☠HAK'K'IN KISA☠
👽👽👽👽
41-50
©Rabiatu sk msh
®NWA
www.babymsh.blogspot.com
KOTU...
Yau kam kotun har tafi ta rannan cika, babban kotun ta cika mak'il har babu wurin zama, mutane daga wasu garuruwan sunzo sauraren k'aransu Abdul.
Shari'arsu itace ta biyu bayan Alk'ali ya gama sauraren wata, sannan aka gabatar da k'ararsu Abdul.
"lauyoyinsu suna kusa?"
Br Alqaseem ya mik'e "Sunana Br Alqaseem Muhammad, lauyan wanda yake k'ara"
Lauyan Abdul ma ya mik'e "Sunana Br Ahmad Saeed, lauyan dake kare wanda ake tuhuma" shima ya zauna.
"lauyan wanda ake tuhuma, ko kana da tambayoyin da zaka ma wanda kake karewa?"
"ina dasu ya mai shari'ah" ya tashi ya k'arasa inda Abdul yake.
"Malam Abdul, ko zaka sake faɗama kotu abun daya faru a daren 4 ga watan 6" ya gyaɗa kai, sannan ya k'ara tariyo duk abunda ya faru a daren amarcinshi.
Sannan br Ahmad yaci gaba da magana, "Ya mai shari'ah, idan munyi la'akari da bayanan da Abdul ya bamu na sanadiyyar mutuwar matarshi, baida wani alak'a da kisan nata, domin kuwa ya taka sawun ɓarawo ne, domin kuwa babu wani ango dazai kashe matarshi a daren aurensu na farko,"
"idan kotu ta bani dama, zan gabatar da hujjata ta farko da zata k'ara tabbatar ma da kotu cewa Abdul bashi da Hannu akan kisan matarshi Hajna"
"kotu ta baka dama"
"Meerah Sayyid, wacce ta kasance Aminiya a wurin marigayiyah"
"idan Meerah Sayyid tana kusa kotu tana son ganinta" ta taso ta tafo, da alama itama tana cikin damuwa, don babu wani kuzarin kirki a tare da ita.
"Malama Meerah, a matsayinki na k'awa, ko kuma Aminiya a wurin Hajna, me kika sani a alak'ar Hajna da Abdul"
"Duk da Hajna na matuk'ar son Abdul, bazai kai koda kwatan son da Abdul yake mata ba, ban tunanin koda na second Abdul zaiyi tunanin cutar da Hajna, Aminiyatah ce Hajna, duk duniya babu wanda yasan sirrinta kamar ni, kuma haka nafi kowa sanin soyayyar dake tsakaninta da Abdul, tabbas Abinda ya faru dasu wata jarabta ce ta Ubangiji, anma Abdul mutumin kirki ne, bazai taɓa iya aikata abunda ake tuhumarshi dashi ba"
Sun taɓa samun saɓani a tsakaninsu?
"a tsakanin Harshe da hak'ori ma ana saɓawa, duk inda aka zauna dole ne za'a saɓa, a iyakar sanina dasu sau ɗayane suka taɓa samun saɓani, a dalilin tayi rashin lafiya bata sanar mishi ba, shima anan take ta bashi hak'uri suka shirya"
Ya juya wurin Alk'ali, "iyakar tambayoyin da nake dasu kenan ya mai shari'ah"
"lauyan mai k'ara, ko kana da tambayoyin da zaka ma Meerah?"
"ina dasu yamai shari'ah"
Ya k'arasa inda meerah take "Malama Meerah, zanso jin tsawon wanne lokaci ne kikasan Hajna?"
"k'awatah ce tun daga nursery school"
"kina nufin nursery school kawai kukai tare ko kuwa dukkan makarantu tare kukayi?"
"tare muke har high institution"
"unguwarku ɗaya?"
"a'ah Anma ko yaushe muna tare"
"kenan ko zatayi fira da Abdul ma kuna tare?"
"A'ah anma dai bata ɓoyemun abunda take neman shawara daga gareni, da ace Abdul yana da wani halin da take zarginshi dashi, nice mutum ta farko da zata faɗa mawa"
"ta yarda da Abdul matuk'a ba?"
"k'warai ma kuwa"
"baki tunanin shi Abdul ɗin yana da wani ɓoyayyen hali da ita kanta Hajnar bata san dashi ba?"
"gaskia ban tunanin hakan...."
"biron dake hannunshi ya jefeta dashi,"da sauri ta duk'e tayi matuk'ar tsorata.
Yayi murmushi, "a tsayuwar da nayi nan kinyi tunanin zan iya jifanki?"
Ta girgiza kai, "toh me yasa na jefeki? Kenan kowanne mutum zai iya canjawa ko yaushe?"
Ta ɗaga kanta, kuma ta girgiza, duk taa rikice.
