New Post

ABUBUWA BAKWAI (7) ABIN KULA GA DAN'ADAM

1. Duniyar da za a barta, me ya kawo hadama? 2. Dukiyar da za a lissafa daya bayan daya, me ya kawo tarata? 3. Rayuwar da zata kare, ina wani farin ciki? 4. Yarintar da tsufa zai zo mzta, me ya kawo takama? 5. Ana sauraren mutuwa, ina wata walwala? 6. Jikin da zai zama gawa, me ya jawo dagawa? 7. Karshe dai makomarsa kabari, me zai sa alfahari? Wanda ya manta da wadannan a ina ya bar hankalinsa? Allah yasa mu dace, yayi mana kyakkaywan karshe. Ameen!

KADA KA RAMA CUTA GA WANDA YA CUCEKA!

Kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka, kai kayi hakuri. Zaka samu abu biyu sakamakon hakan; * Na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. * Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

KADA KA BARI ZUCIYARKA TA ZALUNCEKA!

Kada ka sale zuciyarka ta zalunceka, tabbas zaluncin zuciya ga gangar jiki yake komawa, idan akayi wasa ya zamanto ya shafi rayuwa. Assasa bak'in tunani, yawan zargi da rashin tabbas akan wani aiki, zato, shakku ko kokwanto akan wani al'amari batare da tantance gaskiyarsa ba, shine zaluncinzuciya akan dan Adam. Maza ka hana zuciyarka don akwai hadurra dubu akan hakan.

MAHAKURCI MAWADACI

Tabbas ba kowane dandanon magani ne ke da dadi ba, amma babu shakka shine abu mafi dacewa ga dukkan mara lafiya. A lokuta da dama rayuwa takan dakeka da guduma ta jefaka acikin wani mawuyacin hali, kayi ta fama amma tayi maka tutsu. Amma idan kayi hakuri sannu ahankali zata kwaranye. Hakika ba duk abinda rai yake so yakan samu ba, amma bukata bata taba sauyawa ba kuma bata taba karewa ba. Don haka ka shirya bukatunka da kyau ka bisu daya bayan daya sannu a hankali, kayi gwa- gwarmaya, sannan kayi juriya. Tabbas mafarkinka zai zama gaskiya.

KO KA SAN?

Rayuwa bakin alqalami ce tana bukatar kaifi sannan tana son tsini. Kaifin don ka yanki magauta, tsinin kuwa don ka soki makiya. Haka zalika rayuwa kamar randar ruwan sanyi ce ta kasa tana bukatar tanaji da adani, kodn wata rana ka shayar da masoyanka. Da kyau ka lura da abu biyu a rayuwa; 1. Ka lura da mai zaginka mai aibantaka wata kila wata rana zai iya zama masoyinka mai yabonka 2. Ka lura da masoyinka na kusa mai yawan ambaton alkhairinka, wata kila wata rana zai iya zama makiyinka mai zaginka.

Sunday, 27 November 2016

HAKA SO YAKE 47-48

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_47 - 48_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

_WASHE GARI_

*BIRNI*

Da maraice Abba da momie na zaune yana K'ara lallashin ta, saboda duk ta damu da tafiyar subeey, kowa na gidan yana kewar tafiyar subeey dadinma kanshi yana cikin damuwa. Gida yakoma tsit saikace gidan makoki, Abdul tun safe yafita yabar gidn domin bayajin dad'in zama gidan idan ba subeey,

Sallamar da akayi a waje shine ya sanya daddy tashi ya fita, motoci yatar a harabar gidansa birjin,  tunda ga nesa yake yima mutanen kallon rashin sani, sai dai ya saki fuska suka gaisa.

Wani daga cikinsu ne Yace "mune iyayen Ahmad, mai neman Yarinyar wajensu subeey," Abba yayi shiru cikin jimami ya tuna da momie tayi mishi maganar Ahmad ɗin, fuskarshi cike da jimami Yace "Tabbas hajia taimun bayani a kan zuwanku, anma k'urewar lokaci ya sanya bamu muku bayani ba"

Cike da rashin fahimta kawun Ahmed Yace "Kamarya Alhaji da wata matsala ne?"

Abba Yace "tohh maganar gaskia itace jiya mahaifin suwaiba yazo ya tafi da ita k'auye a can yayi mata miji, sai dai hak'uri"

Kawun ahmed yace "tohm shikenan Alhaji" jikinsu a sanyaye sukayi mishi sallama sukaja motocinsu suka bar gida,

Ahmad nazaune a falo shida ummansa suna jiran dawowar kawunsa, kawai sai ganinsu yayi cike dadamuwa, nan suka gaya masa labarin cewa subeey takoma kauye,
hauka kaɗaine baiyi ba, ya dinga kuka kamar k'aramin yaro Umminshi na lallashinshi, daƙk'yar ta lallasheshi ta hanashi tafiya k'auyen don cewa yayi sai yaje can ya dawo da subeeynshi,

*KAUYE...*

A ranar Alhajin birni yaje wurin subeey, hauwa sai k'ara shisshige mata take, malam habu da kanshi ya rakata inda Alhajin birni yake, an shimfiɗa mishi sabuwar tabarma, ta koma gefe ta tsuguna ta gaisheshi tana satar kallonshi.

Don kyau kam ba laifi yana dashi, Amma girman nashi har yayi yawa ga jinkai da nuna isa a lallai shi mai kuɗi ne.

Basu yi wani fira sosae ba yace ta tashi ta shiga ta turo mishi malam habu, ta mik'e ta shiga cikin gidan ta faɗa ma mahaifin nata saqon Alhajin birni.

Via OHW📚📲

HAKA SO YAKE 45-46

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_45 - 46_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Abba yayi saurin shiga tsakaninsu yana  cewa "A'ah hajia baza'ayi haka ba, shine mahaifinta ya fimu iko da ita, dan haka tun yabukaci 'yarshi kibasa abinsa"

Momie duk hankalinta yatashi jin abba yashigarwa malam habu, bakaramin abu zai iya rabata da subeey ba, da sauri  tace "amma nima ina da iko da ita, domin nima 'yatace"

Malam habu yaga momie batada niyar bashi subeey, cikin zafin rai Yace " gaskiya yaya komi zai faru fa yau bazan bar gidannan ba saida ƴ'yata, dan haka subeey tashi kije kid'auki kayanki mutafi" yafad'a yana kallon subeey,
  Ba musu subeey ta mike har jikinta yasoma rawa saboda tsabar kukan datake,
Momie tayi saurin mikewa tsaye ta rikota cike da bacin rai tace "ba inda zataje, ke koma kizauna" tafad'a tana mayar da Subeey zaune,
Shima malam habu ya mike ransa a bace yace "dakinsan halin danake ciki da bazaki hanani zuwa da subeey ba kumani danasan hakan abin zai kasance daga karshe dabanzan bayar da 'yataba, dan haka nidai kawai kibani suwaiba"  nan dai rigima sosae suke akan subeey, tana gefe sai kuka take cikin tashin hankali, Abdul  ma damuwah ce bayyane a fuskarshi, kasa jurewa yayi dasauri yatashi yawuce d'akinsa,

Daƙk'yar Abba yasamu y lallaɓa momie ta amince ta bar subeey ta koma ƙk'auye ba don taso ba, itama ƙk'arfin hali ne kawai ya hanata kuka don ta shak'u da subeey sosae tanajinta kamar ƴ'yar data haifa, malam habu Yace taje ta haɗo kayanta.

Babu musu ta musu ta nufi ɗakinta,

Bayan abdul yashiga d'akinsa hawayen nadama ne da kuma tausayin subeey suka fara zubo mishi, yaf'ada kan gado yana kuka, zuciyarsa tana masa kuna sosai,

Subeey kuwa Cusa kayan kawai tayi cikin jikka da duk abinda zata buk'ata, sannan ta fito tana kuka suka sallama da momie da Abba. Anan kam momie kasa jurewa tayi, kuka ya kubuce mata da gudu tajuya tabar falon, abba yabita baya yana kiran sunanta,
Subeey kuka take sosai malam habu yaja hannunta suka wuce tasha, anan suka shiga mota, suka nufi kauye, tun a cikin motar tadaina kuka, saboda taga mutane sai kallonta suke,

*KAUYE*

Har lokacin da suka isa gidan malam habu subeey hawaye take, hauwa na hangosu ta taso da rawar jiki ta tarbe subeey ta amshi jikkar Subeey, sannan ta kamo hannunta suka shiga ɗaki tana k'ara gyara mata wurin da zata zauna_ sannu dazuwa mutanen birni" hauwa take fad'a cike fara'a

Subeey dai sai kallon ikon Allah take, wai yau itace hauwa keji da ita tana rawar jiki a kanta, zama tayi ta dinga mata labari tana so ta saki jiki da ita

Hardasu abinci mai rai da lafiya ta girka mata, share hawayenta kawai takeyi tana bawa zuciyarta hakuri, azuci tace " tohh miye amfanin damuwar? Komai Allah ya ƙk'addara faruwarsa bazata iya canja ƙk'addararta ba, kuma bataso tana ganin iyayenta na mata rawar jiki tana matsayin ƴ'yarsu, hakan yasa tasaki jikinta komai takeso shi akeyi agidan, tasamu gata sosai, dadare akace kwanciya, suka barwa subeey gado sukuwa suka kwanta a kasa, hakadai ta kwanta bawani bacci kirki tayiba har gari yawaye,

Via OHW📚

HAKA SO YAKE 43-44

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_43 - 44_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Yau da shirye-shiryen zuwan Abba suka tashi, kowa na gidan cikin farin ciki yake, sai k'ara gyaran gidan suke, ga kamshin girke-girke dake tashi.

Da wuri jirginsu ya sauka, Abdul ne yaje ya ɗaukoshi, subeey na falo tana faman jeren Abinci a dinning ya shigo, da murnata tarbeshi sannan ta durkusa har ƙk'asa ta gaisheshi, ya amsa da "Lafiya lau suwaiba, ya gidan?" tace "da bakanan dai Abba....., anma yanzu tunda ka dawo lafiya Alhamdulillahi"

Momie dake safkowa tace "Toh ay baki ƙk'arasa ba maganarba, da bayanan me? Kenan duk kinfi jin daɗin gidan idan Abba nanan ko?" tana dariya tace "A'ah momie ba haka nake nufi ba, kuma inajin daɗi amma gidan kamar bai cika ba idan Abba bainan ko Ya Abdul? Ta juya tana kallonshi, ko ɗaga kai baiyi ya kalleta ba.

Momie tace "kidai gyara maganarki kawai, amma ni nasan kunfiji da Abbannan naku" Abba yana dariyabYace "da ke sai yau kika sani?" sukayi daria gaba ɗayansu, sannan ta rakashi ɗakinshi ya watsa ruwa.

Sun Zauna su dukansu a falo suna cin girki suka jiyo sallamar malam Habu (mahaifin subeey), cikin farin ciki subeey ta tashi ta taroshi tana murna da ganin mahaifinta.

Bayan ya zauna sun gaggaisa, aka ajjiye mishi nashi girkin yanaci subeey na gefenshi sai daɗi takeji saboda tana son babanta sosae,
Sai bayan yagama cin abincin yayi hamdala, sannna, Momie tadubesa  tace " Da Alama Akwai magana a bakinka malam habu"

Abba Yace "Amma ay da kin barshi ya huta ko?" malam habu yace "A'ah Alhaji daman sauri nake in koma da wuri, magana kam akwaita yaya, zuwa nayi zan tafi da suwaiba can ƙauye nayi mata miji, ya faɗa babu ko ɗar a ranshi.

Abba, Momie, Abdul duk suka ɗago suna kallonshi, banda suwaiba data kasa ko motsi saboda tsabar razana ƙk'irjinta na bugawa da sauri, Momie tace "Wacce irin magana ce kakeyi wannan? Subeeyn zan baka kayi mata auren ƙk'auye? Haba wannan abin aiko a mafarki bazai yuyuba"

Malam yanisa yana kallon momie Yace "A'ah yaya shima a birni yake mijin nata, ba'a kauyeba"

Momie duk ranta yasoma baci dasauri tace "koma a ina yake ban amince ba, nice nan zan aurar da subeey, domin ninafi kowa sanin mijin daya dace da ita"

malam habu Yace "Amma yaya ai bamuyi haka dake ba, tun farkoba saida na hak'ura na baki subeey tayi karatu a hannunki, munyi dake zaki zaɓa mata mijine?"

Momie  tace "bamuyi ba, amma babu wanda zai tauye ma suwaiba hak'inta, yarinya tatashi a birni sannan za'ace amaidata kauye haba!!"

Via OHW📚📲

HAKA SO YAKE 41-42

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_41 - 42_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Bayan sun fita malam habu yad'aga edosa yadube hauwa,
Hauwa ta bushe dadariya "wayaga namijin gaske a gaban mazaje, basai jikinsa yad'au rawa ba" takara maganar tana dariya,

Malam habu yace "ke meye abin dariya farin ciki yana gaf da samuwa acikin gidan nan, yanzu indan Alhaji ya aure suwaiba aini da talauci munyi hannun riga", Malam habu yad'aga hannunsa sama yana rokon Allah yasa suwaiba takasance zabin Alhaji, domin ta wannan hanyar ce kad'ai zai iya biyansa kud'insa,

*BIRNI*

Subeey gabaki d'aya yanzu tasaki jikinta kamar babu abinda ke damunta, duk da kuwa a cikin zuciyarta akwai wani bangane wanda ta ajiye soyayyar Abdul aciki, amma takasa mantawa dashi, koda yaushe taje kwanciya saita tuna cewa yanzu shikenan ta rasa abdul, yanzu watace zata aure Abdul ba itaba, duk ta tuna wannan sai tayi kuka,

Soyayyarta da ahmed kuwa sai abinda yakaro domin yanzu kullum yana hanyar gidansu,
  Tun Abdul yana nuna damuwarsa akan haka har yazo yadaina nunawa amma a koda yaushe yaga ahmed yana fira da subeey, to sai yaji kamar ana masa zugar wuta a zuciya, amma saidai baya ganin laifin kowa ta wannan hanyar shikansa yasan laifin sane,

*BAYAN KWANA UKKU*

Misalin karfe 8:30pm Nadare subeey ce kwance a cikin d'akinta kan gadonta tana juyi, waya makalle a kunnenta ga dukkan alamu waya take kuma wayar tayi matukar mata dad'i, kuma bada kowa take wayarba face Ahmed,
Ahmed yace "kinsan me, Allah jiya nayi mafarkin wai angyara miki edon nan, kinyi bala'in kara kyau"
  Dariya tafashe da ita sannan tace " ai wannan edon nawa bazai taba warkewaba nima hakan natashi naga kaina, kama daina wannan mafarkin,"
Ahmed shima dariyar yake yace "ninasan wata rana insha Allah zan gyara miki shi matukar zai gyaru, amma dai sai bayan munyi aure, domin bazan gyarashi a yanzuba wani yaganki yamun kwace"
Subeey tace "lah ashema ragone akan soyayya har kana tunanin wani zaizo ya kwaceni a wurinka"
Ahmed yace "tap waya isa ai ko mutuwa bazatayi wannan gaggancinba, ke nida kefa mutu ka raba takalmin kaza"
Subeey tayi murmushi tana shirin yin magana,
Momy ta turo kofar d'akinta tashigo, dasauri tacewa Ahmed "ina zuwa momy tashigo" bata jira yayi maganaba takashe wayar tana kallon momy tana murmushi,
Momy takaraso kusa da ita tazauna tana murmushi tace "subeey sarkin waya ke kam ko gajiya bakyayi"
Subeey ta noke kai saboda kunyar dataji ta risketa a lokaci d'aya, takasa yin magana sai murmushi take,
Momy tayi ajiyar zuciya sannan tace "daman bakomaine yakawoniba face akan maganar ahmed, munyi waya da abban ku  yace jibi zai dawo, nayi masa magana akan ahmed, yace kice yaturo iyayensa zuwa jibin sai suyi magana akan aurenku"
Subeey ta rufe fuskarta tana dariya, ciki - ciki tace "toh momy zan fad'a masa" takarasa maganar kamar wata marar lafiya,
Momy tamike tsaye "toh shikenan, sai kin fito ina jiranki a falo" tace to momy,

Nan Momy tafita, 

ko karasa rufe kofar d'akin momy bata yiba subeey tayi saurin ciro wayarta takira ahmed ringing biyu yad'auka tana fara tace "abishirinka "
Ahmed yace "fari kal, kamar farin wata"
Subeey tace "abbana zai dawo jibi, kuma yace agayama katuro iyayenka akan maganar aurenmu"
Ahmed kasa cewa komai yayi dan farin ciki, saidai subeey takara cewa "yadai  naji kayi shiru"
Ahmed yasauke nunfashi yace "masha Allah,  nama rasa mema zance, akan farin ciki, ina zuwa bari naje nayiwa ummata wannan farin albishir" subeey tace "toh agaida umma" nan suka kashe wayar subeey tatashitafita falo sukayi kallo ita da momy,

Ahmed kuwa yayiwa ummansa albisir, saida tayi hawaye dandad'i yanzu dai yaronta zaiyi aure, daman abinda take muradine tuntuni.

Abdul kuwa yasamu labarin a wurin momy domin koda tabar d'akin subeey ta fito falo tatarar dashi azaune yana kalllo anantasar dashi, saboda tsabar bakin ciki, tashi kawai yayi yabar falon tare dacewa momy kansa keciwo, ai kuwa yana shiga dakin yashare hawayensa ,yarasa meyasa yake damuwa da subbey a yanzu, shin kodai hasashen da zuciyarsa ke masa gaskiyane sonta yake,    
    dakarfi yace "no baso a raina, kuma zanfita harkar subeey har abada" da wannan zulumin yakwanta saman gado yana hawaye wad'anda yakasa sanin dalilin zuwansu..

Via OHW 📚📲

HAKA SO YAKE 39-40

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_39 - 40_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Yanaji suna dukan kofar suna fad'an kafito malam habu, Allah idan baka fitoba yanzu zamu kira Alhajin birni musanar dashi "
Haka yayi banza dasu saida suka gaji da kiransa sannan sukaga bayada imanin fitowa, suka tattara inasu inasu suka bakar kofar gidan,

Sai alokacin malam habu yasamu yasauke nunfashi sannan yakarasa cikin gidan,
Hauwa tana tsaye a tsakiyar gidan duk tanajin abinda ke faruwa,
Malam habu nashigowa  ta bushe dadariyar mugunta,
Uffa baice da ita yafe mata ledar kwakin daya shigo dashi, sannan ya wuce d'akinsa,
  Har yakusan shigewa d'akin yaji tana fad'an "malam kullum ace mutum yana cikin gida saikace wata macce, ai wlh nimiji kamar maza yakeyi, kafita mana kafafata da mutanen nan, amma kawai saikazo kazauna gida, wlh Allah dai yawadan ragon namiji"  tana kai karshen maganar tawuce d'akinta,

Hawaye suka sauko acikin edon malam habu, yarasa wane irin rashin tausayine hauwa take dashi, ita kullum bata fahim babu,

  jinjina kansa kawai yayi yashige d'akinsa tare da share hawayensa,

*BAYAN KWANA D'AYA,*

Tunda safe malam habu yatashi yafita masallaci domin a lokacin ne kawai yake samun damar fita batare dawani yaganshiba,
  Bayan sun gama sallah, yadawo gida, dakinsa yashigo yana lazumi, a nan yatarar da hauwa tsaye a tsakiyar d'akin tayi tsaye tana kallonsa a wulaknce,
Saida yakai karshen lazuminsa sannan yadube yace " hauwa lafiya kuwa ? "
Hauwa ta ce " ina kuwa lafiya yau sau nake naje gidan biki, kawatace ta haihu kuma akwai biki tsakanina da ita dan haka yazama dole naje mata dawani abu"

Malam habu yasauke nunfashi yace "yanzu ya kikeson ayi kenan "

Hauwa tayi tako daya zuwa biyu sannan tace "kud'i nakeso a wurinka, kamar dubu ukku zuwa sama haka, zankai mata"

Dasauri malam habu yace "kud'i kuma hauwa kifasan irin halin danake ciki, wanda abinci gidansama gagararsa yake taya za'a yi a yasamu kud'in bayarwa akai gidan biki, dan Allah kidaina wannan Zancen"
Hauwa ta d'aga murya tafara masifa "wlh bazai yuyuba haka kawai, ni bandamu da halin dakake cikiba, kawai nidai kud'i nakeso duk yadda zakayi kafita kaje kaka womin, idan ma sata zakayi ni babu ruwana"

Malam habu yace "Allah yatsareni da inyi sata, hauwa kirika furta kyankyawan lafazi a kan mijinki bawai munanaba, nidai nagaya miki banda kud'i kuma banda mafitarsu dan haka kiyi hakuri,"
    Hauwa tafashe da kuka sosai "yanzu saboda Allah ace mijinka baida kud'i bazar dubu uku wai bakada, ni wlh tattara kayana zanyi nakoma gidan mu naje cen nahuta da wannan talaucin naka," tana karasa maganar tafice tabar d'akin, malam habu yana kiran sunanta amma taki ko juyosa_

Bayan fitarta malam habu yayi tsaye yana kallon kofar data fita, zuciyarsa cike da kuna, bayason yana ganin kukan hauwa, tunani barkatai yarika zo masa, ta yadda zai samu kud'in dazai faran tawa matarsa rai,
  abokinsa malam idi yafad'o masa arai, yasan dacewa matukar yaje wurinsa da lalara indai ta kud'ice tozai samu kuma bazai takurashiba akan yabashi amma saidai shikuma idan zaka biyashi kudinsa saika nunka masa bashi da ruwa yakeyi,

Jikinsa a sanyaye yafita daga d'akin yakarasa d'akin hauwa koda yaje tana had'a kaya tasaka a ghana mazgo,

Malam habu yakaraso kusa da ita yasauke murya yace "kiyi hakuri hauwa, karkije ko ina dan Allah, yanxu zanje nakawo miki kud'in"
    Hauwa tajuyo tashare hawayenta tace "kokaifa haka akeson namiji da sharewa matar hawaye a lokacin datake bukatar hakan, yanxu ina zakaje kasamo kud'in"

Malam habu yace "zanje gurin malam idine nasan zai bani aron kud'i"
Hauwa tayi murmushi "toh shikenan Allah yasa yabayar sai kayi saurin katafi tun safiya bata idar da wayeba, kar wad'an cen An wahalar su ganka"

Malam habu yadube Kofar d'akin, yaga gari yafara haske, sannan yajuyo ya kalli hauwa yace "daukomin hijab, da kuka zani"
Cike da mamaki hauwa tace "mekuma zakayi dasu"
Malam habu yana kokarin cire hularsa yace "zan chanza kaman nune, domin nasan dacewa kafin nakara gidansa gari yayi haske sosai mutanen nan zasu iya ganina, shine zan saka hijab da zani dan sauya kamanni"

Dariya abin yabawa hauwa amma saita gimtse, tace "toh shikenan"
Zura hannu tayi tadauko masa wani hijab da zani ta mika masa,

Haka malam habu yakarba yasaka, abin tausayi yajuyo ya kalli hauwa yace " saina dawo" yana kai karshen maganar yafita yabar d'akin,
  Yana fita hauwa ta bushe dadariya, harda tafawa, saida takai zaune akan dariya, cikin dariya ta furta "Allah sarki malam d'ina, gaskiya nayi sa'ar mallakashi, bokana ya iya aiki" takara bushe dadariya hartakai kwance,

Cikin boyon sifa malam habu yakarasa gidan malam idi, yayi sallama malam idi yafito,
Dasauri yajashi suka koma ciki sannan yacire hijab yace "nine malam habu dan Allah taimako nazo kamun"
Malam idi yayi matukar mamaki dasauri yace "wane irin taimako kuma malam habu"
Malam habu yace " kud'i nakeson ka aramun naira dubi ukku, wlh banida ko sisi kuma gidana babu abinci da za'aci"
Malam idi yace "ni kasan banda matsala amma dai kasan irin bashina, ko yaushe mutum yatashi biya na to nunkamin yake, kayarda nabaka"
Malam habu yace "eh nayarda bani"
Malam idi yasa hannu cikin aljihu yaciro kud'i naira dubu ukku yamikawa Malam habu"
Malam habu yayi godiya, sannan yamayar da hijab d'insa yafita yabar gidan,

Koda yakaraso kofar gidansa gari yayi haske sosai, dasauri yashiga gidan, ya mata bai rufe kofar gidanba, saboda tsabar rikicewa haka yashiga a gigice,

Hauwa naganinsa tayi saurin zowa kusa dashi, "malam ansamu kud'in" tafad'a tana mika masa hannu,

Saidao yacire hijab da zani sannan yasamu yayi ajiyar zuciya yace "eh ansamu gasu" yad'auko yamika mata,
Takarba cike da farin ciki, tana kirgawa saida ta gama sannan tad'ago kai ta kallesa tace "kud'i sun cika, yanzu saura kud'in cefane "
Malam habu yajuyo ya kalleta cike da mamaki "haba hauwa yanzu dan Allah baki ko tausayina kijibifa yadda nasamo kud'in nan dakyar, amma shine bazaki iya cire naira d'ari a cikinsu kigirka mana koda dan tamalele bane, yanzu yakikeson nayi"
Hauwa ta ja tsaki "ohonma kaika sani, niba ruwana a ciki, wad'an nan kud'in dai bazan tab'a suba, kuma wlh ni baruwana dajin yunwarka, domin mu yau gidan biki zamu wuni abinci saimun ture, kai sai kazauna da yunwa, nikaga tafiyata "
Malam habu yasaki baki yakallonta,  tana kokarin wucewa d'akinta

  Kamar daga sama sukaji shigowar karti a cikin gidan,
  Malam habu harzai gudu sukace dawo-dawo_
Dolensa yatsaya cak wuri d'aya yana masu magiya,
Alhajin birni ne yashigo gabansu yana kallob gidan malam habu a wulaknce, sannan yajuya ya kalli karta dake bayansa yace " ko bincikemin gidan nan kufitomin daduk wani abu mai amfani, " bamusu kartin nan suka fara Antayo kayan  d'akin malam habu da hauwa a waje, saida suka yiwa gidan kacha2 sannan suka dawo gaban alhajin birni,

D'aya daga cikin kartin nan yace "alhaji bakomai a cikin gidan na amfani"
Alhajin birni yadube malam habu yace " kai wane irin talaucine ke damunka, mekake dashi duniya bakada kowane"
Malam habu yadurkusa har kasa a gaban Alhaji yana hawaye yace "dan Allah alhaji kayi hakuri wlh zan mayar maka da kud'inka"
Alhaji birni yace " ai banga alamar hakan ba, kai gashi ba manyan yara maza kake dasuba balle nace kabani d'aya yamun aikin gona kota hakanma na fanshe kud'ina, kai bakada kowane,? yara nawane dakai?"
Malam habu yace " yara biyune alhaji"

Alhajin birni yadube gidan kaf yaga yaro dayane ero, dayake mamkale ajikin Hauwa yana kuka, sannan yadube malam habu yace "toh ina d'ayan yaron yake"

Malam  habu muryarsa na rawa yace "d'ayan macice kuma bata hannuna tana hannun kanwa a birni" Alhajin  yawashe baki yace "yawwa anzo gurin, daman ina gaf da neman matar aure, kakawomin 'yar taka nagani kaga idan tamun zan aureta, kuma zan yafe maka kud'in danake binka, kuma zan kara nunka maka wasu kud'in kuma zan baka jari zaka fita acikin talauci"

Bakaramin dad'i malam habu yajiba, zuciyarsa cike rakon Allah yasa suwaiba tayiwa Alhaji koda zai fita wannan halin dayake ciki,

Cikin farin ciki yacewa Alhaji "tohm shikenan kabani daga nan zuwa kwana biyar zanje nazoma da ita idan yaso saika dawo kaganta"

Alhajin birni yace "tohm shkenan, a nan yakwashi makaranbansa sukabar gidan," tare da yarjejeniyar bayan kwana biyar zai dadawo yaga 'yar malam habu, SUWAIBA..

HAKA SO YAKE 37-38

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_37 - 38_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Nan suka watse kowa yakoma d'akinsa,
A ranar Subeey tayi kuka sosai, yanzu shikenan ta rasa Abdul mafarkinta bazai tab'a zama gaskiyaba, yanzu watace zata mallaki abdul ba itaba, hakadai tayita zancen zuci tana kuka,

Shikumlwa Abdul bayan yabar falon d'akinsa ya shiga yana hawaye shima yayi nadama sosai  akan abinda ya aikatawa Subeey a baya, yanzu gashi yarasata har abada kuma a yanzun ne  wani sabon sonta yake ratsa zuciyarsa daman *HAKA SO YAKE*, amma yazama dole yafita harkarta, kodan yabarta tasamu farin ciki da wanda takeso," duk azuci yake wannan zance, yajima zaune akan gado, sannan yatashi ya nufi toilet yayi wanka, bayan yafito yashirya yazo yayi breakfast sannan yafita yabar gida,

Subeey ma haka wanka tayi bayan tafito daga wanka, tashirya tsaf sannan tayi kokarin kawar dadamuwa dake kan fuskarta, tafito falo a lokacin tasamu ta karya bayan tagama suka zauna suna kallon ita da momy,
  Haka zamansu yakasance ita da Abdul...

*KAUYEN MAYYAMA*

Malam habu yana zaune akan tudun kofar d'akinsa ya zabga uban tagumi yana kallon tsakar gidan sa,
   Matarsa Hauwa tafito daga d'akinta tana kokarin gyaran d'aurin zaninta a lokacin ta hangesa zaune yayi tagumi, tsuke fuska tayi tana harararsa bayan ta kammala daurin zanin takaraso wurinsa, fuskarta d'auke da kalar rashin mutumci, cikin tsawa tace  "kai habu!!!" Tafad'a da karfi saida ya zabura ya d'ago kai yana kallonta,
Hauwa tarike kugu kamar mai shirin fad'a sannan tace " kana sane dacewa yau agidan babu abin zamuci, kuma shine kazo kazauna kana kallon tsakiyar gida"
Habu ya sauke murya yana kallon hauwa yace "nasani hauwa amma ai kinsan halin danake ciki, babu yadda na iya dolena nazauna gida domin zaman gidan yafimun kwanciyar hankali, koso kike nafita wad'an nan kartin su jibgeni" yakara maganar cike da kalar tausayi.
Hauwa ta yi fari da edo "nikam ba ruwana ehe komai zasu maka, ai kai kaja, meya kaika cin bashi, kai kenan kullum baka da aiki sai kwasar bashin mutane,  ni wallahi bazan zauna inajin yunwaba nida d'ana ba, dan haka koka je kanemomin abinci da zanci ko kuma wlh yanzu mufita yawon bara nida yarona muje musamu abinda mukaci tunda kai kazamo lusarin namiji"
Tunda tafad'i kalmar bara malam habu yashiga d'imuwa domin yasan bakaramin aikin hauwa bane zata iya zuwa, da sauri ya mike tsaye yad'aura hannusa daya akan daya yace "dan Allah hauwa karkije wannan wane irin bala'ine da wannan zanji, da zafin talaucin dake damuna kokuma da masifarki"
  Hauwa tace "wannan kuma kaika sani nidai wlh kaji zancena saika zabi d'aya kokafita kokuwa mana abinci kokuma yanzu naja erona mufita yawon maula ehe "
Malam habu ya marairaice fuska kamar zaiyi kuka yace "toh shikenan naji zan fita amma kisani idan aka kawo miki gawata saiki zauna kekidai a gidan" yana kai karshen maganar yajuya yanufi kofar fita gidan,
Hauwa tabishi da kallo tana gwatsinar fuska. Sai bayan yafita tafashe Dadariya "aikin banza aikin wofi, auren talaka ko jaraba, ni kajecen idan sun kasheka aina huta, kukan kwana uku kawai zanyi, wlh nadawo budurwata tsaf, nasamu mai kud'i na aura " takara bushewa dadariya sannan tanufi dakinta tana kiran sunan ero (yaronta )....

*WAYE MALAM HABU*

Malam habu haifanfen dan kauyen mayyamane, mano mine na gaske, yatashi cikin rufin asirin Allah yana kula da iyalinsa sosai,

Malam habu yanada mata guda biyu bintu da kuma hauwa, bintu itace uwar gida sunyi auren soyayyane shida bintu, har Allah ya azurtasu da samun haihuwa sunsamu yarinya d'aya wadda suka rad'awa suna Suwaiba,
   A gurin haihiwartane Allah yayiwa Bintu rasuwa, Malam habu yayi kuka sosai,  amma haka aka lallashesa aka bashi hakuri,
Bayan anyi sadakar bakwai ta matarsa aka mayar da jaririyar gurin kakanninta wato mahaifan malam habu,  acen Yarinya tafara girma haryakai shekara biyar, amma har lokacin malam habu baiyi aureba, iyayensa sun matsa masa sosai akan yakaro aure amma yak'i,
Kwatsam watarana babansa yace yanema masa mata Kuma aurensa nan zuwa sati d'aya dan haka yaje ya  gyara gidansa kafin amarya tazo,
Babu yadda malam habu ya iya dolensa ya je yagyara gidansa,

Bayan sati d'aya aka daura aure akan kawo masa matarsa mai suna hauwa,
Haka ya hakura zauna da ita,

Washe gari aka d'auko yarinyarsa aka kawowa hauwa, anan sukaci gaba da renon 'yarsu cikin kwanciyar hankali, sun masu farin ciki sosai a zaman gidansu,

Kwance tashi hauwa tashare shekara biyar babu haihuwa acikin gidan malam habu abin yayi matukar damunta, hankalinya yatashi, tundaga lokacin zaman gidan yafara chanzawa, tafara chanzawa suwaiba, kullum cikin gallaza mata take,  itace wanke wanke itace shara  kullum batada hutu,
Da malam habu yaga abin yayi yawa shine yayi magana,
Amma sai hauwa tace masa "tarbiyace ake koyawa yarinya, kuma da ayyukan gida"  malam habu babu yadda ya iya dolensa yabarta, haka taci gaba da gallaza mata tana gana maya azaba. Yarinya duk tabi yarame, ta kod'e,

Kwatsam wata rana 'yan uwa malam habu na birni (su momie) suka kawo ziyara gidan, Allah ya jarabci momie dason 'ya macce amma batada ita,
  Suna shigowa gidan suka tarar da hauwa tana jibgar Subeey, momei ce taje tayi saurin karbarta tana yiwa hauwa fad'a, 
Malam habu nashigowa aka sanar dashi abinda Ke faruwa zafin zuciya ya d'ibesa anan Ya aukawa hauwa saki d'aya, dolenta takwashe kayanta tabar gidan,
  Nan momie ta bukaci abata suwaiba taje da ita birni,  da farko har malam habu yace bazai yardaba, amma daga baya da aka lallashesa sai ya yarda, a ranar momie ta d'auko suwaiba suka dawo birni,

Shikuwa malam habu, yashiga damuwa sosai narashin 'yarsa kwaya d'aya kuma gashi ba mata,
Ummansa sace matsa masa akan dole saiya mayar da hauwa d'akinta, domin zaman hauwa adakinta shine rufin asirinsa, bazai iya musanyawa umman saba dolensa yasa aka mayar da hauwa,

Bayan dawowar hauwa da shekara, tabazama zuwa wurin bokaye da malaman tsibbo akan tanason tasamu haihuwa kuma tanason duk dukiyar malam habu gabaki d'aya tadawo a hannunta duk abinda takeso shizai mata,

A haka tasamu wani boka yabata magani, tazo tarika zarar kud'in malam habu, batare daya damuba, duk abinda takeso sai yayi mata shi, koda kuwa baida kud'in yinsa sai yaje yaci bashi yazo yabiya mata bukatarta, a haka har suka share shekara biyar tana azarbar dashi da bashi, ya wahala sosai, yaci bashi harna wahala, amma ita ko a jiknta,

  Wata rana kwasam tawaye gari ba lafiya, aka kaita asibiti a nan suka tabbar  mata da tanada ciki,
  Tayi matukar farin ciki akan samun cikin,

Bayan wata tara tahaifi cikin tasamu santalelen yaro, wanda aka rad'awa suna ibrahim amma suna kiransa da ero, .. Yanzu haka ero yanada shekara 6 a duniya,

bashin malam habu kuwa sai kara hauhauwa yake, yanzu hartakai ga bazai iya fita wajeba domin bashin wani alhajin birni yaci, shine alhajin yabawa yan daban garin kwangilarsa idan suka ganshi yafito, tosu kwamasosa sukawo masa, bayan sun narka mashi duka sosai,
   hakan yasa yayi kwana biyu bai fita konina kullum yana gida_ sai yau da hauwa ta'aza masa masifa yasamu yafita,

*Wannan kenan*
  
_Back to story_
*BAYAN WASU MINTUNA*
Malam habune ya famtamo da gudu cikin gidansa yana ihu da wata leda rike a hannunsa, Yana shigowa yayi saurin ya mayar da kofar gidan yarufe yasa key yadanne yana huci...

Via OHW 📚📲

HAKA SO YAKE 35-36

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_35 - 36_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Yana shiga falon, ɗakin momie ya wuce yana k'wala mata kira, yanayin kiran ya sanya ta tunanin ba lafiya ba, ta taso tana tamyarshi "lafiyarka kuwa Abdul, meya faru da kakemin wannan kiran?

Cikin  bacin rai Yace "momie wa yace akabar subeey ta shigo da wannan Yaron gidannan?"

Da mamaki momy Tace "wanne Yaro kenan?*
Abdul ya nuna kofar fita, Yace "wancan saurayin nata mana"

Momt tace "tohh saboda me za'a hanashi shigowa tunda wurin subeey yazo? Koda laifine dan namiji yazo wurinta ita ba macce bace"

Abdul yakara tsuke fuska yana fad'an "Amma dai momie ai bai kamata ace tana shigowa da samari barkatai ba a cikin gidan, hakan zai iya tab'a matabar gidan nan"

momie tatab'e tabaki tana kallonsa Tace "Ikon Allah, banda Ahmad akwai wanda subeey ta taɓa kawowa gidannan? Kadai kawai ka fito fili  ka faɗa mana kishi kake, idan kana sonta zamufi kowa farin ciki Abdul, tunda dama a tare kuka tashi"

Kasa cewa komi yayi saboda takaicin maganar momie da Yake ji, shikenan da yayi magana sai ace kishinta yake? Sonta yake? Tohm shikenan daga bazai kara shiga sabgar taba, duk a zuci yake wannan zancen,

A fili kuwa kasa furta komai yayi , Juyawa kawai yayi yabar ɗakin momie da bishi da kallo tana dariya.

Sama-sama subeey take bama  Ahmad amsa tambayoyin dayake mata saboda kwata kwata hankalinta baya jikinta saboda ganin yanayin yadda Abdul yashiga gida, saitajita duk tayi wani tajima bataji irin wannan akanshiba tun ranar datayiwa kanta alkawarin zata daina sonsa kota halin k'ak'a
    basu wani daɗe sosae ba ta sallameshi ya tafi. Saboda  gabaki d'aya batajindadin jikinta,

Tana shiga gida ɗakinta kawai ta shige ta faɗa gado zuciyarta cunkushe da tunani. Kala-kala

*Washe gari*

Su duka babu wanda ya fito break fast duk momie na lura dasu daman babu wanda Yaci dinner jiya a cikinsu, kuma yanzu gashi safiya ta wayw sunki fitowa suyi break fast, talura da cewa suna cikin damuwa, hakan yasa tanufi d'akunansu,

Kiransu tayi su duka suka hallara a falo ta zaunar dasu tana fuskantarsu,
    Abdul duk ya haɗe rai, subeey tayi kalar ba ruwanta d'in kamar wata marar lafiya,  Momie ta fara magana.
"Ku duka ba kananan yara bane kunsan abinda ke cikin zuciyoyinku, idan har kunason junanku wannan abin farin cikine a wurinmu, ku faɗa mana kawai tun kafin maganar yaronnan ahmed tayi nisa a tsaida ita, meyasa kuke nema ku cutawa kanku"

Su duka shiru sukayi, kuma babu wanda yad'ago koda kansa a cikinsu,

Momie tayi ajiyar zuciya sannan takara kallonsu  tace "ku nake saurare"

Abdul Ya buɗa baki zaiyi magana "amm.. Ammm.."

Subeey ta rigashi "basai kafaɗa ba Ya Abdul, momie babu maganar Aure tsakanina da Ya Abdul, ni na samu wanda ke sona kuma zai aureni, shima inai masa fatan Allah yabashi tagari"
Momie ta jinjina kai, tace "Shikenan Allah ya zab'a abinda yafi zama alkhairi"

Shiru Abdul yayi jin maganganun da subeey tayi, Yayi niyyar ya buɗa bakine ya tabbatarma momie da cewa yanason subeey kuma da aure, amma ita ta rigashi da faɗama momie ita Ahmad takeso, ita  kuma subeey tayi hakane don batason ya faɗawa momie bai sonta, domin babu abndata tsana fiye da jin hakan,

Via OHW📚

HAKA SO YAKE 33-34

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_33 - 34_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Abdul dafe kansa yayi, ya koma ya jinginar da kanshi jikin gado, ko ina cikinshi kyarma yake ya ɗauki zafi kanshi kamar zai rabe biyu yakeji.

Daƙk'yar ya iya rarrafawa ya bud'e bedside drower ɗinshi ya ɗauko magani, ya zuba ruwa a cup dake kusa dashi ya ɗaga kai ya haɗiye daƙk'yar sannan ya koma ya kwanta.
     Wani irin zafi yakeji a zuciyarshi, nan yafara zancen zuci "to mezaisa ya damu kanshi? Haka kawai zai sanyama kanshi ciwo ba wani dalili, "bazan taɓa sonta ba, bazan taɓa aurenta ba" ya faɗa a bayyane, wata zuciyar tace "ka fita hanyarta mana, idan kana kulata ne zaka shiga damuwa" ya gyara kwanciyarshi, tabbas zan fita harkar subeey.hakan ya ajiye aransa har bacci yazo masa,

*Bayan kwana biyu*
Soyayya sosae suke tsakaninsu subeey da Ahmad, kullum tana mak'ale da waya a kunne suna fira.

Abdul kuwa ko kaɗan ya daina nuna damuwarshi a kanta, magana ma saita kama dole take haɗasu, ita hakanma daɗi yayi mata, don yanzu duk lokacinta na Ahmad ne.

Yau tatashi cikin farin ciki, saboda murnar ziyarar da Ahmad zai kawo mata a karon farko, tunda wuri ta fara shirye shiryen zuwanshi, kafin la'asar ta gama da haɗa mishi ƙk'ayatattun girke-girke kala-kala, sannan ta shiga wanka bayan yace mata yana hanya.

Bayan tafito wanka Ta daɗe tsaye gaban kayanta tana tunanin kayan da zata saka, can ta hango wani jan material ɗinta ta tuna yanda yayi mata kyau sosae ranar data saka shi saida Abdul ya yaba ya dinga ɗaukanta hotuna.
Daukowa kawai tayi tasaka Bata tsaya wani makeup ba, powder kawai ta shafa da lipstick, tana gamawa yayi mata waya ya iso yana cikin gidan, tace tana zuwa sannan ta shiga ɗakin momie ta faɗa mata cewa ya iso, momy tace "adawo lfiya"

Nan tafisa a harabar gidan tadda shi a tsaye, bayan takarasa wurinsa tamasa iso yazo yazauna,  Saida suka zauna saman fararen kujeru, sai kallonta yake ya kasa ɗauke idonshi daga kanta,
  Subeey Tace "Sannu da zuwa"
Ahmed yayi murmushi Yace "Yauwah mai kyau na sameki lafiya?

A kunyace ta janyo mayafinta ta rufe fuskarta,
Ahmed yay 'yar dariya Yace "Ya kuma zaki rufemin kyakkyawan fuskar taki? Hmm Gaskiya ne subeeyta, duk yanda na daɗe ina ganin kyawunki a cikin idanuwanki kin wuce nan"

Subeey ta bud'e fuskarta tana murmushi Tace "Hhm indai kyau kakeson gani sai in samo maka mirror kazauna kana kallon kanka, nidai banson kallo"

Amhed Yace "ni kuma farin cikina kenan inrika kallon fuskarki, kuma nasan kinason farin cikinah ba?.

Ta ɗaga mishi kai tana murmushi takara sauke murya tace "bansan ta yanda zan bayyana maka irin farin cikin da nakeji ba ganina a tare dakai"
Ahmed  Yace "nima da nasan ta hanyar dazan bayyana miki sonda nake miki toh da tabbas nawa sai yafi naki"
Tana murmushi tace  "hhm naka dai ka sani.

Firarsu suke gwanin ban sha'awah irinna masoyan da suke matuƙkaunar junansu, suna ƙyalƙyalar dariya abunsu.

Kamar daga sama sukaji shigiwar motar Abdul, yana hangosu duk ya haɗa Rai ya juyar da fuskarshi  gefe ta yadda bazasu gane ya gansuba,
Da sauri Ahmad Ya mi'ke ya tafi inda yake yana miƙa mishi hannu Yace "babban Yaya sannu da zuwa" bayan yafito daga ciki motar  kallon inda yake baiyi ba ya juyar da kanshi ya shige gida.

Ahmad bai wani nuna damuwarshi ba ya dawo inda sabeey take ya zauna sukaci gaba da firarsu hankalinta duk yana kan Abdul ganin yanda ya ɓata rai da ganinta da Ahmad..

HAKA SO YAKE 31-32

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_31 - 32_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Cikin takun girma da kasaita takaraso wurinsu, tayi tsaye a kansu, Sukayi shiru suna kallonta

Momy tayi murmshi tace "yanzu kuma me ake shiryawane,"
Subeey ta kirkiri murmushi sannan tace "a a momy bakomai kawaidai muna firane,"
Momy tace "wato shine ko kufito falo kuyi firar nan dani amma shine kukaki, naganeku 'yan kwanna kinnan kunfara gujemin koh, shi wannan mekayi masa ne naga fuskar tashi a d'aure" takarasa maganar tana nuna abdul da yatsa,

Subeey tajuya tadubesa daga bisani kuma tamaida dubanta wurin momy sannan  tace "a a momy ba komaifa, inajin bayajin dadine, nima tambayar danake masa kenan"
Momy tace "toh shikenan nizan koma falo, sai kunfito,"
Subeey tace toh mommy"
Nan tafita tabarsu,

Bayan momy tafita subeey tasauke nunfashi sannan takara juyowa ta kalli abdul tace "yaya Abdul tunda bazaka gayamun matsalar kaba nizan koma d'akina " tana karasa maganar ta mike tsaye tana kokarin tafiya, Abdul yayi saurin riko hannunta da karfi saida ta razana, ya janyota tadawo saman gado tazauna,
  A hankali abdul Ya d'ora goshinsa akan nata suna sakar nunfashin juna, cikin sanyin murya yace "meyasa kika kulashi, " cike da rashin fahimta subeey tace "waye kuma yaya Abdul"
  Abdul ya lumshi edo sannan ya bud'e yasaka edonsa acikin nata sannan yace "Ahmed!!!, "
Sannu a hankali subeey ta janye goshinta akan nashi,
Tamike tsaye tana kallonsa,
Abdul ya d'ago edonsa dasukayi ja sosai ya kalleta,
Saida tagama karantar yanayinsa sanan tace "kishine koh, kishi kake akaina, hmm toh kishin meye, bayan babu sona a cikin zuciyarka, tohm meye nakishi dan na kula wani"  tadan dakatar da maganarta tana jan nunfashi,
Sannan taci gaba dacewa "Meyasa na kula ahmed koh, shine tambayar dakayimun, tohm nakula ahmad ne saboda ina sonsa a yaune muka tabbatarwa da juna sona hakika, kuma ni a ganina mundace da juna, domin shi misakine nima haka, yaya Abdul katsaya iya matsayinka na yayana karka nemi katakura rayuwata niba yarinya bace masan komai daya dace dani" tana kai karshen maganar ta juya tana hawaye tafita yabar d'akin,

Abdul ya kanne edonsa sosai yakasa bud"ewa, tunda subeey tafara magana yakejin zafi da radadi a cikin zuciyarsa,

Sai bayan tafita dakusan minta biyu sannan ya bud'e edonsa, yana akallon d'akin kansa yakejin yana masa ciwo sosai, nan take jikinsa yadau zafi...

Via OHW📚📲

Wednesday, 16 November 2016

HAKA SO YAKE 29-30

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_29 -30_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

www.babymsh.blogspot.com

Kamar zaki haka yake kallonta yana huci, subeey ta lurada yanayin dayake ciki, ta d'aga mashi edo "yaya yadai, lafiya naganka haka" takarasa maganar da fara'a

Kamar gunki haka ya mata tsaye yakasaka magana,
Subeey tad'an daure fuska tana kallonsa "yaya wai lafiya ne, ko wani abu akayi maka ne"
Hakan ma shiru yamata yana kallonta, sai cen yad'aga hannunsa yanunata kamar zaiyi magana sai kuma yafasa, a hankali yake sauke hannu sannan yajuya yafita yabar d'akin, ransa a bace,

Subeey tayi kuru tana kallon kofar d'akin, a zuci take tambayar kanta "shikuwa wannan me kayi masane haka " tad'an makale kanta akafad'arta sannan tace "komema akayi masa bari dai naje naji" tana gama maganar tajanyo mayafinta tasaka sannan tafita tanufi d'akinsa,

Yana labe a bakin kofar dakinta ashe bayan yafita baije ko inaba, yana tsaye a bakin kofar d'akin yana share hawayen da suka sauko daga cikin edonsa, yana tsoron karya fita suyi kicibus da momy,

Saida yaji motsin tafiyarta tana kokarin fitowa sannan yayi saurin share hawayensa yabar kofar d'akin, gudu-gudu sauri-sauri haka yakarasa d'akin yana shiga yamayar da dakofar d'akin yarufe, dafe kansa yayi saboda wata irin juyi dayake ganin d'akin yana masa, jirine ke dibarsa sosai, da sauri yazauna gefen gado yana maida nunfashi, 5 sec sannan yadawo normal, a daidai lokacin subeey taturo kofar d'akin tashigo,

Ganinshi zaune a gafen gado yadafe kai yasa tayi saurin karasa wurinsa tana fad'an "yaya lafiya...!"  Jin muryarta a kusa dashi yasa yayi saurin d'ago kansa sukayi edo hudu, sai a lokacin Ta lura da irin yadda launin edonsa yachanza zuwa ja, sunfi kusan min biyu suna kallon juna, saicen subeey takauda edonta gefe, daga bisani kuma takara juyo ta dubesa sannan tace "yaya abdul wai meke damun kane, hankalina duk atashe yake kasa nakasa samun natsuwwa dan Allah Yaya abdul kafadamim, menene" koda takara maganar duk hawaye sun cicciko mata edo,
   Bakinsa yasoma rawa yana kokarin furta wata magana, sukaji an turo kofar d'akin anshigo,
Suduka suka mayar da dubansu wurin kofar,
Momyce tashigo tana murmushi ganin su zaune a tunaninta fira suke, amma ganin yanayin fuskar abdul yasa tayi  jugum tana kallonsu..

Via OHW📚📲

HAKA SO YAKE 27-28

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_27 -28_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

www.babymsh.blogspot.com

Subeey ta bushe da dariya tace "perfect, komai ka amsa daidai" shima dariyar yake yace "ai akanki komaima daidaine a wurina"
Subeey tatsayar  da dariyarta tayi gyaran murya sannan tace "yanzu meke tafe dakai,"
Amhed yayi jim yana tunani saicen yayi murmushi yace "duk abinda zuciyar subeey ta saka mata tohm dashi ahmed yazo"
Subeey tayi fari da edonta d'aya "umm ni zuciyata ta bani cewa Ahmed yazone da sakon..." Saikuma tayi shiru tana dariya,
Ahmed yayi saurin cewa "uhim fad'i mana menene"
Subeey ta gimtse dariyar ta sannan tace "sakon so, amma saidai subeey fa tanada wanda take so"
Saida ahmed yaji gabansa yafad'i dasauri yakara gyara zamansa "dan Allah da gaske kike "
Subeey takara bushewa da dariya jin yadda ya tambayeta kamar mai shirin yin kuka,
Da kyar ta iya samu ta tsayar da dariyarta a lokacin duk ahmed ya k'agu yaji gaskiyar lamarin,
Subeey tasauke nunfashi bayan tagama dariya sannan tace "zuciyar subeey fankoce babu komai a cikin sai jiran masoyin gaskiya, mai so tsakani da Allah, mai iya zama dani a duk  halin danake ciki, mai karemun martabata da kuma kimata, mai sakani farin ciki, amm.." Sai tayi shiru,
Ahmed jiyake kamar an masa bushara da zuwa hajji, farin ciki fal a zuciyarsa, dasauri yace "uhim ina jinki karasa mana"
Subeey tace "amm sai kuma wanda zai yarda duk safiya ta Allah na wanka masa mari sau biyar, batare dayaji zafiba, saidai kawai yacemun "thanks dear" ... " dariya ta kubuce mata takarasa karasa maganar,

Ahmed shima dariyar yake sosai " dan Allah kibarni haka, cikina harya fara ciwo, akan dariya," yakara maganar yana dariya,

Subeey takara sauke nunfashi bayan tagama dariya tace "kaji sharud'an subeey, kaifa meye naka sharud'an"
Ahmed yasauke nunfashi sannan yace "duk naji kuma na amince, saidai kuma ni banada sharud'a amma inada dokah"
Subeey tace "uhim ina jinka meye dokar"
Ahmed ya yayi gyaran murya sannan yace "dokar itace karki yarda kikula wani domin inada zafin kishi akan abinda nakeso, sannan kuma ina yiwa macce so 100% banason ta yaudare, domin hakan yana sakani matsala sosai, ina sonki subeey, nasan itace kalmar dakake jiran kiji nafad'a tun d'azu"
Subeey tasauke nunfashi tare da lumshe edo, kalaman dayake fad'a  suna ratsata har cikin jijiwowin jikinta,
Tana murmushi tace "godiya nake, saidai kuma nima inason nace ..." Sai kuma tayi shiru,
"Kinason kice me, dan Allah kifad'a wlh  na k'agu naji" Ahmed yafad'a yana murmushi,

Wata irin kunya taji ta rufeta, tasa hannunta d'aya tarufe fuskarta d'ayan hannun kuwa yana rike da waya,  cikin sanyin murya tace "nima inasonka..." Tana karasa maganar tayi saurin kashe wayar, saboda kunyar dataji, tana dariya,

Abdul Yana lab'e a bakin kofa duk abinda take fad'a yana jinta, jiyake kamar ana masa zuga - zugin wuta a cikin zuciyarsa, edonsa sunyi ja sosai, da karfi ya turo kofar d'akin yashigo zuciyarsa a zafafe, saida subeey  ta razana jin anturo kofar d'akin da karfi kamar za' a karya kofar, ta mike zaune a dai dai lokacin suka had'a edo....

Via OHW📚📲

HAKA SO YAKE 25-26

💕💕  *HAKA SO YAKE* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_25 - 26_* 💕
                💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Subeey tana rik'e da wayarta dai dai number Ahmad take kallo, ita kaɗai take murmushi tana tuna maganganunshi, Duk da babu sauran wuri a zuciyarta da zata iya saka soyayyar wani ɗa namiji a ciki, Ahmad yayi matuk'ar burgeta har take jin zata iya aminta dashi tunda bazata taɓa samun muradin zuciyarta ba.

Kamar ya sanda tunaninshi take, tare da jiran kiranshi, sai gashi ya kirata sunanshi raɗam akan screen ɗin wayarta,

Tayi jim tana kallon screen d'in zuciyarta cike da wasu-wasi tohh idan ta ɗauka me zata ce mishi? Kunyarshi ce ta lulluɓe ta edanta tuna yanda ta bashi numbarta daga tambaya,

A zuci tace " anya idanta ɗauka kiran bata zubda ajinta ba? Wata zuciyar tace "ay kin gama zubdashi kam tunda kika bashi numba" har kiran ya katse bata gama yanke shawara ba.

Cikin fargaba Ahmad yak'ara danna mata wani kiran, wayar nata ringing harya fara fidda ran da zata ɗauka, ta ɗaga kiran tare dayin sallama cikin siririyar murya mai zak'i, sai da ya lumshe ido ya buɗe sannan ya amsa shima ciki zazzaƙar murya.

Shiru sukayi gaba ɗayansu, tare kuma suka buɗe baki tace "Ya kake?" shima Yace "kina lafiya?", dariya sukayi gaba sannan suka gaisa, wani shirun ya k'ara biyowa baya.

Kowannesu sai sak'e-sak'e yake a zuciyarshi, babu wanda yayi magana sai can Ahmad yayi magana cikin zolaya "Sunana Subeey" dariya ya bama subeey sosae tace "Sunanka Ahmad ne, da Alama ka rasa Abin cewa ne kake nemar yimin k'wacen suna"

Yayi dariya Yace "Ay sunan naki ne mai daɗi subeey" tayi 'yar dariya sannan tayi shiru, su duka suka rasa abin cewa.

Ahmadne yak'ara cewa "ba tambayoyin da kikeso kiyimin?" tace "kamar wanne?" Yace "ko Abnda kikeson sani game dani" Tace "ka faɗamin duk abnda ya kamata in sani" Yace "kedai Ki tambayi abnda kikeson sani" Tace "tohh A'ah ba komi," Yace "kiyi tunani"

Tace "Tohh Zan tambayeka, Anma 20secs in baka bada Amsa ba shikenan" Yace "Na yarda"

Tace "Abincin Zamani kona gargajiya?
        "Na gargajiya"
Tace "best colour?
          "skye blue
Tace "Manyan kaya ko k'anana?
         "K'anana"
Tace "indian films ko American?
         "indian"
Tace "farar mace ko ba'ka?
           Yace  "subeey"..

Via OHW 📚

HAKA SO YAKE 23-24

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_23 -24_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

www.babymsh.blogspot.com

Tajima a hakan tanata sharar kukanta, saida aka fara kiran sallar azahar sannan tatashi jiki ba k'wari tanufi toilet tayi alwala sannan tafito ta fara sallah cikin natsuwa da kwanciyar hankali,
****            ****             ****
Bak'ar macece mai kyau da fasali tanad'an da 'yar kiba kad'an, zaune take cikin wani tangamemen falo,
  Falon ya k'awatu da kayar more rayuwa iri-iri, sanyi ac nadukanta tayi wani irin zaman kasaita tana kallon tv hankalinta kwance,

Ahmed yaturo kofar falon yashigo, yana tokara sandarsa harya karasa bakin kujera yazauna, sannan ya sauke nunfashi,

Matar ta dubesa bayan ta'ajiye remote d'in da ke hannunta "Yau kuma sallamar ma bazamu samu bane?"
Takarasa maganar tana kallonsa tare da girgiza masa kai,

Ahmed yasosa kansa cike da kunya ya dago kansa yadubeta yana murmushi "sorry umma wlh na mantane,"
Ya gyara zamansa sannan yace "Assalamu alaikum"
Umma ta amsa masa tana murmushi "yawwa my son kokaifa, daga ina naga kamar duk agajiye kake" umma tafada tana murmushi,
Ahmed yad'anja tsaki yana kokari jingina jikinsa a jikin kujera yace "wlh kuwa umma kamar kinsan a gajiye nake, jira kawai nake nadan hutu saina tashi naje d'aki nayi wanka"
Umma tace "ok aikam yafi kaje kayi wanka ka huta"  saida yayi mika sannan yace "wlh kuwa," yakara gyara zamansa akan kujera,
Umma sai kallon yanayin fuskarsa take, da dukkan alamu tagano cewa akawai magana abakinsa, tayi gyaran murya sannan tace "fuskarka takasa boye damuwar dake cikin zucuyarka, fad'amun meyeke damun Ahmaduna"
Ahmed yayi saurin d'ago kansa yana murmushi "hmm umma na kenan, kina saurin gano damuwata a duk lokacin dana kasance acikinta," yad'an tashi xaune yana kallon umma sannan yaci gaba dacewa "yau gamo nayi"
Umma tad'an zare edo "gamo kuma, !!! Allah yasadai bada aljanba "
Ahmed yana murmushi yace "a  a umma ba aljan bane, watace sunanta subeey, a bakin super market muka had'u yau"

Umma tad'an gimtse fuska domin ba dad'i maganar tayimataba, tayi ajiyar zuciya sannan tace "Ahmed!!, kai bazaka gaji bane, mata nawane suka cuceka, nafa gayama kafita harkar matan zamanin nan, basa yiwa mutum son tsakani da Allah, nifa ina tsoron karkaje wata rana wata tarabani dakai"
  Murmushi ahmed keyi yana kallon umma "umma wannanfa ba irinsu bace, kallo d'aya namata nagane cewa tanada natsuwa ga kamala da kuma ilimi, gaskiya umma ina ji a jikina wannan itace matar aurena, kuma itace tadace dani, domin itama iri nace"
Umma tayi saurin gyara zama tana cewa "itama gurguwarce "
Ahmed ya girgiza kai "a a ba gurguwa bace, sumul take da kafafunta biyu, saidai tanada matsala, amma bazan gaya miki matsalarba a yanzu sai tafiya tayi nisa, "
"Tohm shikenan, na yarda amma idan lokacin da zaka fad'amin yayi toh bazanso fad'aminba saidai kakawo min ita nagani da edona, naga meye matsalar surukar tawa "
Ahmed yana murmushj ya mike tare da riko sandarsa, yana tokarawa harya mike sannan yajuyo ya dube umma yace "shikenan na yarda, nizan wuce ciki nayi wanka, dan wlh jinake duk jikina ba dadi"
Umm tace "toh a fito lafiya, "

Tohm" Harya fara tafiya saikuma yakara juyowa ya dube umma yace "amm umma!! kicewa babba ladi ta had'amin tea kafin nagama wanka, domin harda yunwa nakeji bayan gajiyar,"
Umma tace "sarkin shan tea kaje zangaya mata," takarasa maganar da zolaya,
  Yana dariya yanufi d'akinsa,
Tunda ya bud'e kofar d'akin na zare edo ina kallon yadda d'akin ya tsaru ba datti saikace dakin macce komai a mazauninsa, d'akin yana kamshi turaren larabawa ga sanyi ac yana ratsa mutum,
  Yakarasa bakin gado yazauna tare da ajiye sandarsa gefe, yana furzar da iska abakinsa, a hankali naga yafarayin murmushi wanda shikansa baisan yanayiba, sunan subeey yasoma furtawa yana maimaitawa,
Yadda tagaya masa sunan yatuna, saida ya lumshe edo saboda yadda ya tuna irin zakin muryarta, bakaramin dadi yaji muryar tamasaba, zaiso yakarajin muryar,
  Yana murmushi yaciro wayarsa, number subeey yayi dailing sannan ya kara a kunnesa,
Matar nan mai turanci a cikin waya taturanta masa cewa wayar a akashe take, a hankali yasauke numfashi, zuciyara cike da zargin ayya kuwa ba numbar bogice subeey tabashi ba, sai kuma yatuna dacewa shifa da kansa yakarbi wayarta yakira kansa kuma saida yaga tashigo sannan ya mika mata wayarta,    
     Kara sauke nunfashi yayi sannna ya jefar da wayar kan gado, ya mike tsaye yana kallon d'akin zuciyarsa cike dadamuwa,
  Yajima a tsaye yanata tufka da warwara, sai cen yajanyo sandarsa dake gefen gado  sannan yanufi toilet,

Wanka yayi sosai, sannan yafito duk da shi bakine amma saida fatarsa tayi kalli saboda tsabar hutu dayake samu dakuma kwanciyar hankali,
  Bakin mirror yazo ya shafa mai sannan yataje sumar dake saman kansa, yagyarata sosai,
    bayan yagama yajuya yakarasa bakin drowar ya janyo wata doguwar jallabiya yasaka, sannan yakoma kan gado yazauna,
  Kara janyo wayarsa yayi, yakara kiran number subeey, sai yaji tafara ring, kamar yasaka ihu dan dad'i, yayi saurin gyara zamansa kamar mai shirin kwasar karatu,...

Via OHW📚📲

HAKA SO YAKE 21-22

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_21- 22_*💕
                💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

❗bamu yarda wani ko wata ya juya mana littafi ba ta kowacce hanya, ko a cire mana wani Abun, Duk wanda yayi hakan Allah ya isa bazamu yafe ba‼

Tsaye yayi yana kallon kofar d'akin harta shige, sannan yad'aga kofin ruwan dake hannunsa ya k'worawa mak'wogwaronsa, bayan yagama sha yayi ajiyar zuciya, yana kallon cup d'in, sai yanxu yafara tuna irin fad'an dayayi nan take yaji kunya takamashi zuciyarta tafara was-wasi, "to ma meyasa yake fad'a akan subeey, me hakan yake nufi, kodai yafara sontane ..." dasauri ya girgiza kansa, "A,a nooo" yafad'a da karfi, kamar mai magana dawani, saikuma yakoma yana kallon falon, yaga bakowa, ajiye cup d'in yayi akan danni ya nufi d'akinsa jikinsa a sanyaye, 

Yana shiga yakarasa bakin gado ya zauna yana tuna kalamn Ahmad, a hankali yake sulaleya akan gado har yakai kwance, sannan yasauke nunfashi, yana kallon silin  d'akin, a sannu yasoma bud'e bakinsa yana fad'an "bazai yuyuba naso subeey, subeey ba kalata bace, bata dace da irin matan danake mafarkiba, Allah yasa zuciyata ta yarjemin da hakan" bayan yakarasa maganar yakara sauke nunfashi zuciyarsa cike da was-wasi
    Yajima a hakan sannan yatashi jiki a sanyaye ya cire tufafinsa ya fad'a toilet,

Subeey tunda tashiga d'akin dariya take, mamakine tsintsarsa daya mamaye mata zuciya, to mezaisa yaya abdul yanuna kishinsa akanta dan ya ganta da wani, kodai yafara sontane,  kamar kartayi maganar nan a zuciya, ai kuwa nan take hawaye suka zubo mata daga cikin edonta, a hankali tasa hannu tashare, bakinta narawa tasoma fad'a "meyasa nake yaudarar kainane, ninasan dacewa yaya abdul bazai tab'a sonaba, kuma nima yazama dole nadaina sonsa, " hannunta tad'aga tadafe zuciyarta sannan taci gaba dacewa "dan Allah zuciyata kidaina sakani tunanin  Yaya abdul zai sone, ninasan dacewa bazai tab'a sonaba" tafara dukan kirjinta a lokacin kuka marar sauti ya kub'uce mata, tana fad'an "dole nadaina sonsa wlh dole nadaina sonsa,".....

Via OHW📚📲

HAKA SO YAKE 19-20

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_19- 20_*💕
                💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

www.babymsh.blogspot.com

Dasauri ta biyoshi har suka shiga falo, tana cewa "haba yaya ka tsaya mana, ka tsaya don Allah".

Ya juyo a harzuK'e, "mezan miki idanna tsaya? Shi kenan ko wani jaki da doki kuma sai Yace yana sonki?"

Subeey Tace "nifa ba cewa yayi yana sona ba"
Abdul yakara d'aure fuska Yace "eeh yanzu kuma saiki maidani sakarai, toh idan ba yana sonki ba mezai saka ya anshi numberki?

Momie ta fito daga ɗaki jin hayaniyarsu "me nake shirin ji kuma daga shiryawa?" ya k'arasa inda momie take yana k'ara ɗaga murya "komi ma sai kiji momie, donta maidani sakarai a gabana zata baima wani saurayi numberta? Shikenan ni kullum cikin gadinta nake amma a hakanma ban iya ba?"

Momie daɗi ya kamata cikin fara'a tace "da alama dai yau suby taa samo mana suriki ko?"
    kamar yayi hauka jin kalaman momy yakara bata rai yace "ko tayi saurayi dai ko batayi ba abnda tayi bai dace ba"

Akafaice subeey ta tayiwa momy alama datayi shiru,
momie tayi murmushi tace "tohh ci gaba da faɗa mata ni kunga tafiya ta" momie tabar falon tana dariya

Yana tsaye shikansa yasara dalilin yin fad'ansa, sai masifa yake shikadai, dasauri Suby taje tad'auko mishi cup da ruwa mai sanyi, takarasa wurinsa, ta tsaya a gabasa suna had'a edo yayi shiru, tayi murmushi tana mika masa cup d'in, baisan lokacin dayakai hannu ya karb'a ba, sannan tace "ni bansan faɗan da kakeba Ya Abdul, saboda nayi saurayine kodan na bashi numba?.

Abdul Yace "Duka"

Subeey tayi ƴy'ar daria tace "ina ganin zuciyarka ke tafarfasa yaya kasha ruwannan zatayi sanyi" ta juya da gudu kawai ta shige kar ya k'ara mata wata masifar" tana dariya..

Via OHW📚

HAKA SO YAKE 17-18

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_17 - 18_*💕
                💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Abdul cikin sauri ya k'arasa wurin wannan kyakkawan saurayi yana bashi hak'uri, Anma hankalinshi sam baya jikinshi yanacen ya k'ura ma suby ido, itama kallonshi take tana ayyano haɗuwarshi a cikin zuciyarta.

Baima kalli inda Abdul yake ba ya fara tafiya zuwa inda suby take, sai lokacin suka lura da k'afarshi d'aya tana da matsala, wata irin tafiya yake yanad'an jefa kafar, harda sanda irin mai kyaunnan A hannunshi, A zuciyar sadeey tace "Allah mun gode maka da baiwar dakai mana"

Abdul ya tareshi da cewa "Yadai malam? sai baka hak'uri nake amma kayi shiru sai tafiya kake, idan baka hak'ura ba kaimin magana in biyaka mana" Saurayinnan Yayi murmushin daya k'ara bayyana kyaunshi Yace "Ayna daɗe da hak'ura, tun lokacin sa idona suka hangomin kyakkyawar k'anwarnan taka" yakarasa maganar yana nuna subeey

Damm!! Abdul yaji gabansa yafad'i,  kalaman saurayin sun sosa masa zuciya sosai, Ransa ya ɓace yace "ina ruwanka da k'anwata da zaka k'ura Mata ido? Da Allah malama shige muje" Yaja tsoki yana kokarin komawa cikin mota.

Suby zata buɗe mota Ta shiga sai dai taji maganarshi kusa da ita "Sunana Ahmad ne, da alama yayannan namu zafi ne dashi, amm basai na tsaya miki dogon bayani ba kinsan menene manufata, ki duba idan har kinga cancantata ki taimakeni da numbarki,"

Daga can waje Abdul Yace "zaki shigo mu tafi ko saina barki a wurinnan?" murmushi kawai tayi ta mikawa Ahmad wayarta ba tare da tace komi ba.

Yana murmushi ya  karbi wayar ya saka Mata number ɗinshi sannan ya kira, wayarsa nacikin aljihunsa tad'au ring sannan yakara yin murmushi Yace "yawwa gatanan tashigo, ngde sosae, sai kin jini" ta ɗaga kai kawai ta buɗa motan zata shiga"  har ya fara tafiya ya juyo, Yace "Har yanzu fa bakimin magana ba, ko kina rowar zazzaƙk'ar muryarkine"

Girgiza kai tayi tana murmushi tare da cewa "Sunana subeey" dariya Ahmad yayi mai sauti "Suna mai daɗi, kuma murya mai daɗi"

Subeey tana kokarin shiga mota tace "ngde mai daɗin baki" takarasa maganar da zolaya,

Ahmad yana dariya Yace "tun yanzu shaidar da zakimin kenan? " Bata bashi amsa ba sai dai dariyar da tayi ta shige mota, lokacin Abdul ya gama cika sosai,  zuciyarshi sai tafasa yake baice mata komi ba ya hizgi motan yayi gaba.

