New Post

Thursday, 13 October 2016

HAFSATUL KIRAM 7-8

[10:05, 4/9/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

              7⃣

Duk ya ketamin hijabi, da naga ba cikin hayyacinshi yake ba na gartsa mishi ciwo da sauri na tureshi na qwace, saiga momie ta shgo a rude na koma bayanta jikina na kyarma

Cikin takaici momie ke mishi magana "yanzu umar bzaka daina wannan halin naka b haryanzu? Kullum cikin rantsuwa kake da zaka daina anma har yau kaqi ka canja hali? Fada sosae take mishi anma baice komi b sai layi da yake daqyar yake daga idanu

Momie tace "bxanyi magana dakai ba cikin maye, idan kaa dawo dai dai zaka gamu dani ne, sannan ta qaraso wurina tana tmbyata meya faru?

Tsabar rudewa bata bari na bata amsa ba, har lokacin jikina kyarma yake bakina ya kasa cewa komi da sauri na juya nabar dakin ina qanqame da jikina ina kuka!

Ranar banyi barcin kirki ba, cikin dare na tashi na hada kayana tunda safe momie ta shgo dakina kafinta fita office ta iskeni gaban kayana ina hawaye!

Gaisheta nayi kaina a qasa ina qoqarin maida hawayena, taa dade a tsaye kafin tajaa numfashi ta fara magana "bzan hanaki tafiya ba hafsa damn shawarar da nayi kenan, anma kiyi haquri hafsat kimin alqawarin bzaki fadama kowah ba, daga mata kai nayi ina hawaye ta dafa kaina tace "Allah ya miki albarka hafsatul kiram,

Ta dade tanamin nasiha sosae tana bani haquri, nikam godia nake ga Allah da bai bawa ya umar sa'a a kaina ba! Ta saka driver ya kaini gda

Su momie sunyi farin ciki da dawowatah gidanmu don nima naji dadi sosae na dan samu natsuwa, ko kadan ban bari su momie sun gano damuwatah ba!

Lokacin daddy harya nemamin admission har motah ya siyamin saboda zuwa makaranta, duk da nace bzan iya drivn ba sai dai driver ya dinga kaini, don ko motah naqi in koya.

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[10:31, 4/9/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

            8⃣

Kwatam rannan ina kwance dakinah kiran momie ya shgo a wayata, ina dauka tace in sameta falon daddy

Zaune na iskesu momma da daddy, Aunty rabiatu, momie khadija da mijinta Alh basheer sai faruq daya sunne kai ya zauna samn kujera

A rude na gaishe da kowa gabanah na faduwa na samu wuri na zauna nima na sunnar dakai qasa

Daddy na ne ya kira sunana, a hankali na dago kai yaci gaba da mgn  "ga dan uwanki nan yaazo da maganar nemn aurenki, munyi farin ciki sosae, damn burinmu kenan mu hada aurenku da fatan kema bzaki qi amincewa ba!

Jikinah ya fara kyarma da sauri na dago kai ban iya tsaida hawayen firgicin dake zubomin ba, idan nace banison yaa umar naayi qarya! Kuma bzan iya qin umarnin iyayenah ba, anma idanna tuna abubuwan da suka faru kuma sai inji bzan iya amincewa ba!

Rasa amsar daxan basu nayi, kuka mai qarfi naji na qoqarin zomin, da sauri na tashi cikin sassarfa qafafuna na hardewa na tafi dakina na fada gado ina kuka!

Bnsan shgowarta b, sai dai naji ta dafani da sauri na tashi kaina a qasa, momie khadija ta fara magana cikin damuwah "bzanso mu takura miki ba muyi miki dole, idan har bakison faruq babu mai takura miki, anma alfarma nake nema a wurinki ki amince da aurennan don nasan ke kadai zaki iya taimakamin wurin canja faruq! Don Allah ki mnta da dk abnda ya miki ki amince da auren! Ko kinaso kicemin baki haqura da abnda ya muki ba?

Damuwah ce sosae a fuskar momie da bzan iya jure gani ba, share hawaye nayi ina murmushi nace na amince da wannan auren momie

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

Related Posts:

  • ABDUL WAHAB 14ABDUL WAHAB 14 ©Rabiatu sk msh            ®NWA Yana Shiga bedrum d'insa ya tura k'ofar yasa Mata key        bai samu damar zura sleepi… Read More
  • ABDUL WAHAB 10ABDUL WAHAB 10 ©Rabiatu Sk msh           ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION Sauke numfashi Abdul yayi sannan ya jingina da kujera, wayarshi ya ciro ya fara neman raheem, tun k… Read More
  • ABDUL WAHAB 12ABDUL WAHAB 12 ©Rabiatu sk msh           ®NWA A falo suka iske Sadeey ta 'bata ranta sosae, tana jinsu ta maida fuskarta gefe d'aya ta qara had'a rai ita a dole an 'bata … Read More
  • ABDUL WAHAB 13ABDUL WAHAB 13 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Daga fatima har Abdul babu wanda ya iya magana, duk jikinsu yayi sanyi da kalaman sadeey, maganar da hajiya ta mishi ce ta f… Read More
  • ABDUL WAHAB 11ABDUL WAHAB 11 ©Rabiatu sk msh          ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION Suna tafe suna hira, Fatima na nuna masa hanya, tun ahanya Abdul yasa Fatima taiwa Kadija waya gatanan zu… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts