☠HAK'K'IN KISA☠
👽👽👽👽
6-10
©Rabiatu sk msh
®NWA
www.babymsh.blogspot.com
Zuwansu police station Abbanshi ya gama harzuk'a, ganin yanda yaketa hayaniyar faɗa anma Abdul ko magana ma bai musu, shiru kawai yayi yana kallon k'asa, donshi ganinshi yake ma kamar a mafarki, jiran lokacin farkawarshi kawai yake.
Jijjigashi da mahaifiyarta keyi tana kuka ne ya dawo da hankalinshi kanta yana kallonta, faɗa take da dukkan muryarta.
"wallahi ka saurareni dakyau kaji, bazan taɓa yafe HAKK'IN KISAn y'ata ba, kai gara ma ka buɗe baki kayi magana, don wallahi koda dukkan dukiyatah zata k'are saina wulak'antaka Abdul, tana da gata, bazatayi mutuwan rashin galihu ba"
Ta jefar dashi wuri ɗaya kaman tsumma, abunnan da yake ba k'aramin k'arama Abbanshi haushi yake ba, bama kaman da dukkan tambayoyin da akai mishi yak'i ya buɗa baki ya bada amsa.
Abba ya dafe kanshi, "ka cuceni Abdul, anma kanka ka cuta, ka jefar da duk wani tarbiyyar dana maka, a ganina samun duniya bai isa ya sakaka ka kashe Hajna ba, yarinyar data nuna maka soyayyar da bazaka taɓa samun matar da zata maka shi ba, meyasa Abdul? Wacce irin dukiyah ce ban sakar maka ba? Wanne gata ne ban nuna maka ba? Meyasa zaka kashetah? Wannan abun kunyar har ina? Wallahi yau nayi dana sanin kasancewarka ɗana"
A raunane yake kallon mahaifinshi yana hawaye, "Abba ta yaya? Akan wanne dalili zan kashe Hajna? Wallahi bansan komai akan mutuwarta ba, na faɗa muku muna cikin auratayya ne kawai sai dai naga ta daina motsi, kuma na rantse da Allah ba fyaɗe na mata ba"
"K'arya kake, k'arya kake wallahi kashemun y'a kayi,"
"Miye ribana idanna kashe Hajna? A tunani na koda idanuwanku Abun Allah ya kiyaye, Abun Allah ya kiyaye" saida ya gama jinjina maganar sannan yaci gaba.
"ace koda da idanuwanku kuka ganni da wuk'a ina sokawa Hajna zakuce ne idanunku ne suka muku k'arya, ta yaya zan iya kashe macen dana fiso fiye da rayuwatah? Wallahi ku yarda dani ni ban kashe Hajna ba"
"Saboda kana tunanin mun maka wannan yardar ne shiyasa ka kasheta? Idan bakai ka kashe Hajna ba waye ya kasheta? Ka faɗa mana maganar da hankali zai ɗauka mana"
Shiru yayi yana hawaye, shi kaɗai kaman zautacce yake furta "Hajna ya zaki tafi ki barni? Ya zaki bar masoyinki cikin masifa da kuma rashinki? Ta yaya zan iya rayuwar da babu ke a cikinta? Kin mutu kin huta, Ya Allah ya ɗauka rayuwatah nima in tafi in iske Hajna tah, Hajna nine Abdul ɗinki, da kikasha yimun alqawarin zamu kasance tare duk wuya duk daɗi, don Allah ki kasance dani har yanzunma"
Mamanta ta kwaɗa mishi wani irin marin da bai taɓajin irinsa ba, "Mak'aryacin banza kawai, soyayyar banza ce wannan kake nuna mata bayan ka kasheta"
Kafin ya dawo dai-dai Abbanshi ya fara haɗashi da bango, k'anwarshi khadija ce ta ruga wurin Ummansu da tunda sukaje ko k'ala batace ba.
"Umma don Allah ki hana Abba, yanzu ko tausayin Yayanmu bakiji? Wlhy nina yarda dashi gaskia yake faɗa" girgiza kai kawai Umma tayi ta k'ara gyara tagumin da tayi da hannuwa biyu.
Dak'yar suka k'waceshi a hannun Abba, aka kaishi aka gark'ame daga k'arshe ma hana kowa ganinshi akai. Kafin azahar k'ofan station ɗin ya gama cika da en uwanshi dana Hajna, da sauran en gulma, garuruwa kam babu inda labari baije ba, kowa da abunda yake faɗi, "guba ya saka mata a abinci, asiri ya mata, jininta ya bayar ga dodon tsafinshi" harma da masu cewa "wani abu ya yanka a k'asanta, ai jininta ya shanye" maganganu dai sunyi yawa, ko wanne gidajen radion Kano ka gano labarin dai ake watsawa.
"Ango ya kashe amaryarshi a daren amarcinsu, anma yana ik'irarin shima gawarta kawai ya gani, koya gaskiyar lamarin yake? Sai dai munji ta bakin Angon"
Ɗan k'aramin yak'i k'annen Hajna su 3 maza suka so tarawa a k'ofar station ɗin, faɗi suke sai an fiddo musu da Abdul sun k'watar mata hakk'in kisanta, khadija kuka kawai take tana rok'on Ummansu tasa a fito da Yayansu, saboda duk hayaniyar da ake bai hanata jiyo ihunshi ba.
"Umma karki bari a hukuntashi akan laifin da bai aikata ba, wallahi Yayanmu bazai taɓa iya kashe Aunty Hajna ba"
Umma ta dafa kafaɗarta "wacce Hujja gareki akan hakan? Ke yarinyahce khadija har yanzu bakisan komi ba"
Baki buɗe take kallon Umma, "Umma kina nufin kema kin yrda akan yayanmu ya kasheta?"
"bazance miki eeh ba, anma yaran yanzu ne ba'a shaidansu"
Rasa me zata k'ara cewa tayi, ta sulale kawai ta zauna wurin tana kukan tausayawa yayanta.
©Rabiatu Sk Mashi
0 comments:
Post a Comment