New Post

Tuesday, 15 August 2017

HAKKIN KISA 51-55

☠HAK'K'IN KISA☠
      👽👽👽👽
            51-55
©Rabiatu sk msh
      ®NWA

www.babymsh.blogspot.com

Da fitowansu, Maman Hajna bata jira kowa ba ta shige motanta, ita take driving daman su Muhseen mota daban sukazo, Maryam ma ba'azo da ita ba. Gudu kawai ta ringa shararawa saman titi, tana maida numfashi cikin sauri.
   Wayanta ce tayi ringing, sai data ɗan rage gudu sannan ta ɗaga.
        "yauwah dai"
    Daga can ɗayan ɓangaren akace "Hajiyah nifa bayanin likita yayi matuk'ar tsoratar damu, anya kuwa ba dalilin wannan abun bane?"
     "wanne abu? Watau har kuna da bakin da zakumin wannan maganar kenan"
      "A'ah hajia, kawai dai yaronne yake bamu tausayi"
      "k'aniyar tausayin naku, idan ku kun gaji da rayuwa ni da saurana, don haka ku kama bakinku kuyi shiru"
     "tohm shknan hajia" ta kashe wayan.
     Wata razananniyar murya taji ta k'yalk'yale da wata irin daria data bala'in rikitata, taja wani wawan burki ta tsaya, ba'a daina dariyar ba aka ci gaba dayi kaman za'a fasa dodon kunnanta, duk ta tsorata ji take kama ana juyawa da ita, tsawon lokaci ana wannan dariya sai kuma ta ɗauke gaba ɗaya. Cikin wata kakkaurar murya aka fara magana
      "koba HAKK'IN KISA kikeso a ɗauka ba? Ninan zan ɗauka HAKK'IN KISAn da kaina, akan wanda suka aikata kisan na gaske" aka k'ara ɓarkewa da wata dariyar.
     Duk ta ruɗe ta haɗa zufa gashi motan ta rufe ruf ba hanyar fita, ga mutane suna wucewa sai ihu take anma babu mai jiyota kowa harkarshi yake, sai da dariyar ta tsayane, kuma kaman anyi ruwa an ɗauke.
    A rikice ta k'ara kwasar motar da gudu sai gida.

    Kasa zaune tayi ta kasa tsaye bayan komawarta gida, Abunda ya faru da ita ɗazunnan gaske ne ko mafarki take? Wannan yafi k'arfin mafarki, k'ila dai razanar da tayi ne ya jawo mata hakan.
   Su Muhseen ta saka Maryam ta kira mata, ta zaunar dasu su duka ukun.
    "me kuka fahimta akan bayanan da likita yayi na dalilin rasuwar Hajna?"
   Alhassan yace "bayanan likita na k'arya, Sun dai haɗa abunsu ne kawai don su saka a saki Abdul,"
    "k'warai ma kuwa, kuma mu bazamu taɓa bari ya kashe mana er uwa ba'a hukuntashi ba," inji Muhseen.
     "kai dai barsu mana, muda muke tare da Hajna tun tashinmu bamusan da wani rashin lafiya nata ba, sai shi da aka kai ma ita kwana ɗaya zai k'irk'iro mata da ita"
  
   Alhusein yace "Maryam ba tace tana yawan rashin lafiya ba? Zai iya yiwuwa mune bamu sani ba, nifa na fara tunanin anya kuwa shi ya kashe Hajna?"
      "Rufemun Bakin sakaran namiji kawai!! Yau da ba tare na haifeku da Alhassan ba sai in fara k'ok'ontan kokai ba ɗana bane, magana fa ake akan kisan er uwarka, jininka! Anma harka fara tausaya mishi??"
      "to ae gaskia ne Mama"
   "gaskiyar uwaka, tashi ka bani wuri" ya mik'e.
    "kuma ku tafi"
  Suka tashi zasu tafi, giftawar mutum taji ta bayanta, har wani hucin zafi ta bugeta, da sauri ta waiwaya anma ba kowa.
       "kai kuzonan, ina zakuje?"
     "kefa kikace mu tafi Mama, zamuje masallaci ma an kira Magrib"
    "ku kiramun Maryam"
         "tohh" sannan suka tafi.

    Da dare ta kwanta barci, yana ɗan ɗaukarta ta fara jiyo gadon yana juyawa da ita, ga wata k'ara data cika mata kunnuwa wacce ma tafi ta ɗazu, data tafi zata sauka, za'a haɗa kanta da gado saita bugu sosae, ta koma tsakiyar gado ta k'udundune wuri ɗaya.
     Wata tsawa aka daka mata batasan sanda ta saki fitsari ba,
     "kin ɗauka zakiyi barci ne bayan shi kuma yana can ya kasa?? Hahahahah aikun daina barci kenan tunda kuka hanashi"
    Kafinta ankara anyi sama da ita, saida ta bugu da silin sannan akan maidota saman gadon tim, batasan sanda ta buɗe ido ba, wasu fararen halittune tayi ido huɗu dasu, kowannensu jina jina yana yak'e hak'ora.
    Wani irin ihu tayi sannan ta k'udundune da bargo.  Tsit taji kuma komai ya lafa, sai kyarma take tana kuka, gashi duk ihun da take babu mai jiyota.
    Jin ta tayi kaman abun ya lafa ne ya sakata ɗagowa da fuskanta a hankali, saida ta gama lek'owa sannan ta buɗa idanunta, wasu irin k'wari taga sun nufota a guje kowanne jikinshi na cin wuta.

Tohhhfa, Bara dai mu lek'a gidansu Abdul canma mu gano meke faruwa....

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • HAKKIN KISA 41-50☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽               41-50 ©Rabiatu sk msh     … Read More
  • HAKKIN KISA 31-40☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽             31-40 ©Rabiatu sk msh       … Read More
  • HAKKIN KISA 21-25☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽            21-25 ©Rabiatu sk msh       ®NWA … Read More
  • HAKKIN KISA 26-30☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽              26-30 ©Rabiatu sk msh      … Read More
  • HAKKIN KISA 26-30☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽              26-30 ©Rabiatu sk msh      … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts