New Post

Tuesday, 15 August 2017

HAKKIN KISA 31-40

☠HAK'K'IN KISA☠
      👽👽👽👽
            31-40
©Rabiatu sk msh
      ®NWA

www.babymsh.blogspot.com

     Sanda Meerah ta k'ara dawowa tare da lawyer, Abdul ya k'ara ramewa duk yayi bak'i, kamanninshi sun canja kaman ba wannan hadaɗɗen Abdul ɗin data sani ba. Lawyern kanshi ya tausayawa Abdul da yanda ya ganshi.
      Ya kalla Abdul cikin k'arfafa gwiwa "ka kwantar da hankalinka Abdul, insha Allah komai zaizo mana cikin sauk'i"
       Meerah tace "k'warai kuwa, domin Allah yana tare da mai gaskia, gani tare da lawyer, ka daure ka bashi haɗin kai duk tambayoyin daya maka"
    "nifa na riga dana faɗi duk abunda na sani"
    Murmushi lawyern yayi, "tohm aeni banji ba, ka daure ka sake bani labari"
      "idan na baka Hajna zata dawo gareni? Na faɗa ma Meerah bana buk'atan lawyer, abu ɗaya nafi buk'ata yanzu shine na tarar da Hajna inda take"
     "kenan baka da buk'atar sanin ko waye ya kashe Hajna? Kafison ka mutu kowa yana maka kallon wanda ya kashe matanshi a daren farko? Haba Abdul, Hajna bata cancanci hakan daga gareka ba, kai kafi cancanta daka jajirce wurin gano wanda yake da hakk'i a kisanta"
    
   Maganganun Meerah sunyi matuk'ar tasiri a zuciyarshi, su suka k'ara k'arfafa mishi gwiwa,  "A daren Aurenmu ne kaman kowanne Amarya da ango, nayi k'ok'arin raya sunna tare da Hajna, kuma wallahi ba fyaɗe na mata ba da amincewarta, sai dai na ɗago naga bata motsi jini ko ina a jikinta, na ɗauka ma suma tayi, sai da likita yazone ya tabbatar mana da Hajna ta tafi, Har yanzu ina jiyo kukan Hajna a kunnuwana, ina jin kukanta anma na kasa sauka a jikinta, shikenan Hajna...."
   Ya kasa k'arasawa saboda kuka, sai lawyern ne ke dafa kafaɗanshi yana bashi baki, shi kanshi idanuwanshi sun cika da hawaye,
   "Wannan wani rikitaccen Al'amari ne, yanzu abunda mukafi buk'ata shine takardar likita akan binciken dalilin mutuwanta"
    Meerah ta nisa sannan tace "nifa nafi kallon wannan abun a matsayin asiri, idan ba asiri ba haka kawai daga Auratayya sai mutuwa?"
      "hakane kam, yanzu kai Abdul babu wanda kake tunani dazai iya mata hakan? Don zai iya yiwuwa abinda Meerah ta faɗa gaskia ne"
    "Laifin me Hajna tayi ma wani dazaiyi mata hakan? Bata da abokin faɗa, ko kaine ka mata laifi itace mai baka hak'uri, tun zamana da Hajna ban taɓa ganin tayi ko musayar yawu da wani ba, don haka babu wani da nake zargi akan mutuwanta.

      "Akwai, tabbas ni akwai wacce nake zargi" duk suka maida kallonsu a kanta.
    "budurwanka Haneefah"
        "wacece Haneefa?"
Abdul yace "wata yarinyah ce dana taɓa taimakawa, a  hanya na ganta tana tafiya tana haɗa hanya, duk taa fita hayyacinta, na ɗauketa na kaita asibiti, sai daga baya take faɗamun en fashine suka tsaresu ita da direbanta suka anshe komai nasu, shine duk suka tsorata kowa yayi hanyarshi, na kaita gida kwana biyu ta huta sannan Ummana ta saka aka maida ita gida, tunda tamun zancen soyayya na bata hak'uri, shikenan rabona da ita, babu abunda ya haɗata da mutuwan Hajna"