Daria ta fara yi ciki-ciki tana kallon yanda Abdul ya ɓata rai, a zuci yace "tohh miye nawa aciki? Saboda kawai ta bama saurayinnan numbarta, meyasa nake kishi, mtsw" Tsoki yaja,

Subbey tayi ƙk'ok'arin shanye dariyarta sannan tajuyo ta dubesa tace "yadai Yayana?" banza yayi ya ƙk'yaleta yana ci gaba dajin wani irin zafi a cikin zuciyarshi ganin da yayi sadeey sai murna take hankalinta kwance. Yasa yakara jan tsoki, jiyake kamar yakai mata duka,

Subeey kuwa farin ciki fal a zuciyarta, sunan saurayin tasoma tunawa domin sunan ya kwanta mata, Cikin Zuciyarta tace "ni yama sunanshi?" batasan maganar ta fito fili ba, cikin ƙk'uluwa Abdul Yace "saimu koma a tambayoshi" yaja uban burki ƙk'uu ya tsayar da motar.

Hannu ta saka tana rufe bakinta tace "Allah ya baka hak'uri yaya Abdul, ay yanzu komun koma ma yaa tafi" 
       
     "da bai tafi ba komawar zakiyi kenan? Wato Ke harkin samu damar da zaki kulaƙwani saurayi a gabana koh? Yanzu zai samu damar dazai rainani ina yayanki, sai wani iyayi kike da kilbibi ke kinga saurayi, shi kuma ya jawo wasu  miskinan k'afafu yazo inda kike harda tambayarki number, ke kuma da Allah yasa kunya ta miki karanci shine kika kwasa kika bashi" duk cikin zafin rai yake maganar, nanfa yaci gaba da masifa saikace wanda akayiwa wani laifi,

Jin faɗan bamai k'arewa bane, ya saka suby taja bakinta tayi gum tana saurarenshi, dariya na cinta har suka iso gida, ya riga ta fita daga motar ya shige ciki duk ranshi a ɓace..

Via OHW📚

Monday, 14 November 2016

Monday, 7 November 2016

HAKA SO YAKE 15-16

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_15 - 16_* 💕
                💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Tana komawa d'aki tatarar da momy zaune tana jiranta, da kuka tashigo d'akin, takarasa kusa da momy ta rumgume tana kuka tace "momy yaki saurarona, wai nafitar masa daga d'aki, nabarshi harya samu salamar zuci,," takarsa maganar tana kuka,
Momy tarika bunbuga bayanta "yi shiru subeey kiyi hakuri bari naje nasamesa "

Dasauri subeey tace "karkije momy, banason kowa ya yasakashi yayi hakuri dole, nafiso nida namasa laifi nizan bashi hakuri"

Momy tasauke nunfashi tace "toh shikenan, Allah yasa ya hkura, " tace ameen,

Nan dai momy taci gaba da lallashinta , harta samu tadaina kuka sannan momy tace "yanzu kitashi kije kiyi wanka, idan kika fito kizo ki kwanta insha Allah zaki samu natsuwa"

Tohm kawai tacewa momy, sannan tatashi tacire kayanta ta d'aura tawol tafad'a toilet, Saida tashige toilet d'in sannan momy tabar d'akin,

Bata jima acikin toilet d'inba tafito domin bawani dad'in wanka takejiba, saboda damuwar dake damun zuciyarta, bayan tafito, ko mekup bata tsaya yiba, mai kawai tashafa, sannan ta janyo wata doguwar riga tasaka, takoma kangado ta kwanta,
      Tunani kala2 yarika zomata, tayi nadama sosai da abinda tayi, kalaman da abdul yafad'a mata sune suka rinka dawo mata akwakwalwa, duk taji bata yiwa kanta adalciba, a hankali hawaye suka rinka zomata, muyar a saukake tasoma fad'an "kowane mutum datasa kaddara, toni wannan KADDARA TACE,  kuma tazomin a daidai lokacin daya dace, Ya Allah kabani ikon cin wannan jarrabawa, inaso namanta dashi a rayuwata, sonsa yafita a cikin zuciyata, dole na manta dashi, yazama dole nadaina sonsa" ita kadai take magana tana hawaye,

Sai kuma tayi Murmushi sanna ta furta "yaya abdul kenan, Allah yabaka wacca tafini" tana gama fada tashare hawayenta, sannan ta janyo filo ta gyara kwanciyarta, 
Tafi minti ashiri amma bacci yaki Zomata, sai rabon edo take tana kallon silin d'akin,

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Sai karfe biyar da rabi na yamma sannan tasamu tafito daga cikin d'akinta,

Falo tadawo tazauna ta kunna tv tana kallo, jitayi ana murza kofar d'akin abdul ana kokarin fitowa
A hankali take juyowa kamshin turarensa ya daki hancinta, ta lumshe edo tana murmushi, a lokacin taganshi yana kokarin fitowa sai kuma ta kura masa edo,
Shirin fita yayi cikin wasu kananun kaya, wadanda suka kara masa kyau sosai, 

Saida yagama rufe d'akin Sannan yajuyo a lokacin sukayi edo hudu da subeey, ya d'aure fuska, kamar wanda aka aikowa mala'ikan mutuwa

Murmushi subeey tayi tace " yaya Abdul za'a fitane"
Tsaki yaja, ko uffan baice da itaba, yafice yabar gidan, tabi kofar daya fita da kallo,

Bayan yafita ta girgiza kanta tana murmushi,  batason lokacin data soma yin hawayeba, ita dai kam yaza tayi da soyayyar abdul a cikin zuciyarta,,,,

Hakadai suka wuni, suka kwana agidan,  fuskarnan tashi a daure, gabaki daya yaki sakewa a gidan,

*Bayan kwana biyu*

Kwata kwata abdul
yadaina sakewa subeey fuska, duk ta masa magana komai sanyinta toshi damai zafi yake mayar mata da amsa, Duk tashiga damuwa, harta soma ramewa,

'Yan kwana kinnan da suka sanu matsala tunda safe yake fita yabar gidan baya dawowa sai da yamma,

Momy kuwa zuba musu edo kawai tayi tana kallonsu, tunda Subeey tahanata zuwa tabawa abdul hakuri, ita ala dole da kanta takeson tabashi hakuri,
     Yau subeey tatashi cikin tsananin damuwa, har saida tasomajin kanta na ciwo,
Saukowa tayi daga kangado takarasa bakin drowaer ta janyo wata doguwar riga tasaka sannan tafita tanufi d'akin abdul,

Yana tsaye a tsakiyar d'akinsa yana kokarin shirin barin gidan,  yad'auko turarensa yafesa,

A daidai lokacin subeey ta turo kofar d'akin Nasa tashigo, Suna hada edo ya yatsuke fuska yayi tsaye euri d'aya yana kallonta yaji dame tazo,

Taku tafarayi hartazo daf dashi, suna facing d'in juna, Durkusawa tayi har kasa, sannan tad'ago kanta ta kallesa, a daidai lokacin hawaye suka sauko kan kumatunta tace "shine kadai lafina dan nace inasonka ya abdul, to bakin daya furta so, a yanzu shizai furta baya so, yaya abdul bazan iya jurar ganin fushinkaba, ko zan rasa nunfashina nemai nema maka farin cikine a duk inda yake, Dan Allah yaya abdul kadaina fushi dani wlh najima dabawa zuciyata hakuri akan ta hakura dakai,  a yanzu so daya yarage a cikin zuciyata shine son yaya da kanwarsa, uwa daya uba daya, kuma kaima inason kakalleni da wannan fuskar, kayi hakuri yaya abdul.." kuka ya kube mata ta soke kanta kasa, taci gaba da kukanta,

Duban tausayi yamata, tayi matukar bashi tausayi, ajiyar zuciya yayi sanna  yasa hannu yad'agota ya mikar da ita tsaye yana murmushi " na hakuri, sister subeey, kuma a yanzu na yarda da maganarki, zan rika kallonki a matsayin kwanta ta jini, kidaina kuka kinji" yafada yana kokarin share mata hawaye,

Dadi taji harcikin zuciyarta a  hankali ta furta masa "nagode yaya abdul, amma ni sainaga kamar baka hakur.." Dasauri ya dora hannusa akan lips d'inta yace "shiiii, basai kin fad'aba nagaya miki na hakuri, idankuwa baki yardaba, mekikeson namiki wadda zai tabbatar miki dacewa na hakura"

Murmushi tayi sannan tace "kaje dani shopping yau kuma a yanxu"

Abdul yace "toshikenan jeki kishirya kizo muje" yakarasa maganar yana murmushi,

Takara share fuskarta tana dariya tafice tabar dakin cike da farin ciki,
Tana karasawa dakinta tafad'a toilet shap shap tayi wanka tafito, tazo tayi mek up, tayi kyau abinta, sannan tafito tanufi d'akin abdul, koda taje shima har yagama shirinsa,

A tare suka jero suka fito, momy tana zaune a falo taga sun fito, tabe baki tayi ta bisu da kallo sukuwa sai faman murmushi suke mata kwanin sha'awa, momy tace " yau naga ikon Allah, ayi fad'an ba'a sanar daniba, kuma a shirya ba'a sanar dani, ehhh lallai kuce kuncireni daga cikinku"

Subeey tana dariya tace "a a momy bahaka, ai tsakanin kanwa da yayanta sai Allah, ta juya gefen abdul tana kallonsa sannan tace "koba hakaba yaya abdul"

Abdul ya wangale baki " hakane fa kanwata"

Momy tadubesu tana dariya tace "to ina kuma zuwa haka"

Abdul yace "shopping zamuje"

Momy tayi Murmushi tace "toh Allah yakaiku lfiya yadawo daku lfy"
Su suka amsa da ameen suna dariya sannna suna fice sukabar falon,

Abdul ne yaja motar har suka karasa bakin plaza,  sannan suka fito, suka nufi cikin,

Sunyi siyayya sosai, sannan suka fito, a but abdul yasaka kayan sanna suka shiga mota,

Bayab sun shiga motar Abdul yana kokarin yin reverse yaji yadaki wani abu a bayansa, kashe motarsa yayi sannan yafito domin yaduba yaga meya daka,

Wata motace zata shigo wurin sukayi karo, kuma fitilar motar d'aya ta fashe,

A sannu bakin Abdul ya furta " ohh shett"  yana kokarin karasawa wurin mai motar,

Wani matashin saurayi ya bud'e kofar motar yafito ransa a bace yana shirin fara masifa, a daidai lokacin subeey tafito itama domin taga halin da ake ciki, a lokacin sukayi edo hud'u da matashin saurayin,  turusss yayi yana kallonta...

Via OHW📚📲

Popular Posts

]]>All content on thisblog are copyright protected and cannot be reproduced on other websites without permission.