New Post

ABUBUWA BAKWAI (7) ABIN KULA GA DAN'ADAM

1. Duniyar da za a barta, me ya kawo hadama? 2. Dukiyar da za a lissafa daya bayan daya, me ya kawo tarata? 3. Rayuwar da zata kare, ina wani farin ciki? 4. Yarintar da tsufa zai zo mzta, me ya kawo takama? 5. Ana sauraren mutuwa, ina wata walwala? 6. Jikin da zai zama gawa, me ya jawo dagawa? 7. Karshe dai makomarsa kabari, me zai sa alfahari? Wanda ya manta da wadannan a ina ya bar hankalinsa? Allah yasa mu dace, yayi mana kyakkaywan karshe. Ameen!

KADA KA RAMA CUTA GA WANDA YA CUCEKA!

Kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka, kai kayi hakuri. Zaka samu abu biyu sakamakon hakan; * Na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. * Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

KADA KA BARI ZUCIYARKA TA ZALUNCEKA!

Kada ka sale zuciyarka ta zalunceka, tabbas zaluncin zuciya ga gangar jiki yake komawa, idan akayi wasa ya zamanto ya shafi rayuwa. Assasa bak'in tunani, yawan zargi da rashin tabbas akan wani aiki, zato, shakku ko kokwanto akan wani al'amari batare da tantance gaskiyarsa ba, shine zaluncinzuciya akan dan Adam. Maza ka hana zuciyarka don akwai hadurra dubu akan hakan.

MAHAKURCI MAWADACI

Tabbas ba kowane dandanon magani ne ke da dadi ba, amma babu shakka shine abu mafi dacewa ga dukkan mara lafiya. A lokuta da dama rayuwa takan dakeka da guduma ta jefaka acikin wani mawuyacin hali, kayi ta fama amma tayi maka tutsu. Amma idan kayi hakuri sannu ahankali zata kwaranye. Hakika ba duk abinda rai yake so yakan samu ba, amma bukata bata taba sauyawa ba kuma bata taba karewa ba. Don haka ka shirya bukatunka da kyau ka bisu daya bayan daya sannu a hankali, kayi gwa- gwarmaya, sannan kayi juriya. Tabbas mafarkinka zai zama gaskiya.

KO KA SAN?

Rayuwa bakin alqalami ce tana bukatar kaifi sannan tana son tsini. Kaifin don ka yanki magauta, tsinin kuwa don ka soki makiya. Haka zalika rayuwa kamar randar ruwan sanyi ce ta kasa tana bukatar tanaji da adani, kodn wata rana ka shayar da masoyanka. Da kyau ka lura da abu biyu a rayuwa; 1. Ka lura da mai zaginka mai aibantaka wata kila wata rana zai iya zama masoyinka mai yabonka 2. Ka lura da masoyinka na kusa mai yawan ambaton alkhairinka, wata kila wata rana zai iya zama makiyinka mai zaginka.

Thursday, 29 December 2016

HARAMTACCEN ZAMA 43-44

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  43-44

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

    Aunty na zaune bayan an shiga da Majeeda, Majeed kam sai zagaye wurin yake yaje ya dawo, har Aunty zainabu ta gaji tace mishi,
    "wai bazaka zauna ba Majeed?"
     "Aunty yazan zauna bayan ita tana can tana shan wahala"
    "tohh ci gaba da zagayen ku raba wahalan"

  Nurse ce ta fito,
     "likita yace zaku iya shiga" tun kafin Aunty zainabu ta mik'e ya rigata shiga ɗakin, Abokinsa Mukhtar ne ya hango, ana ce mishi Dr. Shaheed, ya taho da fara'arshi yana bashi hannu,
    "ka ce mana Amaryar da aka hanamu rakiyar ango don karmu ganota ne aka kawomin har inda nake"
   Majeed yayi daria sosae  "kasan dai yanda abun yake, anma ay har gida naso muzo da ita"
   "har yanzu na biyo bashi kenan?"
   "yanzu dai Aboki ya jikin nata?"
  Dr. Shaheed, Ya washe baki tare da k'ara mik'a mishi hannu,
    "ina tayaka murna"
  "banson iskanci fa, matata na kwance asibiti kace kana tayani murna, meke damunta plz?"
    "Koma menene ai aikinka ne mutuminah"
   "ni kuma? Kaifa ɗan iskane rashin lafiyar matar tawa ma saika jamun rai?" Dr. Shaheed sai dariya yake mishi ganin ya damu sosai yace,
    "Amaryarmu tana ɗauke da juna biyune, na tsawon sati shida"

Ya fiddo duka idanunshi cikin tashin hankali ne koko mamaki? K'ila kuma duk tsantsar farin ciki ne,
    "ciki shaheed?"
"k'warai kuwa Aboki, idanta farka zaku iya tafiya, anma bayan ka bani goron Albishir ɗina" ya faɗa cikin zolaya,
  Aunty Zainabu dake tsaye a k'ofan tace, "Ai wannan babbar Albishir ne Dr, ni da kaina zan kawo maka"
    "Tohh Aunty godia nake,"
Duk majeed yayi sukuku har Dr. Shaheed ya fita, Aunty ta wuceshi taje inda Majeeda take kwance, idanuwanta a buɗe ta farka, anma hawayene kawai ke zuba a idanunta,
   "Miye haka Majeeda? Keda zanga murna da farin ciki a fuskarki, miye na kuka kuma?

   Shiru tayi ta kasa koda k'ifta idanunta ne, sai dai hawayenda takeyi kawai, Aunty Zainabu tayi maganar harta gaji,
      "Aunty Zainabu ina ganin fa murna ce taima Majeeda yawa, wannan kyautah ce Allah ya bamu da ba kowa yake bama ba"
    "hakane, ayni namayi tunanin ko ciwonne"
    "A'ah da akwai matsala daya faɗamun"
    "hakane fa" ta zunguri Majeeda,
  "Tashi mu tafi tohh, tun yau kin fara tunanin ciwon nak'uda" saida Majeed yayi dariyar dole,

    A hanya ta dinga kiransu momie tana musu Albishir, Abdul-Majeed yana driving ya juyo,
   "wai ya kike faɗa musu tun yanzu Aunty?"
   "tohh sai yaushe zan faɗa musu? Kaga kuwa yanda suke murna" shiru bai ce mata komi ba, har gidanta suka ajjeta, tana k'ara nanata musu shawarar likita yanda za'ana kula da Majeeda,
    Saida ta fita sannan Majeeda ta samu damar fashewa da kuka, baiyi k'ok'arin lallashinta ba har suka isa gidansu, tun kafin ya gama parking ta fito daga motan har tana shirin faɗuwa, ta ruga ta shige ɗakinta, sulalewa k'asa tayi ta ɗaura kanta saman gefen gadon tana kuka,

   Ya daɗe a tsaye jikinshi a sanyaye, sannan ya matsa inda take, ya mik'a hannu zai jawota ta buge hannu, ya k'ara mik'a hannu ta tureshi tana ci gaba da kukanta, cikin sanyin jiki ya zauna gefen gadon, sai kuma ta maida kanta samanshi sannan taci gaba da kukan,
   Hannunshi yasa yaci gaba da shafar gashin kanta,
   "Ya isa hakanan tohh, meye na kuka" ta k'ara k'arfin kukan nata,
   "Miye na kuka? Idan banyi kuka ba dariya zanyi saboda ina murna da wannan abun dake jikina?"
    "kenan baki murna saboda ɗana yana a jikinki?" tayi tsit tana share hawaye,
   "Anma bata wannan hanyar ba Yaya majeed"
   "saita wacce hanya? Kenan kuwa har abada bazamu ga ɗanmu ba, kina nufin har yanzu baki kallona a matsayin mijinki?" ta shiga girgiza kai,
   "abunda ya kamata muyi murna da farin ciki ne, ki daina kallon cikin dake jikinki a matsayin wanda muka samu a HARAMTACCEN ZAMA, ki kalleshi a yanda kowa ke kallonshi, kema kina sonshi ko?"  ta daga mishi kai,
   "nima inason duk wani abu dazai fito a jikinki, ina sonki sosae Majeeda"
    Ta tashi taɗan rage tsawonta, ta kwantar da kanta jikinshi tana wasu hawayen, ya ɗago da fuskarta
   "bazan taɓa bari kiyi kuka ba Majeeda indai ina tare dake" ta juya bayan hannunta tana murmushi zata share hawayenta, ya rik'e hannun,
     "na miki alk'awarin share hawayenki, a duk halin da kika tsinci kanki, na farin ciki kona damuwa, ina tare dake"
    Ya saka harshe yana share mata hawayen, sai kukan natama ya koma na farin ciki, ya haɗa bakinshi da nata yana kissing ɗinta, har saida yaga hankalinta ya kwanta, sannan ya saketa,

©Rabiatu sk msh

Wednesday, 28 December 2016

HARAMTACCEN ZAMA 41-42

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  41-42

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

     Suna shiga mota kamar ya mata magana kuma ya fasa, sai da suka shiga gida ya bita har cikin ɗakinta, ko a lokacin jikinta a sanyaye yake.
   Ya tsuguna inda take ya ɗaura hannunshi a saman gwiwoyinta, ta zuba mishi ido tana k'ok'arin kauda damuwarta.
    "kina tsoran za'a iya gano HARAMTACCEN ZAMAn da muke ko?" ta ɗaga mishi kai,
   "toh waya sani bayanmu dazai iya faɗa musu har su gane? Wannan tsoran naki ne da shakku kawai matsala na, plz ki daina kinji" tayi murmushi saboda yanayin daya k'arasa maganar,
     "na daina masoyi, kawai gabana ne yake ta faɗuwa"
    "ki manta komai a ranki mana, banason abinda zai rabani dake"
    "nima hakan"

Bayan wani lokaci...
SO DA SHAK'UWAne (Amrah A msh) kullum ke k'aruwa a tsakaninsu, wani kulawan sai tsakanin Majeed da Majeeda, komai a tare sukeyi, tarairayarta yake sosae kamar k'wai ɗaya a cikin miya, baya shakkar nuna mata soyayyah a gaban kowa, soyayya suke irin babu irinta a duniya,
     Majeed ne ya fito da shirin fita, yasha kyau cikin farar shadda, yana tsaye yana saka agogo itama ta fito da mayafinta,
    "tohh saina dawo masoyiyah, mezan zo miki dashi?"  ta mak'ale kafaɗa kamar wata k'aramar yarinya,
   "nifa da gske bazaka barni ni kaɗai ba"
   "haba tawan, ya za'ai naje wurin ɗaurin aure dake?"
    "tohh ka fasa zuwa mana"
   "Ɗaurin Auren Abbakar ɗin?" ya faɗa yana zaro ido,
    "inkin yarda dai na kaima Aunty zainabu Ajiyanki" ta ɗan saki fuskarta,
    "Anma bazaka daɗe ba?"
  "da an ɗaura aure zan dawo"
    "tohh shkenan muje"

   Suka fito tare, a hanya suna tafiya tana tsaidashi, komai ta gani tanaso ya sai mata, kwaɗayi dai kala-kala shi kuma ya dinga biye mata,
     A k'ofar gidan Aunty zainab ya ajeta, ta sauka sannan ta lek'o tagar da yake,
    "saika dawo," ta mishi kiss a gefen kumatu
    "tohh babe, saina dawo" ya ɗaga mata hannu yana fara'a, saida ta shiga gidan sannan ya tafi,

   Tana shiga Aunty ta taso da fara'arta tana mata oyoyo, ta zube saman kujera, Aunty ta kalleta da mamaki,
    "Halan a gajiye kike?"
  "A'ah aunty, yunwah dai"
Aunty ta zauna kusa da ita,
     "ya gidan naku?"
   "lafiya lau Aunty" sannan ta gaisheta, duk ba yanda Aunty ta saba ganinta ba,
   Ta jawo ledanta ta fiddo Apple ta faraci, sai dafe kanta take,
    "Aunty nace inajin yunwa, ko saina nema abincin?"
   "Tohh ay naga daga gidanki kike, kuma baki sanar dani zaki zo ba"
   "ni ban tsaya na k'oshi ba, ganin zan fito"
    "tohh ay yanzu zan ɗaura na dare" ta mik'e tana dafe da kanta,
    "nidai bazan jira ba Aunty, bara na dafa ko cous-cous ne"
    "sai dai indomie"
  "tohh yana iya" ta nufi kitchen ɗin, indomie ɗinma saida ta rumurmutsi wata taci hakanan kafin ta dafa, ko dahuwa bata k'arasa ba ta juyeta ta fito,
    Aunty nanan inda ta barta, ta fito tana tafiya tana rik'e kanta, ga wani irin tashin zuciyah da takeji idanta shak'i k'anshin indomie ɗin, ta daure dai ta zauna, Aunty tace,
   "wai lafiyanki?"
  "wlhy Aunty ciwon kai nake fama dashi kwanannan, da jiri" taje zata zauna, jiri ya kwasheta ta kusan faɗuwa da sauri Aunty ta taso zata rik'eta, ta daure ta ajje indomie ɗin,
    "Wai yadai majeeda" sai dai kawai gani tayi majeeda ta sulale a wurin,
   Aiko duk ta rikice, ta shiga kiran layin mai gidanta muhd anma yak'i shiga, ta kira layin majeed, taa kusan katsewa ya ɗauka,
    "kayi sauri kazo yanzu majeeda ba lafiya, kayi sauri plz" bata jira me zaice ba ta katse,
  
   Shima jin muryarta a rikice, duk hankalinshi ya tashi, bai tsaya sallama ta kowa ba ya shiga motanshi ya nufi gidan Aunty, tafiyar mintuna kaɗan ya kaishi gidan,
    Ganin halin da Majeeda take ya sakashi k'ara ruɗewa,  baisan sanda ya saka hannu ya ɗauketa ba, Aunty ta biyosu a baya suka wuce Asiti sai kwarara gudu yake, ikon Allah ne kawai ya kaisu,

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 39-40

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  39-40

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   Suna cin Abinci suna firarsu, sai dariya duke, kallonsu kawai zakayi ka gane masoya ne dake matuk'ar son juna,
    Alama ya mata da idanu data juya taga wasu tsofaffi mata da miji A bayansu, suma soyayyarsu sukesha kamar ba tsofi ba ko a nigeria, da jikanyarsu y'ar yarinya mai kyau, A hankali yace mata,
    "na k'agara mu zama kamar tsofinnan"
       "nima sun burgeni sosae"

  Sun gama suna fitowa suka haɗu da Aisha a hanya, tun kafin su ganta ta tsaya tana kallonsu, hannunsu mak'ale da juna, suna tafiyarsu gwanin sha'awah zuciyarta sai bugawa.
   Majeeda taa rigashi ganinta, itama saida k'irjinta ya fara bugawa wani irin kishinta takeji, ta fara k'ok'arin zare hannunta daga nashi, ya rik'eta tsam don shima yaga Aishan, har sukazo suka wuce inda take tsaye kamar bai ganta ba, ta juya taci gaba da kallonsu har suka shiga mota.
    Batace mishi komi ba, anma duk jikinta yayi sanyi, shikam baima nuna mata alaman komi ba yaci gaba da janta da fira har saida yaga hankalinta ya kwanta.
   "plz Yaya Majeed muje gidansu momie da gidansu Umma"
     "Marece yaa farayi sai dai gobe" ta marairaice fuska.
    "kaifa kace saina gaji"
  "nifa naso mu koma gida, anma ki zaɓa ɗaya dai"
     "nidai tohh muje gidan Umma na daɗe banga zahra ba"
      "Gidan momie zamuje nan kika daɗe bakije ba"
     "Duk yanda kace mijin gidanah" ya harareta da wasa
   "mijin gidanki ma ba mijinki ba?" tayi daria sosai,
    "hakane mijina, kuma MASOYINA NA HAR ABADA (mrs Umar)"
     "gsky naji sunannan yaimin daɗi"

Text ya shigo a wayarshi, tana hannunta tana game, shi kuma yana driving.
    "Dubamun text ɗin waye?"
Tayi minimizing sannan ta shiga duba text ɗin, sai da kanta ya sara ganin mai turowan, anma tadai dake.
    "karantamun mana" da ɗan washe fuskarta ta fara karanta mishi,
    "Wai honiee yaushene zaka daina wahalar da zuciyatah ne? Yanzu don kana tare da wannan banzar matar da bama son ta kake ba zaka shareni" ta k'yalk'yale da daria bayan ta gama karantawa,
    "ke kuma miye na daria, sai akace miki ki karanta duka, Aisha ce ko?"
     "harma akwai wata bayanta kenan? Nifa aka mawa ba kaika ba, da gaske dariyar ta bani"
    "nidai naji haushi, ba tun yau ba nasan kina sane da bata gabana"
   "yanzunma ban tambaya bafa"
     "tohh nayi shiru matar gidana" sukai dariya lokacin sunzo k'ofar gidansu, aka buɗe mishi gate suka shiga.

    Tare suka jera suka shiga falon momie na sallama da bak'uwa, ganinsu da tayi tare tama kasa ɓoye farin cikinta, tayi saurin sallamar bak'uwar ta taho sai k'ara washe baki take,
     "tare kuke tafe?" Majeed ya shafa gefen gemunshi ya silalo daga saman kujerar kanshi a k'asa yana gaisheta, Majeeda ta koma inda take ta kwantar da kanta jikinta,
    "Momienah inata kewarki"
  "ba gashi yanzu kinzo kin ganni ba?"
    "ba irin haka ba momie, gidannan ma dukanshi ina kewarshi"
     "Rabani da shagwaɓarnan taki, kunyi sa'a ma daddynku yana gida"
   Ta tashi tana murna,
"Anma naji daɗi sosae momie bara naje in gaisheshi"
      "Tohh ɗiyar daddynta" yanayin momie kawai zaka kalla ka gane tsantsar farin cikin da take ciki.
    Majeeda da Majeed tare suka jera suka shiga falon Abba, shima yaji daɗin ganinsu sosae a tare, ya dinga sanya musu Albarka.
 
    Sannan gabanta ya shiga faɗuwa, tama kasa haɗa ido da Abba, duk a tsorace take gani take kamar zai iya gano abinda suke ciki, duk jinta take wata daban,
   Ta gaya musu kyautar motar da Majeed ya mata, suka dunga mishi godia sosae,
   Majeed ya lura da sukukun da Majeeda tayi, duk hankalinshi na kanta, basu daɗe ba suka tafi.

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 37-38

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  37-38

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

  8:35am
    Ta fara farkawa, kallon bayanshi take bayan ta buɗe ido, ta murgina inda yaketa dubashi bai tashi ba, ta kwantar da kanta kawai a bayanshi tana jin soyayyarshi na k'ara shigarta.
        Gani tayi kawai ya buɗe idanu sannan ya murgina ta koma k'asa, ya tallabo fuskarta yana kallon kyakkyawar fuskarta, itama kallonshi take suna ma suna murmushi, ta ɗan ɗago da fuskarta takai mishi kiss a goshi, ya lumshe ido ya buɗe cikin nishaɗi,
     "kawai bana gajiya da kallonki" ta juyar da idanunta cikin jin daɗin abinda ya faɗa, sannan cikin narkar da murya tayi magana,
   "tohh ka faɗamin magana" kiss ɗinta ya mayar mata sannan yace, "inasonki da yawa Majeeda"
    "Nima ina sonka sosai"

  Tare suka shiga kitchen, a shiririce suka haɗa break fast suna shan soyayyarsu, shi baiso tayi aiki, itama tafi so ita tayi, sai dai sukayi a tare kowah dai baison ɗan uwanshi ya wahala.
    Tare suka zauna suka ciyar da junansu, sannan suka koma barci sai kusan azahar suka farka.

   3:00pm
  Suka fito da shirunsu, tana sanye da wani haɗaɗɗen material skye blue, ɗinkin riga da sket yayi matuk'ar amsarta, tayi kyau sosae da farin mayafi, sark'ar wuyanta ma fara, ba wani makeup tayi ba, anma kyau kam tasha shi.
    Shima sanye yake da wani haɗaɗɗen yadi shima skye blue, ɗinkin yasha aiki mai kyau, ba k'aramin haɗuwa yayi ba, tabbas ba qaramin dacewa sukayi da juna ba.
    Saida suka tsaya suka sha hotuna masu kyau, sannan suka jera suka fito tana kwance a jikinshi,
    "wai ina zamuje?"
  "wurare da yawa, yaune farkon fitarmu, har sai kince kin gaji" ta k'ara kwantar da kanta jikinshi.
    "baka fiddo motan ba Yaya majeed yanzu sai naje can?" duk'awa yayi ya ɗaukota, suna tafiya yana kallon fuskanta cike da soyayya.
   "kanaji dani da yawa"
      "Kin cancanci fiye da hakan" sai da ya buɗe ya sakata, sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver, ya fitar da mota suka tafi.

   Wurin siyar da motoci yayi parking, suka fito a tare tana duba wurin "kamar wurin saida motoci"
     "lallai kifin rijiyace ke, motah zaki tayani zaɓe"
     "wow! Anma dai kowace irice ka ɗauka red colour, ina sonta sosai"
   "Akwai su da yawa, kedai muje ki zaɓamin"
     "zan jiraka a mota plx"
  "kin gaji?" yana ɗaga mata gira.
    Ta ɗaga kai tana dariya, ya buɗe mata ta shiga motan sannan ya wuce wurin, ya ɗan ɗauka lokaci sannan ya dawo, yaja motan suka tafi.
  

     A yana driving ma suna rik'e da hannun juna.
   "Yaya majeed wai me zakayi da mota, bayan wanda kake da?"
     Ya ɗan juyo yana kallon fuskarta, suka sakarma juna murmushi.
    "banso wani ya k'ara ɗaukomin kene daga makaranta, plz karki k'ara shiga motan kowa, ga motanki nan idanma bananan"
   Ta k'ank'ame hannunshi cikin tsananin farin ciki.
   "dagaske motahta ce yaya majeed?"
    ya ɗaga mata kai yana murmushi.
    Wani ihu ta saki, sannan ta faɗa jikinshi, dole yayi parking a hanya.
    "Nagode sosai yaya..." ya ɗaura hannunshi a saman leɓenta.
    "babu godia a tsakaninmu, kinmin Abinda bazan iya biyanki da komai ba Majeeda, ina sonki da yawa, babu abinda bazan iya miki ba" ta ɗago fuskarta suna kallon juna,
    "nifa ban ɗauka wani babban abu na maka ba Yaya majeed, anma nima ka sakani farin cikin da bansan yanda zan bayyana maka shi ba, kullum soyayyarka k'aruwa take a cikin zuciyatah"
   "Kinason jin ta yanda zan gane kinyi farin cikin sosae?" ta ɗaga mishi kai cikin zumuɗi.
   Ya matsa dai-dai kunnanta ya mata raɗa, ta ɗago suna kallon juna ya kanne mata ido.
    "Rannan da zafi fa"
  "wannan bazakiji ba, indai ba baki shirya faranta min ba"
    "A'ah fa na yarda, anma sai gobe" ya ɗaga kafaɗa, "na yarda".
    "Kina jin yunwa?" ta ɗaga mishi kai.
   Ya juyar da motan suka nufi restaurant.

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 35-36

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  35-36

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   Da dare suna zaune suna kallo a falo ta fara rufe ido alaman barci, sannan ta tashi daga jikinshi tana mik'a, "nidai saida safe" ya ɗago yana kallonta "barci?" ta ɗaga kai, "tohh bara in kashe kallon in taho" rausayar dakai sannan ta juya ta tafi ɗakinta, sai da tayi shirin barci sannan ta kwanta sai gashi ya shigo shima da shirin barcinshi.
   "Anan zaka kwana?"
  "ehh mana, in rama miki kwananki" murmushi kawai tayi har yahau gadon ya kwanta.
    "nida na kwana a k'asa?" a hankali tayi maganar, ya jita anma sai yace, "me kikace?" Majeeda tace "bance komi ba"
    Ya jawota jikinshi sannan yace, "anan dai kika kwana" sukai daria su duka, sannan ta juya mishi baya duk da amanne take a jikinshi.

    Sun daɗe a haka, su basui magana ba, kuma ba barci suke ba, ya saka hannu ya kashe fitilan.
   Tsawon lokaci sannan yayi magana a hankali "Meya hanaki barci" tayi shiru kamar mai barcin gaske batace komi ba, ya fara mata tafiyar tsutsa a wuyanta ta nok'e tana daria, "kice wani abu mana" inji majeed
    "me zance?"
"wani abu mai daɗi"
    "plx ka barni nayi barci"
  "plx nima ki faɗamun yanda zanyi barci mai daɗi"

   Ta nisa tana jan numfashi sannan tace, "Ina sonka Yaya Majeed, tabbas aurenah dakai bai cikin zaɓina, sai dai banson sanda soyayayarka ta cikamun zuciyah ba, kai namijine da kowacce mace zatai Alfaharin samu, fatana ko da yaushe in kasance tare dakai har k'arshen numfashina, ina sonka yaya Majeed, soyayyar da bata da iyaka, bazan daina sonka ba har Abada"
   Ya k'ara rungumota jikinshi cikin jin daɗi farin ciki fal a zuciyarshi.
     "nima ina sonki sosae Majeeda, ki kasance a tare dani, zan maye miki duk wani damuwarki da farin ciki, bazaki taɓa dana sanin kasancewa dani ba, ina sonki da yawa majeeda, don Allah karki barni" ya jawo hannunta bayan ya zare zoben hannunshi, ya saka mata, ta damk'e lallausan hannunta cikin nashi "zan kasance tare dakai har gaba da Abada yaya Majeed"
    "Na shirya miki wani albishir gobe, anma bazan faɗa miki"
   "plz mana yaya majeed"
"idanna faɗa miki bazai miki wani daɗi ba, kin gani da idonki" tace "tohh shknan" anma badon taso, duk tunaninta ta kasa gane ko Albishir ɗin menene, gashi ba ranar birthday ɗinta bane, ta hak'ura dai a haka barci ya ɗaukesu

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 33-34

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  33-34

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   Tasha barci sosai har 10 ta wuce sannan ta tashi, a hankali ta buɗe idonta tana kallon gefen da yake, bainan sai dai ta hango takardar daya mata rubutu a jiki "Good morning" ta ɗanyi murmushi sannan ta dire k'afafunta k'asa ta sauko ta fito falon tana tafiya a hankali, anan ma bainan ta wuce ɗakinta kawai.
    Shiryawa tayi cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga mai shegen kyau, da kaɗan ta wuce mata gwiwa, itama ɗan k'aramin hannu ne da ita, saboda yanda takejin jikinta bazata iya ɗaukar kaya mai nauyi ba, gashin kanta ma data tubke ji take duk ya mata nauyi, ta warwareshi kawai ta ɗan kwantoshi daga gaba, ga wani k'amshi da yake tashi ko ina a jikinta.
    Da fara'arta ta fito cikin nishaɗi, har lokacin bai falo, ta wuce dinning table kawai hango kululon da ita a jere daman yunwa takeji.

     Tana tsaye ta fara buɗa kulan farko farfesun kaza ne, na biyun kuma soyayyan dankali ne, tana cikin buɗewa taji an rungumotah ta baya, sannan ya sak'ala hannuwanshi cikin nata "kin tashi lafiya?"
  "lafiya lau sannu da gajia" ya sakar mata kiss a wuya, ta nok'e tana daria sannan yace "gajiarme", "kasha girki mana"
   "ba wani gajia tunda masoyiyatah na girka mawa" daria tayi sannan ta juyar da kanta ta kwantar a kafaɗarshi, "kema ya taki gajiyar?"
    "gajiyar me?" ta tambayeshi yana daria sai so yake ta ɗago da fuskanta "kinaso in faɗa?" ta k'ara shigar da kanta a jikinshi tana daria "A'ah, nima ba wani gajia tunda masoyinah na faranta mawa" dariya suka yi dukansu, tace, "nifa Yaya Majeed na qagara naji girkinnan" a shagwaɓe tayi maganan, "yanzu kuwa," yaja mata kujera ta zauna, sannan ya zauna kusa da ita.

    A plate ɗaya ya zuzzuba musu, ta ɗauko fork zata fara ci ya rik'e hannun, "daga yau wannan aiki nane" ta buɗa idanu tana daria, wata sabuwar soyayyar majeed na k'ara shigarta, ji tayi tafi kowacce mace farin ciki da samun Abokin zama wanda yake bata kulawarshi,
    Haka yaci gaba da bata a baki har saida ta k'oshi, sannan ya langaɓe kai cikin wani salo "Saura ni", itama langaɓar dakai tayi "nifa bakacemun zanyi aiki ba" shikenan tunda bazaki bani ba, ni bama zanci ba ya tashi kamar zai tafi.

   Dariya sosai ya bata tace "toh shikenan daman nasan ka k'oshi tun a kitchen" ya dawo da sauri ya zauna, "bazaki lallaɓani bama ko?" ta jawo fork ɗin, "anma sau ɗaya zan baka", ya marairaice "Yana iya tohh? Na yarda" ta ɗebo abincin ta nufi bakinshi dashi, saida ta kusan saka mishi ya buɗe bakinshi, sannan ta juyar da cokalin ta cinye tana daria "laah! Aikam bazan yarda zaki biyani ne" ya jawota yana k'ok'arin saka bakinshi a nata sai k'yalk'yatar daria suke.
    Haka ya gama cin Abincin a shiririce, sunayi suna nishaɗinsu irinnan na ma'auratan gaskennan,

   Ranar da yake friday ne bai fita office ba, wurinta ma babu maganar zuwa ckul, soyayarsu suka dinga sha kamarsu cinye juna, sai tarairaya majeeda takesha a wurin majeed, ko motsi zatayi tare suke motsawa😉 yananan lik'e da ita, kunsan irin farkon soyayyarnan.

   Komai batayi ba ranar, girkin rana ma shine ya musu sai dai ya zaunar da ita falo ya kunna mata kallo, ta narkar da fuska  a shagwaɓe tace "nidai banson kallonnan, k'ara muje can kitchen a tare ko bazanyi komai ba ina kallonka"
   Ya kamo hannunta yana shafawa a fuskarshi "banso ki shigo kimin dariyan ban iya ba, kiyi kallonki, indai ninema bazan iya minti 2 bana ganin fuskarki ba, zan na fitowa" ta k'ara marairaicewa "nidai..." ya ɗaura hannunta a leɓenshi, "plz kiyi kallonki" ta ɗaya mishi kafaɗa sannan ya juya ya tafi girki.
    Bai minti biyu zai fito ya sumbaceta cikin soyayya, sannan ya koma a haka harya gama girkin.
     Da dare ne dai saiya fita ya musu take away, wannan rana ku biyu sun zame musu na farin ciki sosai.

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 31-32

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  31-32

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   Duk wani ihu da take tana tuttureshi harda cizo da yakushi bai tsaya saurara mata ba, baimasan tanayi ba har saida ya fara jinshi dai dai sannan hankalinshi ya dawo jikinshi, kwantawa yayi gefenta yana maida numfashi kamar wanda yasha gudu.
    Kasa koda motsi tayi, har lokacin hawaye take, maido nepa da akayi ne ya sakashi mik'ewa ya haɗa mata ruwa mai zafi a toilet, yazo inda take ya saka hannu zai ɗauketa ta buge hannu, yaja baya, "kinga karki k'arama kanki wahala idan kin shiga ruwan zafi zaki rage jin ciwon" dak'yar ya lallaɓata ya kaita toilet ɗin, sai harararshi take, shikam dariya yake abinshi saboda wani irin farin ciki da yakeji.
     Cikin kwamin wankan ya direta, taga yak'i ya fita, "me kuma kakemin anan" ya shafi gemunshi "wankan da kika tambayeni kozan taimaka in tayaki, shine zan miki",
    "Haba Yaya majeed, plz nidai ya isa haka, ka ficemin plz", "tohm saikin fito, ga wani ruwan nan a bocket wanda zaki wankan tsarki" "naji" kawai tace da taga alaman in batayi magana ba bazai fice ba, sannan ta maida kanta tana jin wani yanayi daban.
    
   40mnts later
Ta fito tana tafiya dak'yar, har ya gyara shimfiɗar ya canja zanin gado, ta kwanta gefen gadon sannan ta juya mishi baya, mirginowa yayi inda take ya kwantar da kanshi saman kafaɗarta ta tureshi muryarta da alaman kuka take tace, "wai me kakeyi haka Yaya Majeed? Kasanfa abinda kakeyi haramun ne" ya ɗan rage fara'arshi, bayan ya kamo hannuta yana wasa dashi "me nayi da ba dai-dai ba? Ɗazun da kika k'udundune a jikina na hanaki ne?" ya kai mata cizo a yatsanta daya saka a baki ta saki k'ara, da sauri takai mishi bugu a k'irji, "bafa wasa ake ba Yaya Majeed" sai kuma ta fashe da kuka sosai.

    "Ka cuceni yaya majeed, shikenan ka rabani da abinda nake tak'ama da, yanzu wanne namiji ne zai aureni a haka bayan kai kamin saki uku? Zina fa kenan muka aikata, da wanda bai sona kuma"
   "Bayan NI DAKE, wa yasan zina muka aikata? Kin manta duk duniya tana mana kallon miji da mata ne? NI DAKE ne kawai mukasan babu aure a tsakaninmu"
    "Zamuci gaba da zama a haka ne? Kasan dai duk daɗewa dolene zanje na auri wani" hannunta dake rik'e a nashi ya ɗaura a bakinshi,
   "ki daina faɗar haka plz, karki rabu dani Majeeda, sai yanzu na gane sosai ina buk'atarki a rayuwatah, wannan sirrine tsakanin NI DAKE, kinsan dai idan har iyayenmu suka san halin da muke ciki tsinuwa ne kawai, kuma dole su rabamu" ya marairaice fuska, "banson na rasaki a rayuwatah"
     Tunda ya fara magana take kallonshi kamar wani zararre, anya Yaya majeed yana cikin hankalinshi? Baki a buɗe tace "HARAMTACCEN ZAMA zamuyi kenan?"
    "kada ki zurfafa tunaninki mana, ki manta kawai da yanzu babu aure a tsakaninmu, ki kalleni a matsayin mijinki, tunda babu wanda yasan sirrinmu, muma mu manta abinda ya faru", hafsatul kiram ce ta faɗo mata a rai, ita kaɗaice tasan sirrinta da majeed, tohh anma yanzu ai basu k'asar sun tafi moscow ita da umar ɗinta, kuma ta yarda da ita bazata taɓa faɗama wani sirrinta ba.
     "nidai bazan iya HARAMTACCEN ZAMAn nan ba, kowa yaci gaba da harkarshi kawai tunda daman ba sona kake ba, kawai sha'awanah kake"
    "Waye ya faɗa miki bana sonki?" yayi saurin katseta.
   "bai kamata wannan maganar ta fito daga bakinki ba, ni kaina bansan sanda na fara sonki ba Majeeda, anma ki yarda dani ina sonki, tun lokacin dana kasa ɗauke idanuna daga kallon kyakkyawar fuskarki a wancan ranar, na tsinci kaina da matsananci tausayinki a lokacin da kika fara rashin lafiya, har nakejin daman ciwon ya dawo a jikina, wannan ba so bane? Duk inda zanje koda na fita daga gida tunanina yana a kanki ta yanda bazan iya ɗaukar lokaci ba sai nazo na ganki, a hakan ba sonki nake ba?, da meyasa bana sha'awar jikinki sai yanzu? Idan har banisonki bazan taɓa sha'awarki ba, bansan yaushene ba ko kuma tayaya na fara sonki, anma na rantse da wanda raina yake a hannunsa ina sonki fiye da yanda nake son kaina,"
    "kafin yanzu ina buk'atar, abinci, ruwa da iska ne kawai don in rayu, anma yanzu rayuwatah tana matuk'ar buk'atarki majeeda"

   Share hawayenta tayi cikin farin ciki ta kwantar da kwanta a k'irjinshi, "nima ina sonka sosai yaya majeed" ya saka hannu yana shafa gashin kanta shima cikin jin daɗi yace, "Kin yarda zamuci gaba da zaman aurenmu?" ta ɗaga mishi kai.

OMG😱 ZAMAN AURE KO DADIRO? mamakin kam bai barni naa ci gaba da rubutu ba har suka shige bargo suka barni hangame da baki😷

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 29-30

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  29-30

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   Ana gama sallahr isha'i ya shigo gidan, kai tsaye ɗakinta ya nufa har lokacin tana kwance da ciwon ciki.
    Yaje inda take "Sannu ya jikin?" kai kawai ta ɗaga mishi "don Allah ka haɗamin ruwa mai zafi a toilet" da sauri ya mik'e ya tafi haɗa mata ko 5mnt ba'ai ba yace "gashi can" dak'yar ta mik'e tana tafiya, ya bita a baya yanaso ya rik'ota don gani yake kaman zata faɗi, sai da takai k'ofar har ta shiga taga bai koma ba cikin gatse tace "ko zaka taimaka min da wankan?" da sauri ya koma yabar wurin bayan ta rufe k'ofar.
    Sai da ya tabbatar tasha magani, ya tsaya har barci ya ɗauketa sannan ya bar ɗakin nata.
   Kwana biyun da tayi tana ciwon ciki duk shine yake kula da ita, wani lokacin sai dai ta tsaya tanata mishi kallon mamaki wai yaya majeed ne haka yake mata hidima,
    Cikin kwana biyunnan ba k'aramin shak'uwa sukai ba, ko fita yayi yanzu yaa daina daɗewa zai dawo gidan koda bazasuyi magana ba, itama duk inda yaje a k'agare take ya dawo.

    Ta gama kwanakin da take tayi wanka, yanzu taa samu sauk'i, anma duk da haka yana shiga ɗakinta yayi tsaye kawai bazaice komi ba, ko su haɗu falo kallo anma babu wani magana tsakaninsu.
     Yau tun kusan da rana hadari ke haɗuwa yana washewa, shima ya hanata fita taje makaranta, anma har dare ba'ayi ruwa ba.

10pm.
    Aka fara iska mai k'arfi, tana kwance ɗakinta bayan majeed ya lek'o ya fita, tayi shirin barcinta da er qaramar riga iya cibi mai hannu bra, sai sket ɗan qarami ko cinyoyinta bai gama rufewa ba, anma saita rufa cikin bargo fuskarta da hannuwanta ne kawai a waje, ta saka charge tana chatn.
    Tunda aka fara iskan tayi kasak'e tama kasa chatn ɗin, abinka da jaharmu ta katsina😉 ana fara iskannan ba daɗewa aka ɗauke nepa, da sauri ta maida kanta cikin bargo tana jiran a tada Gen, wani irin tsoron da bata taɓa ji ba ya kamata, har aka fara ruwa a duk'unk'une take duk taa tsorata, ba shiri ta jawo zaninta dake gefe ta ɗaura sannan ta zura hijabinta, ta yaye bargonta a hannu da sauri ta nufi ɗakin Majeed tana haskawa da fitilan wayanta sai sauri take tana waige-waige, tana zuwa ta faɗa kawai sannan tayi sallama.
   Yayi ɗai-ɗai saman gadonshi dagashi sai Vest da gajeren wando, ya ɗago yana kallonta duk tayi tsuru-tsuru da jingin kaya a hannunta, gajiya tayi da kalan kallon da yake mata tace, "an ɗauke wuta kuma naga ba'a tada Gen ba, nidai tsoro nakeji ni kaɗai gashi ana ruwa"
    "Ɗakin naki ne kike tsoron kwana?" ta ɗaga mishi kai.
     "tohh shknan ki kwanta anan bara in koma falo" ta ware manyan idanunta cikin ɗan hasken fitilan tana kallonshi.
    "Inyi zamana a ɗakina mana, Ai wallahi falonma sai dai mu tafi tare" ta fara warware bargonta ta shimfiɗa gefen gadon da yake daga k'asa, ta buɗa wardrobe dinshi ta jawo wani bargon ta kwanta sannan ta rufa dashi duk yana kallonta.

   Led lamp ɗinshi ya jawo zai kashe, "Don Allah yaya Majeed karka kashe hasken tsoro nakeji," ya maida ya ajiye sannan ya jawo bargonshi shima ya rufa duk sukayi shiru.
    Can aka fara wata irin tsawa, ta wani k'ank'ame gadon cikin tsorata tana karanto addu'ar da akeyi in ana tsawa (subhanallazi yusabbihul ra'adi, bihamdihi walmala'kati min khifatihi) tana maida numfashi da sauri da sauri.
   "kinga nifa bazaki hanamun barci ba da wannan tsoran naki, sai wani k'ara kike..." tun kafin ya rufe baki aka k'ara wata tsawar, batasan lokacin da tayi wurgi da bargon da take ciki ba ta haye saman gadon daman tuni taa cire hijabin jikinta, wurin hawan gadon zanin ya cire ta faɗa jikin Majeed ta ruk'unk'umeshi, yasa hannu zai cireta daga cikin shi ta k'ara rik'eshi tana jan numfashin tsoro, saitin kunnanshi take jan numfashin, gaba ɗaya taa gama rikita shi.

    Tananan a jikinshi har aka gama ruwan saura yayyafi, anma duk da haka bata sakeshi, kallon k'irjinta yake yanda zuciyarta ke harbawa, komai nata a bayyane, ga wani irin k'amshi dake tashi ko ina a jikinta, ya fara kai hancinshi yana shinshinar wuyanta, ya saka hannunshi dai-dai cibinta yana shafa cikin, duk da ta shiga yanayi bai hanata rik'e hannun nashi ba, ko tsawa saurararta baiyi ba ya fara kissing ɗinta ta ko ina, yana sarrafa jikinta yanda yaga dama duk ya rikece.
   Ita ɗinma ta fara manta a wacce duniyar take, tuni yaa  rabata da duk wasu kaya dake jikinta, bata tashi tsorata ba saida taji yana niyyar shigarta, ta fara tureshi anma yak'i sakinta, harda ɗan kukanta "Yaya majeed ka daina, babu kyau fa", ya ɗago da jajayen idanunshi cikin sark'ak'k'iyar murya, "Plz majeeda kar muyi haka", cikin wata irin murya dake k'ara rikitashi "Nidai a'ah yaa maj...." ya hanata k'arasawa, ya haɗa bakinshi da nata, cikin kalan nashi salon mai rikitarwa.

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 27-28

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  27-28

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

Sauri tayi ta tashi zaune, ciwon cikin ma taa daina ji.
   "ki tashi kiyi break fast"
  "Yaya majeeed me kakeyi har yanzu ba nasha maganin ba?"
    "eeh anma ai bakici komai ba, donma kin samu an nuna miki kulawa?"
     "naji anma dai ka fita zansha"
  "indai kinason in fita sai kinsha koda tea ne, ko so kike a fara cewa ban kula dake?"
   "wama zaisan banda lafiyan? Nidai nagode hakanan"
    "Yanzu wani yasan ciwon ciki kike me zasuyi tunani?" yaja tsoki, itama shiru tayi bata k'ara cewa komi ba.

Bai hak'ura ba saida ya haɗa mata tea, sannan ya fita "Gobe in Umma ta k'ara tambayanki kice ban kaiki asibiti ba ko ban kula da cin abincinki" yanayin yanda yayi maganarne ya sakata murmushi, ko umma ce ta mishi magana?
   Bai k'ara shigowa ɗakin ba, da rana yunwa ta isheta, gashi duk jikinta babu k'arfin da zata ɗaura girki, kuma tea yaa isheta hakanan, hakanan dai ta fito da nufin shiga kitchen ɗin ko zata samu abinda zataci.
    A tsakiyar falon suka haɗu da plate a hannunshi shak'e da yankakkun fruit, ta ɗan kauda kanta zata wuce.
       "ban ɗauka zakici abinci ba shiyasa na taho miki da fruit kawai" ta juya zata tafi
   "shima na k'oshi fa" ta koma zata tafi, "tohh me kikeso a anso miki?" "ba komi fa" taci gaba da tafiyarta, rik'o hannunta yayi, tana niyyar k'wacewa suka jiyo sallamar Aunty zainab tana shigowa ɗakin da sauri ya saketa.
      Kamar ta koma a ranta tace nifa shiyasa banson zuwa gidan yara, majeed yace, "sannu da zuwa Aunty" ta amsa tana niyyar zama
   "Aunty kizo shigo daga ciki mana," ta matsa daga wurin Majeed suka wuce ɗakinta tare da Aunty zainabu" bayan sun zauna ne Aunty zainabu dai ta gaji da kallonta ganin dai k'arfin hali kawai take.
    "Anma dai baki lafiya ko?"
"eeh anma naa warke"
     "me akace yana damunki?"
   "A'ah bamuje asibiti ba, ina dai jin...."
    "kinajin me Majeeda? Zaki zauna da laulayi ne bazakuje asibiti ba kamar dai wacce batayi karatu ba?" maganar Aunty ma dariya ta bama majeeda,
   "Aunty ciki kuma? Nikam kowah ma ya samin ido dole ne daga mace tayi aure sai haihuwa? Nidai ulcer tace ta ɗan tashi"
   "ba dole bane anma don me ake auren? Karma ki fara sanyama ranki wannan, ni ba gashi ina jiran haihuwar ba Anma har yau Allah bai nufa ba"
       "ni Aunty kima daina maganar nan"
   "saboda me?" ta tsareta da kallon tuhuma, ta kasa magana, sai ga majeed yayi sallama ya shigo.
   Suna gaisawa da majeed, Majeeda ta mik'e, "Aunty me za'a girka miki?" "kinga basai naci komi ba daman a hanya nake, garin damuna k'ara in sauri in wuce" cikin wasa majeeda tace "Aunty ko ruwa dai aka fara ai a gida kike, kuma dai yaune zuwanki na farko", "ina laifi ma da kika ganni?" majeed yace "ba laifi Aunty anma mudai yini mukeso" daria tayi sukaci gaba da fira harda majeed, sai da ya fita sannan ta jawo ledar magungunan mata masu kyau ta mik'a mata tana mata bayaninsu.
    Saurarenta kawai take, ita dai ba buk'atarsu gareta ba, babu amfanin da zasu mata sai dai tayita ajiya kar tak'i amsa Aunty tayi tunanin wani Abun.

   Aunty Zainabu bata daɗe ba ta tafi, Majeed ma lokacin ya bar gidan.
   5:00...
      Taji dai yunwar tak'i saurara mata, tun safe fa tea kawai tasha, daurewa tayi ta shiga kitchen ta fasa k'wai dai dai cikinta ta soya, sannan ta zauna falo ta cinyeshi tas tasha ruwa, sannan ta fara jin kanta.
    Sai dai me, kamar abinda ciwon cikin ke jira kenan, tun kafin ta tashi daga wurin mararta ta fara wani azababben ciwo, dak'yar ta iya kai kanta ɗaki.
   
©Rabiatu sk msh

Monday, 19 December 2016

HARAMTACCEN ZAMA 25-26

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  25-26

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

    Da Asuba, ciwon mara ne ya farkar da ita, tun cikin barci ta fara juye-juye harta farka, ta dafe cikinta ko motsi batason yi, tanason ta ɗauko maganinta anma ta kasa tashi saboda yanda ya matsa mata.
      Dak'yar ta samu ta mik'e ta jawo jikkarta ta fara laluben maganin sai dai kwalinshi babu ko ɗaya, kamar ta fasa kuka ga wani irin azababben ciwo, haka tana duk'ewa ta samu ta haɗa ruwan zafi a toilet taje tayi wanka anma duk da haka kamar ana k'ara tunzuro ciwon cikin gashi ita kaɗai a ɗaki.
     Dak'yar ta iya k'arfin halin kwaso kuɗi a jikkarta ta fito mai gadi ya siyo mata, da yake a ɗan duk'e take tafiya rik'e da cikinta ga azabar ciwo, bata lura dashi yana shigowa falon ba ita kuma zata fita harta kusan kai mishi karo, da sauri ta dawo da baya, kanta a k'asa tabi gefenshi zata wuce, shima gefen da zata wuce yabi suka kusan haɗewa a tare, kuma kowannw ya koma ɗayan gefen, da suka kasa wucewa dai ya saka hannuwanshi biyu saman kafaɗarta, sannan ya juyar da ita ya wuce.

    Wani irin murɗawa cikinta yayi anan ta duk'e-duk'e rik'e da cikinta, ta daɗe a haka kafinta iya mik'ewa tana ɗagowa suka haɗa ido da majeed, duk ta daburce tace, "yadai?" yaɗan saki fuskarshi "ba komi", sannan ta juya ta wuce a wahalce.
     Bata iske mai gadi ba, da alama bai gidan gashi duk taa gama jigata, haka ta lallaɓa ta koma ɗakinta, tana faɗawa gado ta saki kukanta marar sauti ga ciwon sai k'aruwa yake, ta dinga murgina saman gado harta sauko k'asa.

    "Ga maganin" taji ya ambata, ta ɗaga fuskarta tana kallonshi rik'e da laida a hannu, ya ajje robar faro da cup a kusa da ita, ta mik'a hannu ta ansa maganin, irin wanda takesha ne da pad guda biyu, ta ɓallo guda ɗaya ya mik'a mata cup ɗin ruwa ta haɗiye dak'yar sannan tace "na gode" ta koma ta sulale k'asa tana jiran ciwon ya lafa, a haka barci ya kwasheta duk taa k'udundune wuri ɗaya.
    Tausayi ta bashi ganin yanda tayi kwanciyar duk taa takura, lokaci ɗaya har taayi ramar dole, sai lokacin ya tuna ko break fast batayi ba ya bata magani, da sauri ya tafi kitchen ya ɗauko flask da kayan tea ya ajje mata.
     Tananan kwance inda ya barta tana barci, anma da alama batajin daɗin barcin ciwon cikin ma bai gama sakinta ba sai rumtse ido take tana rik'e ciki.
        Bazai juri ganinta a k'asa ba, ya saka hannu ya tallabota, kamar yaa ɗauka jaririya, ya dire ta saman gado, tun lokacin da yaa ɗaukota ta farka, anma ta kasa buɗa idonta wani irin kunyarshi maa takeji.
   Megasa Yaya majeed zaina taɓani koya manta yanzu babu aure tsakaninmu? tunaninta ya katse saboda yanda mararta ta k'ara juyewa, tai wani irin k'ara batasan lokacin data k'ank'ame hannunshi da hannu ɗaya ba, ɗayan hannunta na rik'e a cikinta har lokacin da yake yana tsugune saitinta.
   Wani irin tausayi take bashi ganin yanda takeyi, fuskarshi kamar zai tayata kukan, ya kalli hannunta dake sak'ale a nashi, zara-zaran yatsunta masu kyau sosai da taima ado da jan lalle, baisan sanda yaci gaba da murzasu a hankali ba yana kallon kyakkyawar fuskarta, sai runtse ido take, ga ciwon ciki, ga wani irin yanayin da takeji hannunta rik'e a hannun majeed.

   Kallonta yaci gaba dayi, sai yanzu ne yake k'are mata kallo, ya saka hannu ya yaye mata yalwataccen gashin kanta mai sulɓi daya rufe mata fuska, fara ce tas, irin farinnan mai kyau, gashin girarta gazar-gazar mai kyau kamar an zana mata shi, gata da manyan idanu masu kyau da ɗaukar hankali, girar idonta bak'a wulik koda a rufe suke idanunta k'ara kyau suke, da dogon hancin ta wanda ya dace da kyakkyawar fuskarta, idanunshi ne suka sauka a kan ɗan 'karamin bakinta (pink lips), ya tuna yanda take motsashi idan tana mishi masifa, sai yaji ta burgeshi ma idan suna faɗa kyau yake mata.
   Yanzunma motsashi ta dingashi kamar zata tashi, dimples ɗinta na lotsawa, a hankali yakai ɗayan hannunshi zai shafi gefen fuskarta, kamar ance ta buɗa ido, ya sauka cikin nashi da sauri ya mayar da hannun

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 23-24

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                 23-24

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

  Tsayuwar ta fara gajia da ita ta ciro wayarta tana dubawa, ba don tana da abunyi da ita ba, sai don kawai ta rasa abinyi gashi har lokacin ba wani motan da zata hau.
       Wata haɗaɗɗiyar mota ce ja, mai shegen kyau ta wuce inda take, sai kuma akayi reverse da motar aka dawo saitin da take, kaudar da kanta tayi sannan ta matsa gefe. Kusan mintina biyar mai motan bai fito ba kuma shi bai tafi ba ita kamar ma batasan da wani mota a wurinba.
    Buɗe motan yayi ya fito da takunshi na k'asaita, "Masha Allah" na faɗa saboda irin kyaun dana hango a tattare dashi, harna kusan jefar da wayata kasancewar darene ina tunanin ko Aljani ne, dai dai inda Majeeda take ya tsaya.

    "Da alama kina jiran Abin hawa, gashi kuma dare ya fara nisa zai miki wahalan samu" kajimin mutum ko ina ruwanshi dani
   "hakane zan samu insha Allah"
      "Zai miki wahalan samu fa, kiyi shawara da zuciyarki idan harta amince miki zan kaiki har inda kikeso, babu daɗi kamilalliyar mace kamarki ta tsaya a titi a cikin darennan"
    Maganarshi fa hakane, idanma ya tafi ya zata samu wanda zai kaita gida? Kuma da alamar natsuwa a tattare dashi ta san bazai cutar da ita ba, gaba tayi wurin motar kawai ba tace komi ba, ya buɗe mata yaci gaba da karanto addu'ah a ranta.

    Har k'ofar gidanta ya kaita "ajjeni nanma yayi" yayi parking ta fito tana mishi godia, murmushi kawai yayi yaja motanshi, dai dai lokacin majeed shima ya sako motanshi kuma yaga lokacinda ta fita daga motan.
     Kamar wanda ake hankaɗawa ya shiga gidan tana dai-dai shiga ɗakinta yasha gabanta,
    "daga gidan ubanwa kike?" na ɗauka "gidan ubanka zatace"😄 tunda gidansu taje,anma sai tace "gaishe dasu Umma mana, kana da matsala da fitata ne?"
     "k'arya kike tun ɗazu Umma tacemun kin taho, wane ɗan iskane ya maidoki?"
   "kash!" ta dafe kanta da hannu ɗaya "kaga nama mnta ban tambaya sunanshi ba, ragemin hanya yayi, babu ruwan wani da harkar wani" shiru yayi yana kallonta yama rasa bakin magana, tohh meyasa ma ya tanka mata? Shi ina ruwanshi kowa ma zata kula.

   Ta juya ta barshi anan zata shige ɗakinta, k'afarta ta zamo bata ankara ba ta taho zata faɗo da sauri ya tare ta ta faɗa a k'irjinshi ta tallabeta da hannuwanshi, kallonshi take cikin fargaba saboda yanda ta kusa faɗuwa, sai maida numfashi take, shima kallonta yake cikin ido, wani irin yanayi da bai taɓaji ba ya ziyarceshi wannan kallon da suke ma juna.

   K'ara matseta yayi a k'irjinshi, tsawon lokaci suna a haka kafinta lumshe kyawawan idanunta ta buɗe, idonshi dai-dai laɓɓanta ta buɗesu a hankali tace "da zafi" yanda ya mata rik'on, sakinta yayi yana dai-daita kanshi, sannan ya juya ya tafi yana waiwayenta, itama kasa motsawa tayi daga inda take ta k'ura mishi ido cikin wani yanayi harya shige ɗakinshi.
      Jiki a sanyaye ta shige ɗakinta, ta kasa mantawa da yanayin data motsa fuskar majeed ce ke mata yawo a sanda take a k'irjinshi.
    Haka Majeed ma ya kwanta barci da tunanin abinda ya faru, daya rufe idonshi yanayin yake dawo mishi, koda ya buɗe kuwa bazai daina ganinshi da majeeda rungume ba, juyi kawai ya dingayi a lallausar katifarshi yana jiran lokacin da barci zai ɗaukeshi.

Hmm niko nace kome hakan ke nufi??

©Rabiatu sk msh

Sunday, 18 December 2016

HARAMTACCEN ZAMA 21-22

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  21-22

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

   Kwana biyu tayi tana tunanin yanda zata rama abunda Majeed ya mata anma taa gaza samun mafita, gashi kullum sai ya raba dare kafin ya shigo gidan, tunda safe kuma yake fita, ita yaa maida ita er gadin gida duk da baiyi mata shamaki da fita ba.

   Yauma da marece sosai ta dawo daga lecture, suna hanya drivern ta ya ɗaukota, da yake hanyar gidansu majeed ne, hakanan taji tanaso taje gaishe dasu, ta cema drivern ya biya da ita.
    Ya ajjeta ta fito har zata tafi kuma ta dawo "malam balah zaka iya tafiya, zan ɗan daɗe ne" yace, "tohh hajia" sannan ta shiga gidan da sallamarta. 
     Zahra taci karo da ita, aikam ta buga uban tsalle da gudu ta taho rungumeta "Oyoyo Matar Yayanmu"
     "Aifa sis kamar a bakinki aka raɗa wannan suna, ina umma?"
    "tana ciki ki shiga bari inzo"
     "tohm naa bari".

Ta yaye labulen ɗakin Umma ta shiga haɗe da sallama, ta ɗago tana amsawa tana ganin Majeeda ce ta k'ara faɗaɗa fara'arta tana mata sannu da zuwa, sai yanzu ne ma wata kunya ta k'ara nannaɗeta, ta duk'a har k'asa tana gaida Umma ta amsa mata.
      "Ina majeed ɗin ko ba tare kuke ba?"
    "Daga makaranta ne yace Driver ya kawoni, anma zaizo ɗaukana Umma"
     "Tohh Allah kawoshi lafiya, kuna dai zaune lafiya ko?"
     "Alhmdlh Umma"
  "ki faɗamin gaskia dai naaga duk kin rame" wai taa rame fa, tace a ranta, tana tuna randa taje gida momie cewa ta dinga yi taayi k'iba taayi haske, alamar dai tana mata zargin ciki ne da ita, da yake momie ce sai ta ce mata "momie ni kece uwah ta farko da akama ɗiyarta auren dole kuma tazo ganin gida a ce mata tayi k'iba" momie tace "watau ma auren dole aka miki ko? Kina nufin har yanzu baku zaman lafiya da mijin naki?" tace ma momie, "ba haka nake nufi ba momie".

      Umma ce ta katse mata tunani "Yadai kikai shiru Majeeda? Indai da matsala ki faɗamun in tsawata mishi"
     "ba wani matsala Umma, kawai kwana biyu banji daɗi bane" ta k'ak'alo k'arya.
   "tohh Allah ya k'ara lafiya kundai je asibiti ko?"
   "Ai naaji sauk'i Umma"

     Zahra ce ta shigo ta janye ta suka koma can ɗakinta da fira, itama tsokanarta take kodai sun samu rabo,
    "nikam sis kamar Abinda kowa ke jira kenan, duka yaushe aka gama hidimar bikin ko hutawa bamu yi ba?"
       "Abinda kowa ke jira mana kenan, in hutawa ne kam ai kinyi, anma burinsu Abba kenan kullum ganin en jikokinsu"  sai da gabanta ya faɗi, tayi shiru tama rasa abin cewa, tohh ta inama zata samu cikin tunda ba auren garesu ba?.

   Haka ta yini cikin gidan duk tayi sukuku kuma, har bayan isha'i taa rasa yanda zata tafi kuma gashi tace ma Umma Majeed ne zaizo su tafi, yanke shawarah tayi kawai ta kira malam balah, shi ɗinma ta dinga kiranshi anma wayanshi a kashe.

Wurin 9 Umma ta lek'o ɗakin Zahra, "wai ina majeed ya tsayane?"
        "Umma inajin dai wani abunne ya rik'eshi, anma zan tafi kawai kar dare yayi sosai"
    "A'ah ya zaki tafi ke kaɗai? Ki mishi waya dai yayi sauri yazo ku tafi" ita kam ko number wayarshi ma bata da, yama za'ayi yazo ɗaukanta.

   Har 10 tayi ta rasa dabarar da zatayi tabar gidan Umma, su duka suna zaune a falo, gabanta sai faɗuwa yake, tun farko ma meya sakata yin k'arya.
      Sa'a tayi wayarta ta fara ringing, tayi saurin maida wayan silent sannan tayi kamar taa ɗauka sannan ta ɗan matsa daga inda su Umma suke ta fara magana yanda zasuji.
     "hi, lafiya lau ya aiki?" ta ɗanyi shiru sannan tace, "A'ah ya za'ai na tafi kace na jiraka?"
     "Ayyah! Tohh a dawo lafia, sai ka dawo gidan" tun kafin ta zauna Zahra tace "Halan ina ya tsaya?"
      "wai kinji fa gaisuwar wani baban ɗan wurin aikinsu sukaje Mashi, anma suna hanya kuma motan a cike take, yace inje a napep" Umma tace, "Ayyah!Allah yaji k'an musulmi, sai kiyi sauri dare na k'arayi, tace "tohh shknan Umma"

Zahra ce ta rakata har bakin titi, sun daɗe suna tsaida abin hawa duk da mutane a ciki gashi batason hawan mashin, dak'yar suka samu wani mai napep ta shiga sukayi bankwana da zahra.
    Har ya tada zai tafi Yace "hajia ina za'a kaiki?" tace, "G.R.A"
     "kiyi hak'uri hajia bazanje can yanzu ba ina ɗan sauri ne" babu yanda ta iya ta fito daga motan gashi dare ya fara nisa 10:3., ta juya ko burbuɗin Zahra babu, ga unguwar babu mutane.

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 19-20

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  19-20

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

  Cikin jin haushi tace, "Anma dai in ba'a kawoni da ɗaki a gara ba an kawo ni da cous-cous ko?"
    Baiko ɗago ya kalleta ba Yace "Anma a gidana kike zaune, indai zaki zaunamin a ɗaki, dole ne kimin girki, bayan wannan babu wani abu" ba tace mishi komi ba ta koma kitchen ɗin don yanzu batason magana tayi nisa tsakaninsu yanzu zasu fara faɗa.

Bayan wata biyu...
   Majeeda ce sanye cikin doguwar rigar material, ta ɗaure kanta da ɗan kwalin, ta jawo Abayarta har k'asa ta saka, sannan ta ɗaura nik'ab a fuskarta, ta janyo hand bag ɗinta sannan ta fito waje. Driver nanan yana jiranta, ta buɗe sit ɗin baya ta zauna yaja motan sai ALQALAM UNIVERSITY dake cikin garin katsina.

   Kullum shigarta kenan tunda ta fara shiga makarantar, kamar wata matar aure shiya saka har yanzu batayi koda k'awa babu ruwanta da kowah.
      Sai marece sosae ta koma gidan, bata lura da motanshi ba ta saka kanta cikin falon, maganganu ta fara jiyowa.
     "haba Aisha, ba nace karki zomin gida ba? Karki manta fa akwai banbanci tsakanin gidanmu da gidana".
   "akwai banbanci, anma kasan ko inane zan iya zuwa don in ganka, tunda kai ba son zuwa gidanmu kake ba"
     "naji, anma kincemin inzo banzo ba? Ki k'ara hak'uri mana lokaci kaɗan ya rage a fara maganar aurenmu"
    "kullum haka kake cewa, ni dai tunda nazo ka bari ko gaisawa muyi"

Wani abu ne ya tsaya ma majeeda har wuya, kamar ta kama majeeda ta shak'e takeji, a ciki-ciki tayi sallama ta shiga ɗakin duk suka juyo suna kallonta, ta k'urama majeed ido kawai, taa daɗe bata ganshi ba, don tunda ya fara zuwa aiki ya daina zaman gida, girki ma idan taayi a kitchen take bar mishi.
   taa rigashi ɗauke idanunta, ba tare da tace komi ba ta shige ɗakinta.
      Ibraheem ya faɗo mata a rai, yanzu yaa daina kiranta, ko kiranshi tayi sai yaga daman ɗagawa, koya ɗaukama bazasu wani daɗe ba zai kashe wayan, shiyasa itama ta daina damunshi, yanzu hankalinta akan karatun kawai ta maidashi.

   Cikin ɗakinta haushin Aisha ne kawai ya cika mata ciki, daganan tana jiyo maganganunsu tak'i tashi ta tafi duk da maganar da majeed ke mata, tashi tayi ta tafi falon bayan ta cire hijabin jikinta, ta gyara ɗaurin kwallabin sannan ta fito.
    Shiru suka k'arayi suna kallonta, ita kam kamar ma batasan dasu ba, ta k'arasa gaban kallo ta kunna, ta rik'o remote ɗin ta zauna kallo.
      K'asa-k'asa Aisha taci gaba da mishi magana duk hankalinshi na kan majeeda, ta k'ure k'arar ma yanda bazasu ji ba, duk a takure yake anma Aisha taa kasa ganewa, kawai ya juya zai tafi ɗakinshi itama ta mik'e zata bishi.

Majeeda ce tasha gabanta,
       "kinfa fara wuce iyaka malama, don tsabar rashin kunya ki biyo mijina har gidana, kinga ban tanka ba shine zaki bishi har ɗaki, ubanme zaki yo a ciki?"
   "Akan mijin da bai damu dake ba baya sonki kike tada jijiyoyin wuya? Abinda ranki ya baki shi zamu yo"
    "k'arya kike wallahi ki shigo har gidana kina faɗamin magana, banza mai k'wak'war namiji har gidanshi, ai naga mugun son da yake miki ne ya saka sai dai ke ki biyoshi"
    "laaah, ni kike faɗa ma magana? Kana jinta fa majeed"
       
Duk suka maida kallonsu ga majeed ɗin, "Da bakizo gidanta ba taa faɗa miki? Kinga muje in maida ke gida"
       Majeeda tsayawa tayi tana kallonsu har suka fice, lallaima yaa fifita wannan banzar a kaina kenan, har saida ta jiyo ta mata gwalo, haushi kamar ta fasa ihu.
    Lallai don yaga yanzu babu aurenshi a kaina ne harda shigomin da wata a gida, wallahi bazan yarda ba nima sai na rama.

   Bai wani daɗe ba ya dawo, anan ya wuce ta inda ya barta, ya wuceta inda take tsaye yana tafiya da kakkausar murya cikin gargaɗi yace, "babu ruwanki da kowacece zatazo wurina, babu ruwan wani da harkar wani" ya wuceta sannan ya k'arasa maganar.

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 17-18

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                 17-18

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

  Shirun da Ibraheem yaji tayi ya saka ya dinga "hello, masoyiyah, kina jina?"
      "ina jinka masoyi zan kiraka yanzu," sannan ta katse kiran tana k'ok'arin dai dai ta nutsuwarta.
   Ta kalli majeed tana mayar mishi da irin kallon da yake mata "Meya shigo dakai ɓangarena? Ka mantane sharaɗinmu na babu wanda zai shiga harkar wani? Kuma bazaka zo inda nake ba"
     "ke har kina da bakin magana? Baki manta da sharaɗinmu ba meyasa kike k'ok'arin faɗa mishi sirrinmu?"
         "ni ban faɗa mishi ba ko kaaji naa faɗa?"
   "kina shirin faɗa dai, wannan ba k'aramar magana bace da idan kin faɗa ma wani yaɗuwarta bazai kawo matsala ba, har yaushe kike tare da Ibraheem da kika yarda dashi har zaki faɗa mishi wannan sirrin namu? Ke kin kasa rik'e sirrinki ta yaya kike tunanin wani zai rik'e miki? Wallahi karki kuskura ki faɗa ma wani wannan maganar"

   Jikinta yaa riga da yaayi sanyi, taama kasa maida mishi, ya juya ya bar ɗakin, taja tsoki "daman gulmace da sa ido ya shigo dakai kenan" ta harari k'ofan tana murguɗa baki kamar yana ganinta, sannan ta tashi ta shige ɗakinta.

   Yinin ranar bak'i ta dingayi masu zuwa ganin gidan Amarya, kowah yazo sai ya zagaya gidan ana lellek'a ɗakunanta, ba k'aramin haɗuwa da tsaruwa gidan yayi ba, ga dukiyar da iyayenta suka zuba mata a ciki.

  Ba ita ta zauna ba sai 9 na dare bak'inta suka gama tafiya, duk taa gaji ga yunwa bata samu taa girka komai ba, baba haule dai taa koma gida,
     Kwanciyah tayi ta jawo wayarta miss calls ɗin Ibraheem ne babu iyaka, itama ta kirashi bai ɗaga ba, ga yunwar dake yatsina mata y'an hanji, mik'ewa tayi kawai ta nufi kitchen ta ɗaura girki, da yake an haɗa mata komi.

   Fried cous-cous ta dafa dai-dai cikinta, sai k'amshi ne ke tashi, tananan tsaye harya gama dahuwa ta sauke ta jawo plate zata zuba kenan ta juyo wayarta na ringing a ɗaki, ta ajiye da sauri ta tafi ta ɗauka wayar.
   Ibraheem ne, ta zauna gefen gado sannan da ɗaga kiran.
     "Da fatan ma'abociyar kyakkyawan murmushin nan tana cikin nishaɗi"
   "sosai tunda ina tare da muryan masoyinah"
     "kawai ɗazun ina cikin ɗokin jin albishir daga gareki, saiki yankemin waya, halan angonki ne ya kiraki?"
      "shiya shigo dai, anma ai bai isa don ina waya dakai in katse saboda shi ba"
   "Hmm, kin manta da mijinki ne? Kina kulawa dai don baniso muna shiga hak'k'ik aure da yawa" sai can ya tuna kuma.
       "Yauwah aurenki yanzu ma... me kike cewa?" sai da ta ɗan daburce duk taa rasa me zata ce sannan tace "yanzu ne yake k'ara damuna masoyi, anya bazamu gudu muyi aurenmu?"
    "Aure akan aure kenan? Nifa banda matsala da iyayena Masoyiyah jiran fitowarki kawai nake, basai mun gudu ba kinji tawan"
     "tohh" kawai tace mishi a zuciyarta tunani take anya bazata faɗa mishi ba? Kuma sai taji tsoran kashedin da Majeed yayi mata haka kawai ta fasa faɗa mishi.

Majeed yana ɗaki shima babu inda yaje, sallah ce kawai take fiddashi, sai juyi yake akan gadonshi saboda yunwar da yakeji tunda rana, daya juya sai yayi tsaki "Yanzu mutum ya tafi restaurant yana haɗuwa da idon sani akama yi mishi surutun ya fara fita cin abinci"

    Gani yayi zaman bazai mishi ba, ya tafi kitchen ya duba ko zai samu abinci.
    Cikin sa'a kuwa ya hango tukunya saman cooker gas, ita ya fara buɗawa, abinci ya gani kuwa da zafinshi k'amshi sai tashi yake, ya jawo plate ɗin daya gani a wurin ya juyeshi tass sannan ya fito falo ya zauna ya fara ci.

Sai da ta gama wayanta da ibraheem daman yunwa duk taa addabeta, ta fito ta wuce shi a falo ta nufi kitchen ko kallon inda yake batai ba, shima ko sanin taa wuce baiyi ba.

Ta duba inda ta ajiye plate babu, kodai bata ɗauko ba? Ta janyo wani plate ɗin dai ta taho zuba abinci, tana buɗa tukunya wayam babu komi, fiddo idanu tayi waje cikin mamaki ta ɗauka tukunyar tana girgizawa kodai bata gani dai dai bane, anma wayam babu komai.
   Toh waye zai shigo har gidanta ya kwashe mata girki? Kodai aljanu ne, can ta tuna fa ay ba ita kaɗai bane a cikin gidan, toh shi kuma mezai dameshi da girkinta? Tunani dai ta dinga yi taga bazai mata ba, ta fito daga kitchen ɗin can ta hango shi ya saka plate a gaba yana kwasar girki.

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 15-16

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                 15-16

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

Ci gaban labari
    A hankali majeed Yace "miye mafita? Nifa tsakanina da Allah bazan iya zama dake a matsayin mata ba" tace "nima haka wallahi, kuma indai zamu zauna a inuwa ɗaya sai munyi faɗa" yace "hakane ya zama dole musan abunyi" tace "tohh me zamuyi?"

    Yace "mu rabu kawai kowa yayi sabgarshi, tunda kowa ɓangarenshi daban" ta zaro ido "idan fa suka gano?" yace "tohh waye zai faɗa musu? Kinga saima in samar miki admission kici gaba da makarantarki" tace "hakane tohh sakeni"

    Ba wani tunani ko damuwa a fuskarshi Yace "na sakeki saki ɗaya" itama ba da wani abu a ranta ba tace "saki ɗaya ai ana komawa" kafin ta rufe "baki yace "na sakeki saki biyu" tace "ai wallahi saki biyunma ana komawa, ka cikashe kawai" Yace "na sakeki saki uku.

    Wani ihun daɗi ta saki saboda tsananin farin ciki, ta tashi tana tsallen murna, harta tafi ta dawo.
       "Anma babu ruwan kowa da harkar kowa? Babu aurenka a kaina, babu faɗa a tsakaninmu, ko nuna iko da shisshigi" yaja tsoki yana juyar da fuska
      "ke duk wannan ya dama, salon kuma shegen surutunki ya kai ki faɗa ma wani"
     "Anma haka zamu zauna ba tare da kowa ya sani ba?
       "nafa gaji da ganinki wurinnan malama, babu abinda ke tsakanina dake, ki ɓacemun da gani"

Kamar ta maida mishi da bak'a, ta tuna idan tayi hakan faɗa ne zasu ci gaba, ta taɓe baki kawai ta shige ɗakinta, cikin ɗokin ta kira ibraheem ta faɗa mar.
     Kiranshi ta dinga yi anma tak'i shiga har ranta ya soma ɓaci don yanda ta k'agara ta faɗa mishi tasan sai yaa fita murna, cikin haka sai ga kiran hafsatul kiram babbar Aminiyarta kenan.

  "Ran Amarya ya daɗe tare dana angonta"
   "wacece Amarya? Yanzu duk k'wak'warki dai bazaki kirani da wannan sunan ba" inji majeeda.
     Bayan hafsatul kiram tayi dariya tace "Tohh ina angon naki? Na kasa hak'ura ne na kira ki, duk da nasan kunanan tare yana jinya" ta faɗa cikin tsokana don tasan zata k'ular da majeeda.
    "banson iskanci fa hafsa, ina auren yake da har zai samu zuwa kusa dani ma?"
   "saman kanki mana, da aka ɗaura miki jiya".
     "tohh wallahi na saukeshi yanzunnan, karma ki ɓatan rai ina cikin farin ciki?"
     "kamarya majeeda?" ta faɗa da mamaki"

Da yake majeeda ta yarda da hafsatul kiram sosai, kuma tasan duk rintsi bazata taɓa faɗama wani sirrinta ba, kuma tana cikin son ta faɗa ma wani, nan take ta kwashe komai ta faɗa mata.
   Shiru tayi kamar wacce tayi suman zaune sai da majeeda tace "ko kin kashe wayar ne?"
   "kin kashemin bakin magana dai? Yanzu auren naku kuka kashe a washe garin amarcinki? Kuma zaku zauna a gida ɗaya? Haba majeeda kamar dai....."
      "kinga rik'e mamakinki da duk maganganunki, da kuma sirrina, kinsan don na yarda dake ne na faɗa miki ko? Babu wani abin dana sanin insha Allah"
   "Allah ya yarda, anma duk kin sakemin jiki"
   "tohh a warware lafiya, ki gaishe da Ya umar" bata jira me zata ce ba ta kashe wayar.

  Layin ibraheem taci gaba da neman, sai sintiri take a tsakar ɗakinta, can taji taa fara ringing, ta samu kujera ta zauna tana jiran ya ɗaga anma har ta katse shiru.
    Sai da ta mishi kira biyu ana ukun ne ya ɗaga da alama barci ya tashi.

   "na kwanta barci da tunaninki, banyi mafarkin komai ba bayanki, gashi na farka da zazzak'ar muryarki, plz in fara jin sautin lallausan murmushin masoyiyah ta" sai da ta mishi murmushin sabo da yanda kalamanshi suka mata daɗi tace, "ba murmushi na kaɗai zaka farka dashi ba, harda Albishir ɗin da zaiyi maka daɗi sosai"
  "faɗamin da sauri masoyiyah, tunda kafin ki faɗa ga tukuicinki" ya sakar mata daddaɗan kiss a kunne

Ta rufe ido ta buɗe cikin nishaɗi, "Yaimin daɗi sosae masoyi, karfa ka sakani mantawa da albishir ɗin"
     "sai in k'ara miki wanda zai saka ki tuna"
  "banma manta bafa, anma duk da haka naa biyoka bashi, yanzu miye yayi mana katanga da zama mallakin juna?"
     "Auren ki da majeed mana" inji ibraheem
    "tohh k'ara kwantar da hankalinka, don indai aurena ne yanzu....."

Maganar ta mak'ale mata saboda ganinshi tsaye a k'ofar falonta, yana wurgo mata wani mugun kallo

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 13-14

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                  13-14

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

    Batayi wani barcin kirki ba saboda yanda ta k'agara gari ya waye, ga uban kukan da tasha da safe duk idanunta sun kunbura. Gari na gama haske ta shirya wurin 11 tace ma Momie taa tafi gidan Aunty Zainab, da yake tasan matsalanta da damuwanta kuma bata da wani abokin shawara kamar Aunty Zainab ɗin shiyasa momie bata hanata taje ta kwantar mata da hankali ba.

   Napep ta tara ya kaita gidan Aunty Zainab, tana sauka daga napep ɗin yana fitowa da motarshi daga gidan, ta juyar da kanta gefe kamar bata ganshi ba, yayo kanta da mota kuwa har ya kusan take mata k'afa sannan ya fito daga motar.
     Yana nunata da ɗan yatsa yace "ina fatan kinsan abinda ke faruwa, kuma baki amince musu ba" sai data gatsina sannan tace "kaima kasani ai bazan taɓa amince da auran ka ba"
        "Yaa miki kyau, don wallahi aka aura min ke gutsun-gutsun ina iya miki in jefar dake, don ko kaɗan baki cikin kalar matan da nake so"
       Tsoki kawai taja ta juya ta tafi don batason tsayawa magana dashi ma, wata tsanar shi ce ke k'ara zo mata ta shige gidan Aunty Zainab kawai.

Tun daga ranar kullum cikin damuwa suke, babu wanda bai kwanta rashin lafiya a cikinsu ba, k'iyayya sosai suke nuna ma junansu, anma iyayensu sukai watsi dasu sai dai hidimar biki kawai suke.
     Duk yanda suka so a fasa auren sai da aka ɗaura shi su duka babu mai so, a tunaninsu iyayen idan akayi auren daga baya zasu warware ne suci gaba da son junansu, basu sanda babban kuskure ne suka tafka ba (inji rash kardam).

A gurguje dai😜

Mu koma labari....

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 11-12

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                    11-12

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

    Sai dare Driver yazo ɗaukanta, Zahra ta rakota har wurin motar. Zata shiga kenan idonta ya hango mata Majeed babu nisa da inda take, shida wata yarinya da alama zance suke, aikam dariya ta fara harda rik'e ciki. Zahra ta fara dudduba jikinta tasan halin Majeeda da dariyan mugunta tace "wai meya baki dariya haka?" ta buɗa baki zata yi magana ta k'ara kwashewa da dariya. Zahra tace "wai miye haka?" ta soma k'ulewa, shima Majeed yana jiyota hankalinshi duk ya dawo kanta sai aika mata da harara yake ta cikin duhun, dak'yar tana rik'e cikinta tace "Abin da ya bani mamaki na gani, wai mace da zuwa wurin namiji zance".

    Zahra ta sassauta murya tace "don Allah ki daina mana, kin san dai halin Yayanmu yanzu ya taso kuyi tayi, itama budurwarnan tashi ce da shegiyar k'wak'wa".
   Tun kafin ta gama magana Majeeda tace "barni in faɗa wallahi, an daiji kunya mace  da zuwa zance wurin namiji, ko meye ma abun so anan?"
    Cikin faɗa ya taso inda take kamar zai shige mata, zahra harta ɓalla da gudu cikin gida, itama shigewarta tayi cikin mota da sauri kafin ya ida isowa tace ma Driver ya tada su tafi. Sannan ta lek'o da kanta da k'arfi tace "kayi kai kaɗai, da wannan marar aikinyin da take biyoka har gida, wlhy k'arama tun wuri ki canja masoyi wannan ba abinso bane" sannan suka wuce nan suka barshi yana cizon yatsa data gama gaggaya mishi maganganu kuma bai mata komi ba.

    Har dare idan ta tuna ita kaɗai sai ta dinga daria, koda suna chatn da Ibraheem sai da Yace mata "wai ya na ganki yau kina cikin farin ciki?" Tace "Ay kullum ma cikin farin ciki nake da annashuwa indai ina tare dakai"
Yace "Hakane Masoyiyatah, anma da alama farin cikin naki na yau yaafi na kullum" tace "hakane fa, wlhy wani abune ya bani daria, anma dai bazaka tambayeni ko miye ba?"
      "ko ban tambayeki ba nasan zaki faɗamin ba?😉
    "hakane Masoyi, anma ka share kawai"
    "na share Masoyiyah, bani labari"
     "ba labari sai dai na zuciyatah"
     "shi nafiso masoyiyah, bani labarin soyayyatah a cikin zuciyarki"

    Anan suka bar maganar, suka ci gaba da firarsu kawai, anma idanta tuna abinda taima Majeed sai ta dinga dariya ita kaɗai, kafin shima ya tashi ramawa.

***
   Sun gama fira da Ibraheem yayan k'awarta kuma saurayinta, fito ta rakashi har gaban mota suna fira kamar karsu rabu.
   Daddy ne ya shigo ya kallesu Majeeda sai k'yalk'yala daria take, tana ganin haka tayi saurin shanye dariyarta ta dai-daita nutsuwarta, ibraheem ya fita har inda daddy yake ya duk'a ya gaisheshi, sama-sama ya amsa sannan ya wuce cikin gida.
    A sanyaye Ibraheem ya koma wurin motarshi ya shiga, ta rik'e k'ofar motar duk taa marairaice fuska ganin canjawar yanayinshi.

    Sai ga motar Majeed taa shigo gidan, ta ɗaga kai kawai sannan ta maida hankalinta wurin Ibraheem.
    Zuwa yayi har inda suke sannan yayi parking motar ya fito, zai wuce Ibraheem ya mik'a mishi hannu suka gaisa sannan yayi gaba yana cewa...
   "yau naaga nacin zance, saurayi na zaune saman seat ɗin mota don tsabar baiji da mace zai barta tsaye tana shan gajia" ya wucewarshi kawai.
   Tasan da ita yake, kawai dai bata son ta tanka mishi a gaban Ibraheem ne ya sakata sharewa, ba daɗewa ta sallami Ibraheem sannan ta shige gidan, ɗakinta kawai ta wuce donma karsu k'ara haɗuwa, bata sanma sanda yabar gidan ba.
   Da safe taje gaishe da Daddynta, harta taso zata tafi ya tsaida ita, ta koma ta zauna kanta a k'asa gabanta naa faɗuwa.
   "ɗazu wanne yaro ne yazo gidannan?" sai da ta ɗanyi shiru sannan tace "Yayan k'awata ne Daddy"
    "Yayan k'awarki kuma meya kawoshi gidannan?" shiru ta k'arayi har saida ya k'ara maimaita tambayarshi sannan tace "ba komi fa Daddy".
   Yace "ina fatan hakanne, domin kuwa naa riga dana miki miji" da sauri ta ɗago da fuskarta "miji kuma Daddy?"
    "k'warai ma kuwa, idan ma bakisan ko wanene ba yanzu zaki sani, domin kuwa tun kina k'aramarki mukayi ma Mahaifinmu Alk'awarin haɗaku aure da Majeed"

   Wani irin zabura tayi "Majeed dai Abba? Ni wallahi bazan aureshi ba, na rantse bani sonshi" yace "tohh naji baki sonshi, tashi ficemin daganan, maganar aure tsakaninku dai babu fashi" nan ta k'ara fasa wani kukan, ta tashi ta nufi ɗakinta har tana tuntuɓe a hanya faɗi take ita wallahi bazata taɓa aure Majeed ba.

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 9-10

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                    9-10

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

Haka rayuwah taci gaba da tafiya, babu jituwa sam tsakanin majeed da majeeda, tana da shekara 6 ko wucewa zatayi sai majeed ya saka mata 'kafa taa faɗi, gata da masifa ita ma ta ɗago suyi tayi dak'yar iyayensu suke rabasu.

Cikin haka kaka ya kwanta ciwon ajali, ya tara 'ya'yan nashi duka ya fara musu wasiyya sannan yace "na sanku da zumunci, da kuma son zumunci, ku k'ara rik'e junanku ko bayan raina, a duk lokacin da naga khadija da Abdul majeed sai wani abu ya zomin a raina, ji nake kamar nine da mahaifiyarku, naso ina da rai inga ranar aurensu, anma kumin al'kawari ko bayan rai na zakuyi musu aure"

Alhaji Sani Yace "Insha Allahu kaka bazaka mutu bama sai kaga auren nasu"
    Kaka Yace "inaa Sani, kai dai kawai ku rik'e alk'awari, don ciwonnan nawa jikina yana bani bana tashi bane, ko bayan raina ban yafe ma duk wanda ya saɓa wannan alk'awarin ba a cikinku, majeeda itace matar majeed" tare suka haɗa baki "Insha Allah baba"

Maganar daya faɗa k'arshe kenan, sai dai yayi kalmatus shahada, rai yayi halinsa.
    Sunji mutuwar mahaifinsu sosai, sunyi kuka, tare da k'ara jaddada maganarshi ta k'arshe suna k'ara ɗaukarta da muhimmanci.

Sai dai wani Abu, majeeda da majeed suna girma suna k'ara rashin jituwa a tsakaninsu, tun suna ɗaukar abun nasu yarinta ce, har sunkai lokacin da majeeda ta gama secondry school, majeed ma ya gama makarantarshi har ya fara aiki, Aunty zainab kuma anyi mata aure da shekara ɗaya.

Yau gidansu majeed ta shirya ta tafi, zahra nata yi mata tsegumin bata son zumunci sai dai ita tazo, yau dai ta shirya driver ya tafi kaita.

Tayi sallama falon ta shiga, babu kowa, saita wuce ɗakin umma ta gaisheta sannan ta fito ta nufi ɗakin da zahra take.

Hangota tayi ta k'urama t.v kallo da alama a tsorace take, lallab'awa tayi har inda take ko sanin taa shigo ma batayi ba, sannan ta k'wala k'ara saitin kunnanta.

Aikam ta mik'e a firgece daman duk a tsorace take, ko tsayawa kallon majeeda batayi ba ta zunduma waje a guje tama rasa inda zata nufa, itama majeeda tabi bayanta da gudu tana mata dariya sai so take ta rik'ota, anma ina tama k'i tsayawa wuri ɗaya sai dai taji tayi karo da mutum.

Da sauri taja da baya zuciyarta cike da fargaba ta ɗago idonta taga ko waye, suka haɗa ido da majeed yana mata wani irin mugun kallo.

Ganin shine itama taja tsoki kawai ta nufi wurin zahra da tayi tsuru-tsuru tana kallon majeed, tace "muje matsoraciya, kinsan bazaki iya ba kika saka film ɗin horror ke kaɗai a ɗaki kina kalla"

Tace "Tohh yana iya tunda ina son kallo? Film ɗinne yayi kyau" har lokacin zahra satar kallon majeed take daya kasa motsawa daga inda yake har lokacin.

Ya daka musu wata uwar tsawa "baku da ido ne da zaku bugi mutum da wasan banzanku na k'ananan yara kuma bazaku bashi hak'uri ba?" zahra tace "kayi hak'uri yaya" tana zungurar majeeda itama ta bashi hak'uri.

Majeeda tace "hak'urin me kike bashi? Shine fa ya shigo ta hanyarmu" ta murguɗa baki sannan ta juya taci gaba da tafiyarta.

Yace "lallai ma yarinyar nan, yauma rashin kunyar zakimun?" waiwayen ɗakin ta kamayi sannan ta ɗago idonta itama ta watsa mishi wani irin kallo sannan tace "babu yarinya anan"
         "idan nazo na murɗe wannan shegen masifaffen bakin naki kyamun bayani"

Tace "zan zauna ne kamar sakara ka murɗemin baki? Kaima kasan ba tsoranka nake ba wallahi".

Nan fa faɗa ya kaure, majeed ya kasa wucewa ɗakinshi saboda yanda majeeda ke gasa mishi maganganun, ranshi yayi matuk'ar ɓaci shiyasa yarinyar ko ganinta bai sonyi, masifaffiya ce kuma tayi matuk'ar rainashi.

A zafafe ya nufeta da niyyar kai mata mazga, dai-dai lokacin umma ta fito jin hayaniya, majeeda na tsaye inda take ko gezau ba tayi ba

Umma tace "Aaaaah, majeed mezan gani haka? Abin naku ya wuce faɗa a baki har duka zaka kai mata?" cikin jin zafi yace "Umma zan tsaya k'aramar yarinya kamar wannan ina faɗa tana faɗa ne? Ai wallahi sai ta gane ni ba sa'anta bane".

Tace "ai sai dai in baka faɗa ba wallahi, donni bazan tsaya kana nunamin iko ba"
  Umma tace "tohh kuci gaba kunji ko? Tunda a gabana ma bazaku bari ba, kana babba anma bazaka daina shiga harkar k'annan ka ba, zo ka wuce ɗakinka" tana nuna ma majeed hanyar ɗakinshi.

Ya wuce yana aika ma majeeda da harara, itama harararshi take harya wuce ɓangarenshi, sannan taja hannun zahra suka wuce ɗakinta.

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 7-8

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                    7-8

©Rabiatu sk msh
         ®NWA

Labari...
        Ilileee

WANI LOKACI KAFIN AURANSU...
Alhaji Sani da Alhaji salisu, y'an uwane dake matu'kar son junansu da son zumunci, kaka Abdul hameed shine mahaifinsu mahaifiyarsu khadija taa rasu da daɗewa, shi kaɗai ya rage musu shiyasa suke matu'kar ji dashi.

Alhaji sani wanda suke kira da Abba, kuma mijin Umma, yana da yara biyu, Abdul majeed wanda aka saka ma sunan kaka, da kuma 'kanwarshi zahra.

Sai Alhaji saleesu shima Yara biyu ne dashi duk mata, Aunty zainabu wacce ta girme musu su duka, da Autah khadeeja (majeeda) itama sunan kakarta ne da shiyasa ake ce mata majeeda.

Tun haihuwar majeed, kaka yake matu'kar ji dashi saboda sunanshi da aka saka mishi ga yaron shiru-shiru da saurin shiga rai, babu ruwanshi da hayaniya sai dai baison raini, kusan kullum suna gidan kaka shida Aunty zainabu da ta girme mishi da shekara 3.

Aunty zainabu nada Shekara 10, majeed nada shekara 7, k'anwarshi fatima zahra tana da 2years, aka haifi majeeda, iyayensu sunyi matu'kar murna sosae, bama kamar da tun bayan haihuwar zainabu basu k'ara samun haihuwa ba sai akan majeeda.

Ranar sunah aka saka ma jaririya suna khadija, anma za'ana kiranta da majeeda, kaka yaji daɗi sosai kasancewar sunan matarshi ne aka saka mata, tun a ranar ya k'udurta wani abu a ranshi, tsakanin takwaranshi majeed, ta takwarar matarshi majeeda.

****
Aunty zainab ce ta fito da shirin fita, taci kwalliya da goyon majeeda a bayanta, ta samu momie zaune ɗakinta tana kallo.

Tace "momie zamu tafi" momie tace "tohm a dawo lafiya, a gaida kaka Alhaji" zainab tace "zaiji momie" sannan ta fito har driver ya fito da mota, ta shiga sannan ta kwance goyon majeeda ta rungumeta ya tada mota sai gidan kaka.

Tana shiga da sallamarta, Abdul majeed dake zaune kusa da kaka ya amsa mata yana "oyoyo Aunty zainab" kaka daya cika baki da dambun naman da ƴaƴanshi suka kawo mishi Yace "Allah yasa da matata kikazo mun zainabu" tace "ni baka ma son ganina kenan sai wannan tsohuwar matar taka?" kaka Yace "Ai kinsan dolene naji da deeje, kedai kwantota ki mik'omin itanan mu gaisa" ta mik'a mishi ita majeed duk ya haɗe rai.

Tana hannun kaka sai mutsilniya take irinna jarirai tana ture majeed ta k'afarta, haushi ya kamashi ya rik'o k'afafunnata ya ri'ke, kaka ya lura dashi tun haihuwar majeeda ba wani son ganinta yake kusa dashi ba .
       "majeedar zaka ɗauka ne?" saurin girgiza kai yayi.
   Kaka Yace "haba takwarah na, ina lura dakai fa tun haihuwar ɗiyarnan ba son zuwa kusa da ita kake ba"
Majeed ya k'ara ɓata rai Yace "Ay nifa babu ruwana da ita kaka, tun haihuwarta ka daina ji dani da taazo sai dai kayita ɗaukanta, ko gidansu mukaje da ummana sai tayita ɗaukanta"
  Kaka Yace "kai bakaso ana ɗaukar matar taka ne?" da sauri yace "ni ba matata bace, bani sonta" shiru kaka yayi bai k'ara cewa komi ba.

Kiran sallahn da akayi ne ya saka zainab ta fita ɗauro Alwala, kaka ya mi'ka ma majeed ita yace "ri'keta tohm inyi sallah" kamar bazai amsheta ba, sai da kakanma ya kwantar mishi da ita sannan ya fita alwala.

Kaka na tsakar yin alwala, zainab na shirin shiga ɗakin suka jiyo majeeda ta k'wala wani uban kuka, da gudu zainab ta k'arasa shiga ɗakin ta iske bakin majeed dai-dai k'afarta ya gartsa mata ciwo da sauri ya ɗago.

Ta tsaya tana kallonshi "meka mata majeed?" ya fara kame-kame "wallahi Aunty zainab babu abinda na mata, ita keta kukanta tana halbina da k'afafunta" tace "tohh ka ɗauketa ka rarrasheta mana" badon yaso ba, ya ɗaga ta sama duk da ba wani k'warewa yayi da ɗaukan ba, aykam saitin bakinshi ta dalalo mishi tumbuɗi.

Baisan sanda ya saketa ba saida ta kusan faɗowa zainab ta ri'kota ya fita da gudu yana kakarin amai, sai da suka nutsu suka dinga mishi daria.

Haka rayuwar majeeda da majeed take tun suna k'anana, tun lokacin data fara tafiya data samo abun ɓarna saita nufeshi ta k'wala mishi, shima haka indai daga shi sai ita ne ya dinga mintsininta kenan, kwata-kwata basu zama wuri ɗaya.

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 5-6

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                    5-6

©Rabiatu sk msh
        ®NWA

©Rabiatu sk msh
        ®NWA

Washe gari tunda safe baba haule tana gama haɗa musu break fast ko tsayawa karyawa batayi ba ta fita ta tari napep sai gidansu Abdul majeed.

Har lokacin 'yan biki basu gama tafiya ba anata hada-hadar haɗa musu break, baba haule ta raɓa ta gaishe su sannan ta wuce ɗakin Umman Majeed.

Tana falon d'akinta tana waya cike da kwanciyar hankali da alama mai wayan tana tayata murnar bikinne, sai data gama wayar cikin fara'a suka gaisa da baba laure.

Umma tace "Anma dai baba haule lafiya da sassafennan" kanta a 'kasa tace "Rashinta ne ya tado dani tunda sassafennan, don jiya bamu yi barci da kwanciyar hankali ba" Umma ta 'kara sassauta murya cikin tashin hankali tace "meya faru baba haule?" gyara zama tayi ta faɗa mata duk abinda ya faru.

Ran Umma ya ɓaci sosai ta fara faɗa "lallai yarannan anyi mararsa mutunci, mu zasu bama kunya? Ana tunanin in anyi auren zasu daina faɗa anma suyi biris da maganarmu! Bari inje in samu Alhaji in faɗa mishi"

Baba haule tace "tohh shikenan hajia ni daman gani nake tun wuri gara a raba auren nasu tunda basu so, kar wata rana a wayi gari sun kashe kawunansu ma"
    Umma tace "su kashe kansu mana, ya fiye mana dai da ace su ba 'kananan yara ba sun sanyamu karya Alk'awari" baba haule tace "tohh Allah dai ya kyauta".

Koda Umma ta jema Abba da maganar shima faɗa ya dingayi, ya ciro wayarshi ya kira 'kanenshi mahaifin majeeda ya sanar mishi, shima faɗa ya dinga yi suka ce su haɗu gidan, bazasu yarda yara su maidasu k'ananan mutane ba harsu tada Alk'awarin mahaifinsu.

Majeeda ta fito daga wanka, tana shafa mai ta jiyo k'arar motoci, da sauri ta zura doguwar riga ta fito daga bangarenta jin kamar maganar mahaifanta.

Hangosu tayi kuwa kowannensu fuskarshi babu walwala, gabanta ya faɗi tabbas akwai matsala, a sanyaye ta fito daga ɗakinta kamar marar gaskia, ta samu wuri ta rakuɓe tana gaishesu.

Umma kawai ta amsa mata, sai ga majeed ya fito da shirin fita, shima saida gabanshi ya faɗi ganinsu su duka a falon, a sanyaye kamar ita shima ya koma gefe ya zauna 'kasa, shi baima samu kowa ya amsa mishi gaisuwan ba.

Shiru ɗakin yayi na 'yan mintuna sannan Abba Yace "sannunku kunji, sannunku da abinda kuka aikata" duk suka k'ara sunnar da kawunansu kamar mararsa gaskiya.

Abba Yace "Tohh wlhy ku buɗe kunnuwanku kuji, ku baki isa ku maidamu k'ananan yara ba, mune nan mu muka haifeku, Alk'awari muka ɗaukar ma mahaifinmu kuma akanku bazamu karyashi ba wallahi"
   Daddyn majeeda Yace "in banda shirme da shiririta irin nasu ai idan ana shiga kabari a fito tohh za'a aurennan a kwance"
      Abba Yace "bawai kunga daman muna ɗaga muku k'afa ba, tohh wallahi kuka kuskura kuka raba aurennan sai dai ku nemi wasu iyayen badai mu ba" duk suka ɗago a tare suna kallon Abba.
      Daddy Yace "wallahi nima ba a gidana ba, kuma zan tsine miki ne duk ranar da kika k'ara faɗa da mijinki"

Umma tace "ita kaɗaice mai laifin? Baza'a ɗaurama ɗiyata laifi ba a barshi ga k'wareta, nima kau ina shirin tsine mishi duk ranar daya k'ara dukanta"

Gaba ɗaya komi ya kwance musu, sauraren iyayensu kawai suke har suka gama faɗansu suka tafi babu mai wani kuzarin magana duk sun kasa motsawa daga inda suke, har iyayen nasu suka tafi.

Sunfi rabin awa babu wanda ya motsa daga inda yake, babu wanda ya cema kowa wani abu, duk wani kuzarin dake jikinsu ya saki.

A hankali majeed Yace "miye mafita? Nifa tsakanina da Allah bazan iya zama dake a matsayin mata ba" tace "nima haka wallahi, kuma indai zamu zauna a inuwa ɗaya sai munyi faɗa" yace "hakane ya zama dole musan abunyi" tace "tohh me zamuyi?"

Yace "mu rabu kawai kowa yayi sabgarshi, tunda kowa ɓangarenshi daban" ta zaro ido "idan fa suka gano?" yace "tohh waye zai faɗa musu? Kinga saima in samar miki admission kici gaba da makarantarki" tace "hakane tohh sakeni"

Ba wani tunani ko damuwa a fuskarshi Yace "na sakeki saki ɗaya" itama ba da wani abu a ranta ba tace "saki ɗaya ai ana komawa" kafin ta rufe "baki yace "na sakeki saki biyu" tace "ai wallahi saki biyunma ana komawa, ka cikashe kawai" Yace "na sakeki saki uku.

Nikam mamaki ne ya kamani da wannan ɗanyen hukunci da suka yanke a tsakaninsu, anya kuwa zaman nasu zai yiwu a haka?

Kafinnan waye Abdul majeed? Wacece majeeda? Menene tarihin auren nasu? Idan kuka biyoni a sannu zan warware muku🚶🏻‍♀🚶🏻‍♀

©Rabiatu sk msh

HARAMTACCEN ZAMA 3-4

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
    ♠♠♠♠♠♠♠
                 3-4

©Rabiatu sk msh
          ®NWA

Labari...
        Ilileee

Ta ɗago fuskarta tana kallonshi cikin mamaki da takaici "Yanzu Yaya majeed nice zaka ɗaga hannunka ka mara? Wlhy da kayi kuskuren da zaka daɗe kana dana saninshi" Yace "kuskuren me zanyi?" yana matsowa inda take "ke kin isa inyi dana sani don na mareki? Sai in dakeki na daki banza?" tace "mu daki juna dai, don na rantse banyi kama da macen da zata tsaya namiji ya dake ta ba" kafin ta rufe baki kau ya kai mata mari har saida ta du'ke, ta kai hannu tana taɓa kuncinta da take tunanin ko yaa zurma ciki.

Sosai taji marin da'kyar ta iya daurewa ta ɗago, bata tsaya wani tunani ba itama ta ɗaukeshi da zazzafan mari, shima yayi tangal tangal zai faɗi, sannan ya ɗago kallonta kawai yake yama rasa da bakin da zai mata magana.

Itama tsayawa tayi tana kallonshi sai huci take cikin shirin duk yanda ta kama, har lokacin dafe take da gefen fuskarta yana mata raɗaɗin zafi, baice mata komi ba kamar yanda ta zata, sai dai ya fara dube-dube can ya hango incense burning ɗinta, ya janyoshi ya fuzge wayarshi ya nufo ta gadan-gadan.

Batasan sanda ta runtuma waje da gudu ba, tana waige-waige can cikin sa'a itama ta hango wayar chargern 'yan kawo Amarya ta ciro ta tsaya tana jiran isowarshi, kamar wani zaki ya tafo ya ɗaga wayar wuta itama ta ɗaga ya murɗe hannunta sannan ya tsula mata, ta ri'ke wurin ta fara murzawa.

Ya ɗaga ya 'kara zuba mata wata a tsakiyar baya, taji zafinta sosae ta saki ihu, baba haule mai aikinda aka kawo musu ta jiyo da gudu ta fito inda suke tana sallallami.

Ganin majeed ya juya wurin baba haule ya saka majeeda ɗaga tata wayar ta zabga mishi, ya juya yana kallonta idonshi jajir da ɓacin rai baba haule tace "miye haka majeeda shi ga bari ke bazaki bari ba?" tace "ai wallahi baba haule bazai shani a banza ba biyu fa yaimun".

Tace "yau naga abinda ya girmi kakannina ni haulatu tunda nake, wlhy ko a labari ban taɓajin amarya da angon dake faɗa ba ranar aurensu"

Yace "Allah ya sauwa'kemun da amarya da wannan baba haule kima daina faɗa"
      "haba yarannan, aurennan fa an riga da an ɗaura, ku sanya ma zuciyoyinku ruwan sanyi mana"
       Majeeda tace "Ai wallahi badai a aurena da majeed ba, ai nasha faɗa bani sonshi ya nace sai da aka aura mishi"
    Ya taso mata cikin faɗa "toh uban waye yace yana sonki? Ke kinsan na wuce da aurenki wallahi" tace "oho dai kuma saina rama ɗayan bulala na don komai zakai dai-dai nake dakai," tana kaiwa nan ba shiri ta tsula mishi bulala.

Ko gezau baiyi ba, saima ya sha'kota fuskarshi tattare da ɓacin rai tana ta kiciniyar k'wacewa anma ya ri'kota gam, ta fara kai mishi bugu yana kaucewa yana 'ko'karin ri'ke hannuwanta.

Wata sabuwar rigimar ce ta 'kara kaurewa, da baba haule taga bazata iya rabawa ba ta fita da gudu tana 'kwala ma mai gadinsu kira.

Shima hayaniyarsu taa hanashi barci ya taso da sauri yabi bayan baba haule suka shiga gidan shima mamaki fal cikin zuciyarshi, da'kyar suka 'kwace majeeda a hannun majeed, baba haule ta shige ɗaki da ita har lokacin bakinsu baiyi shiru ba suna aika ma juna ba'kaken maganganu.

Shima ta lallab'ashi ya tafi ɗakinshi, sai huci yake irinna sadaukan mazannan.

Kowanne da ɓacin rai tare dajin haushin ɗan uwanshi ya kwanta, don barci yana ɓarawo ne kawai ya sacesu, anma kowanne zuciyarshi kamar zata fasa 'kirji ta fito

©Rabiatu sk msh

Popular Posts

 
]]>All content on thisblog are copyright protected and cannot be reproduced on other websites without permission.