[14:53, 4/16/2016] Rerbee'art sk♥: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
🎄
🎄🎄
🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄
🎄🎄
🎄
NA
Rabiatu sk msh
1⃣8⃣
Zaune take hafsatul kiram ta saka hotan Umar a gaba hawaye na zuba a idonta ita kadai ke magana cikin kalar ban tausayi "Yaa umar mai yasa zakamin wannan hukuncin? Zan iya jurar ko wanne hukunci daga gareka anma bnda wanda xai nisanta ni da ganinka? Meyasa ka tsaneni? Meye bkaso wanda nake da? Zan iyayin komi daxai sanyaka farin ciki, Rayuwatah ne kawai bn iya qararwa saboda inason inyita ne tare dkai! Anya kuwa akwai ranar da zaka so ni??
Daga bakin qofa taji an bata amsa da "A'ah, da sauri ta dago tana kallon deezy har lokacin hawaye na zuba a fuskarta, deezy taci gaba da magana "babu ranar da zumanah zai soki, ni kadai yakeso, kin gani ba? Igiyoyn aurenki da suke kanshi ba wani Abu bne, don bzaki taba mallakar zuciarshi da gangar jikinshi ba! Sunana deezy! Bzan taba yrda wata ta shga zuciar umar ba bayanni!
Hafsatul kiram bata tanka mata ba suka jiyo muryar Umar naa kiranta, tayima hafsatul kiram kallon sama da qasa ta juya ta fita! Zama tayi saman gadon tana ci gaba da kukanta!
A qofar fita falon sun jera shida deezy zasu fita momie ta shgo, sakin hannunta yayi ta matsa daga kusa dashi, wani irin kallo momie ta watsa mishi duk yaa rikice cikin in ina yace "momie deezy ce, ya kalli deezy yace "gaa momienah!
Harda duqawa ta gaishe da momie cikin jin kunyar kayan dake jikinta, fuskar momie ba yabo ba fallasa ta amsa sannan tace "deezy ko zaki bamu wuri muyi magana da d'ana? Tace "Tohm momie! Ta juya ta nufi hanyar fita, Umar Yace "ki jirani inzo, ta daga mishi kai ta fita!
Lurv my princess Amrah😘
♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[15:47, 4/16/2016] Rerbee'art sk♥: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
🎄
🎄🎄
🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄
🎄🎄
🎄
NA
Rabiatu sk msh
1⃣9⃣
Momie ta kalli Umar cikin mamaki tace "wai umar meka dauki aurene? Gidanka zaka shgo da wata macen? Har yau kai bzaka nutsu ba? Nayi zaton idan na aura maka hafsa zaka dawo hankalinka kasan me kake, anma kana cutar da yarinyar da babu ruwanta!
Yace "momie ki fahimceni nipa....! Daga mishi hannu tayi tace "naa riga naa gama fahimtarka umar, qarama tun wuri ka koyama kanka son hafsatul kiram, idan har bzaka iya bata haqqoqonta na aure ba nizan nema matah haqqinta! Da sauri ya kalli momie cikin mamaki! Ta daga mishi kai tace "tabbas nizan qwatoma hafsatul kiram haqqinta!
Juyawa tayi ta fasa shga wurin hafsatul kiram saboda yanda umar ya gama bata mata rai, tsaki taja tun farko sune suka sangarta shi da soyayyarsu wai danshi kadai ne suka haifa, ga hafsatul kiram nan da take ita kadai a wurin iyayenta hakan baisa sunqi bata tarbiya ba, yarinya mai nutsuwa, kawaici, haquri da biyayya!!
Umar kaasa motsawa yayi daga inda yake saboda tsananin bacin rai da tashin hankali, zuciar en maza taa baci kamar ta fasa qirjinshi ta fito!!
Juyawa yayi ya nufi dakin hafsatul kiram da batasan meke faruwa ba, fitar deezy momienta da daddy suka kirata suna fira cike da kewar gida, sai dai taji ya banko qofa cikin bacin rai, da sauri jikinta naa kyarma tace "momie, daddy zan kiraku! Bata jira mezasu ce ba ta kashe wayar!!
Miqewa tayi tsaye cikin tsoro jikinta na kyarma ya shaqota cikin zafin nama ya nannadeta cikin hijabin jikinta duk idanunta sun firfito sumane kawai batayi ba don tsananin tsoro!
Cikim daga murya yake magana "sau nawa zan fada miki ki daina shga tsakaninah da mahaifiyatah? Naa fada miki sau ba adadi bn sonki, bn qaunarki, na tsaneki! Baqin ciki yake qaramun ganinki a cikin gidannan! Bn taba tsanar abu ba duk duniar nan kaman yanda na tsaneki!
Jefar da ita yayi gefe guda ta fada saman gado ta saki wani irin kuka mai cike da ban tausayi! Juyawa yayi cikin fushi zaibar dakin yaci karo da momie tsaye bakin kofa!
Gefe yaja ya tsaya yanaci gaba da huci kamar zaki!
Lurv my princess Amrah😘
♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[17:05, 4/16/2016] Rerbee'art sk♥: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
🎄
🎄🎄
🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄
🎄🎄
🎄
NA
Rabiatu sk msh
2⃣0⃣
Momie tace "miye hka umar? Cikin huci idanunshi sunji jajir yake cema momie!
Kinji da kunnanki ba? Deezy kawai nakeso momie! Naa auri hafsatul kiram ne kawai saboda farin cikinki, anma bzan taba iya kallonta a matsayin matah ba! Raina qunah yake a duk lokacinda na tuna wai itace matatah hkan na cutar da zuciatah! Na auri hafsatul kiram saboda umarninki, kinyi farin ciki ba? Anma hkan bzaisa in zauna da ita a matsayin matah ba!
Ya juya ya fita fuuuu kamar mai shrin tashi sama! Da sauri hafsatul kiram ta tashi ta jawo akwati ta fara hada kayayyakinta! Momie ta qaraso inda take cikin sauri har tana hardewa tace "me kke shrinyi hafsatul kiram? Daina zuba kayan tayi sannan ta dauki jikkarta ta rataye kanta a qasa tana hawaye tace "gidanmu zan tafi momie, ni kadaice matsalar yaa umar! Bzanso in sakashi a damuwah ba, qara in tafi inyi nesa dashi!
Momie tace "kina nufin kin haqura dashi? Hafsatul kiram tace "naa haqura da yaa Umar momie, zam barshi yayi rayuwarshi da wacce yakeso! Momie ta dafa kafadarta tace "son da kke mishi pa? Shru hafsatul kiram tayi, Momie tace "duk son da kke mashi zaki tafi ki barshi??
Tace "Inason yaa umar momie, anma idan har naa kasa sakashi farin ciki bai cancanci kullum in dinga quntata mishi ba, yaa fada da bakinshi ba son ganinah yake ba! Momie banison abnda zai batama yaa umar rai! Ta juya taci gaba da tattara kayanta!
Momie tace "nasan kinyi haquri hafsatul kiram, kina da matuqar biyayyah! Naa kasa sama miki farin ciki a rayuwar aurenki, karki tafi kibar umar yana da buqatarki, naayi miki alqawarin zan nema miki 'yancinki anma don Allah karki tafi!
Rumtse ido tayi yanda momie ke lallashinta, bangare daya kuma ga farin cikin Umar da tsanar daya mata! Bataso ta tsaya wani tunanin dazai karyar mata da gwiwa, taa kasa hada ido da momie saboda wata irin kunyarta da takeji!
Kanta a qasa daqyar maganarta ke fita saboda tsananin kuka tace "kiyi haquri momie naa kasa zama suruka ta gari a gareki, naa kasa zama matar da danki zaiyi alfahri da ita! Kiyi haquri momie anma bzan iya ci gaba da cutar da zuciar yaa umar ba! Nice matsalarshi, idan na barshi xaiyi farin ciki, hakanne burinah!
Ta dauki akwati da jikkarta a rataye ta nufi kofa!
Lurv my princess Amrah😘
♥♥Rabiatu sk msh♥♥
0 comments:
Post a Comment