"magana zakiyi ba kaɗa kai ba"
Br Ahmad ya mik'e, "objection Ya mai shari'ah, barrister baida hurumin dazaina rikitata"
"Barrister Alqaseem ka kiyaye"
"Nagode ya mai shari'ah, iyakar tambayoyina kenan" ya yafi ya zauna
Barrister Ahmad Saeed ya tashi tsaye "idan kotu ta bani dama zan gabatar da shaidata ta ta biyu, kuma shaidar da zata tabbatarma da kotu babu hannun Abdul a kisan matarshi Hajna"
"Kotu ta baka dama,"
"Dr Hameed, likitan da yayi bincike akan dalilin mutuwan Hajna"
"Idan Dr. Hameed yana kusa kotu tana son ganinshi"
Bayan ya fito, yayi rantsuwa akan zai fad'a gaskiya, sannan ya ciro takadda, "wannan itace takardar binciken da mukayi akan dalilin rasuwar Hajna," sannan ya bada aka mik'a ma Alk'ali yaci gaba da kora bayani,
"a binciken da mukayi, kamar yarda yan fannin lafiya da kimiyya suka sani koda (kidney) itace take tace duk wani abu daya shiga cikin mutum, ta tura na jini wurinshi, na ruwa haka, fitsari, zufa da sauransu. Idan ta gaji da aikinta tana bari suna dank'arewa a wajen saboda sunyi yawa fiye da yanda zata iya d'auka. Wannan taruwan da zaiyi ya dank'are a wuri d'aya saiya zame ma mutum kamar wani dutse ko nau'i na ciwo daganan sai a fara samun matsalar fitsari, and other kidney diseases irinsu kidney stones, phylo nephritis da sauransu, kuma tana iya k'ara tarama mutum by product ɗinta a jiki, kamarsu uric acid wanda yake kaman dusar k'ank'ara, idan ya taru ya daskare sai ya gangaro kan kafafu musanman guiwa yana haifar da gout."
Ya nisa sannan yaci gaba "Abinda k'odar Hajna ta nuna mana yayi matuk'ar firgitamu, haka kuma munyi mamakin yadda take rayuwa a haka duk da baa mamaki da ikon Allah,duk da k'anwarta tace tana yawan ciwo amma tana da dauriya da k'arfin hali, shiyasa ma bata bari mamanta ta sani, duk da k'odar tata ta hagu tafi illata da hakan shiyasa ta daman ke taimaka mata wajen rayuwa, a iya bincikenmu abunda muka gano kenan, k'odarta a cunkushe take da wasu irin tarkace tana fama da cuta shekara da shekaru"
Sakamakon binciken da muka samu a hanta (liver) ta Hajna yayi matuk'ar tsorata mu, domin har wani ɓangare na hantar tata ya fara zama kore-kore, lokacin da mukayi LFT (liver function test) mun gano wasu parameters din basu aiki yarda ya kamata anma a haka take rayuwa cikin ikon Allah"
"iya binciken da mukayi kenan, amma duk da haka bazamu iya cewa dalilin daya kasheta kenan ba, duk da shima zai iya kasheta har lahira, abun da mukafi tunani shine, akwai wani ɓangare daga k'asan Hajna, wanda yayi weak, dalilin ɓallewae jinin da tayi kenan lokacin da mijinta ya kwanta da ita,"
Tunda likita ya fara bayani, tuni jikin Maman Hajna ya jik'e sharaf da zufa, sai k'ifta idanu take, ta ɗan fiddo da kunnanta yanda zataji dakyau, jikinta har kyarma yake, Addu'a kawai take Allah yasa binciken ya tsaya iyakarnan.
Maman Abdul kam kasa zama tayi kaman mai cutar basur, da wasu maza biyu daga bayanta da suke ta matse'matsen fitsari, nikam abun saiya ɗauremun kai, Maman Hajna da Umman Abdul kuma miye nasu a ciki??
Br Ahmad yace "da waɗannan shaidu nawa nake rok'on wannan kotu mai adalci data wanke Abdul daga zargin da ake masa na kisan matarshi, domin kuwa babu hannunshi a cikin mutuwarta, daman can Hajna tana fama da rashin lafiya, Abdul sawun ɓarawo ne kawai ya taka"
"Ina da ja Ya mai shari'a" inji br Alqaseem
"idan Abdul sawun ɓarawo ya taka, kenan waye ya kashe Hajna? Bance ban yarda da bayanin likita ba anma ai Hajna a hannun Abdul ta rasu, don Haka babu wani mai HAKKIN KISAN Hajna sai Abdul"
Alk'alin kanshi shari'arnan tana chaja mishi k'walwa, tana daga cikin shari'o'in da yake masu rikitarwa, ya gama ributunshi sannan yace "zamu ɗaga wannan shari'a zuwa sati mai zuwa, a ranar ne kotu zata yanke hukunci, kowanne ɓangarori suyi k'ok'arin tattara hujjojinsu zuwa wannan lokaci"
Kooootuuuu...!!!
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment