ɓoyayyan ciwone dake damunta? Ina nufin irin ciwukannan dake cin jiki a hankali"
"Gaskia bata dashi, idanma tana dashi zata faɗamunne, don ko tuntuɓe tayi saita nunamun, haka ta taso tun yarintarta"
"akwai wasu wanda take faɗa dasu ko kuma wanda kike zargi akan mutuwar y'arki bayan Abdul?"
"yarinya ce nutsattsiya, mararson hayaniya, bata da wani abokin faɗa, wama zai kasheta bayanshi? Shine nan ya kashemun 'yata, azzalumi kawai, insha Allahu sai yaga k'arshenshi" ta k'arasa maganarta tana kuka.
Ya koma ga Alk'ali, "wannan shari'ar mai sauk'i ce yamai shari'ah, duka shaidu sun gama tabbatarwa babu wani wanda ya kashe baiwar Allahn nan Hajna, sai mijinta Abdul, da wannan nake rok'on kotu mai adalci data yankewa Abdul hukunci mai tsanani yanda sauran mutanen dake burin kashe matayensu su ɗauka darasi daga gareshi, ta kuma k'watarwa mahaifan Hajna HAKK'IN KISAN 'Yarsu, ngde yamai shari'ah"
Ya koma ya zauna, alk'ali na en rubuce-rubuce sannan ya ɗago da kanshi.
"zamu ɗaga sauraren wannan shari'ah zuwa 15 ga wannan watan da muke ciki, don haka kowanne ɓangare suyi k'ok'arin kammala tattara shaidunsu, za'a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma har zuwa lokacin"
"kotuuuuu!!!"
Waiwaye Adon tafiya.....
©Rabiatu sk mashi
0 comments:
Post a Comment