     "Akwai kuwa, Hajna bata taɓa faɗa maka bane saboda batasan damuwanka, anma akwai ranar da Haneefa ta taɓa iskemu gidansu Hajna lokacin ta fito rakoni, da waya hannunta tana chat dakai, wani wawan burki taja sannan ta fito daga motan tana mana kallon sama da k'asa, sannan ta kalla Hajna.
     "nan ne gidansu wannan wawuyar Hajnar?"
    Bata nuna taji haushi ba, saima tace mata, "da wawayun Hajnar kike magana"
   Tunnan tasha jinin jikinta, ko bata faɗa ba nasan ganin ajinta dana Hajna ba ɗaya bane shiyasa tasha jinin jikinta.
    Ta nunata da yatsa, "zuwane na miki gargaɗi akan kula Abdul da kikeyi, idanma asiri kika mishi kiyi saurin karyawa, don nawane ni kaɗai"
     "tohh fa, baiwar Allah ai..." da sauri ta saka hannu ta dakatar da Hajna.
    "kinga nayi kama da wacce zata saurare maganarki? Zuwa nayi in faɗa bawai a faɗamun ba, idan kinji kanki kika taimaka," itadai Hajna murmushinta kawai take, tana ganin yanda na taso da faɗa ta rik'e. Harta juya sai kuma ta dawo.

     "nasan fa Abdul kuɗinshi akeso, idan nace zan rabaki dashi harta da gidan da kuke ciki zai anshe kayansa ne, ki faɗamun ko nawa zaki iya siyarmun da soyayyanshi, kar kiji komai ki faɗa koma nawa ne"
    "uban waye yace miki shiya siya gidannan? Ko an faɗa miki kowa matsiyaci ne kaman ke?" Hajna ta rik'oni,
      "ke ba dake nake ba, idan kika k'ara sakamun baki a cikin maganata sai kinyi nadamar sanin Hajnar ma da kikai"
   Cikin murmushi tace, "nawa zaki iya siyen Soyayyan Abdul ɗin? Million 2?"
       Haneefa harda saurin ɗaga kai, "idan su suka miki" Hajna ta girgiza "million biyar?"
      "million 10??"
   "ke talauci hauka ne?"
         "million 20??"
    "lallai kinma koma sata"
   "ae har yanzu ban faɗi farashin soyayyar Abdul ba, kinsan me yasa?" cizgar kai tayi cikin jin haushi.
     "saboda babu shi, idan har kina tunanin akwai kuɗin da zasu iya siyar miki soyayya, tohm kinyi babban kuskure"
    "kece kikayi kuskure Hajna, da kike tunanin zaki iya ja dani, mu zuba ni dake, indai Abdul ne gaki gashinan, zaki gane wacece Haneefa"
   Tana gama faɗar hakan ta juya ta barmu, a lokacin na tsorata k'warai da zantukan Haneefa, naso Hajna ta barni na faɗa a musu tsakani, anma ta hana, tace babu wanda ya isa ya mata Abunda Allah bai nufa ba, da haka tasa muka bar maganar.

      "Maganarki gaskiya ne, zamu buk'aci Haneefa a wannan binciken namu"
   Abdul ya nisa sannan yace "babu hannun Haneefa a kisan Hajna"
      "meyasa zakace haka?"
   "saboda Haneefa ta rigani aure, tun kafin aurenah da Hajna akayi aurenta, tunda ta samu wani ta hak'ura tunda daman tasan ba sonta nake ba"
    "toh fa, wannan case ɗin naka yana da matuk'ar ɗaure kai, tunda nake ban taɓa haɗuwa da case mai rikitarwa irin wannan ba"
        "abun da bai taɓa faruwa bane ko a tatsuniya, me yasa saini kaɗai zai faru dani? Duk cikin mutanen dake duniyar nan, Meyasa saini kaɗai?"
     "A'ah Abdul, Allah na sonka shiyasa yake maka wannan jarabawar domin ya auna imaninka, kayi k'ok'arin cin wannan jarabawar, komai ya faru dakai karka ɗauka don kai kaɗaine Allah bai so, ka gode mishi zaka ga Alkhairin abun"
      "Allah yajiqan Hajna"
    "Ameen ya rabbi"

  Duk wani bayani da gakeson ɗauka ya gama, yayi rubutunshi, duk da shi kanshi case dinnan ya gama ɗaure mishi, baisan ma ta inda zai fara bincike ba, gashi lokaci ya k'ure an kusa yin zama na biyu.
      Tun bayan fitarsu ya jingina kanshi yana hawaye, ya rasa tunanin me zaiyi, shi duk wannan abun ana k'ara fama mishi ciwon mutuwan Hajna ne.
     "me yasa kika shigo rayuwatah Hajna? Meyasa kika shigo rayuwata kinsan zaki tafi ki barni?"
     "kin mutu kin huta da rikicin dake duniyarnan tamu, ya Allah kaji k'an wannan baiwa taka"

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts