New Post

Friday, 14 October 2016

HAFSATUL KIRAM 38-39

[5/1, 10:54 AM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

         3⃣8⃣

Momy tayi tambaya meya faru dasu, a lokacin umar yana kwance bazai iya mata bayaniba,
   Bayan awa shida umar yafarka, kuma yasoma samun sauki, zafin da zuciyarsa takeyi ya rage sosai,
   Bayan ya farfado momy take tambayarsa meya faru dasu,
   Nan ya kwashe komai yagaya mata,
  Momy tace "wannan wace irin maccice, saikace batada imani, Allah yakiyaye gaba"
   Umar yace ameen,
 
Hafsatul kiram shiru shiru kakeji bata farkaba, harkusan dare, nan kuma hankalin momy dana umar yakara tashi, gashi gorar jinin da aka kara mata harta kare, amma hafsatul kiram shiru,
 
  Momy da umar suna zaune a gefen gadon hafsatul kiram misalim karfe goma nadare,
   A firgice hafsatul kiram ta sandara ihu, "wayyoo zasu kasheni, ya umar kacceceni" ta tashi da karfi,

Momy ta riko ta tana kuce kuce,  momy tace " ke hafsat momy cefa, kibude idonki kiganni"

A hankali hafsatul kiram ta bude idonta, suka hada ido da momy nan tafashe da kuka, ta rungume momy,

  Momy ta kankameta tana shafar bayanta "kiyi shiru kidaina kuka, insha Allah komai yazo karshe, kinji"
  
Hafsatul kiram tana shanshekar kuka ta share hawayenta, tafito daga jikin momy, momy tace kikoma kangado ki kwanta,

   Momy ta rika hannunta, kafin sukara bakin gado, taji kanta na sarawa, kamar zai fita, wani irin zafi takeji,
  Jiri yafara dibarta, tana hannun momy ta sulale ta fadi kasa,

   Tashin hankali nagano karara a fuskar umar, momy tayi sauri rikota tana jinjigata amma ina ta suma, a gigice momy tacewa umar "jeka kirawo likita"
  Umar yafi da gudu yaje yakira likita,
   Likita yazo yana dundubata yaga komai da sukayi mata normal, bawata matsala,
  Ya juyo ya kalli umar yace " batada wata matsala kawai shock ne ya dibeta amma ba wata matsala a cikin aikin da mukayi mata, likitan yadan dakatar da maganar sa, a lokacin yadaura hannunsa a kanta ya bude idonta daya, sannan yasake dora hannunsa a tsakanin wuyanta da kirjinta, sannan yaci gaba dacewa "karku damu bawata matsala insha Allah zuwa ajima zata farka, kufita waje kubata lokaci yanzu tana bukatar hutu"

  Jikinsu ba wani kwari suka tashi suka fita tare da likita,

Acen kuwa gefen deezy, a ranar sunsha dukan bala i a gurin yan sanda, saida sukayi musu likis, suka galabaita sannan suka daina dukansu,
   Da Kuma  zancen gobe za'a makasu a gaban kuliya wato kotu,
   ( su deezy ansha wuya 😂😛)..

Lurv my princess Amrah😘

❤❤Rabiatu sk msh❤❤
[5/1, 10:54 AM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

             3⃣9⃣

Washe gari,

Hafsatul kiram tafarka, cikin kwanciyar hankali, umar yaje gida yakawo musu kayan break
  Momy ta hada mata tea, mai kwairi tarika bata abaki, aka samu tadan sha, daga nan kuma takoma bacci,

  9:00am umar yakoma gida yayi wanka, sannan yadawo asibiti yasanar da momy cewa zaije koto,
  Momy tace Allah yabada saa,
  Umar yace "ameen, saina dawo, harya yabi hanya saikuma yadawo yace "inda wani abu da kuke bukata sai akirani asanar dani "
   Momy tace "toh,"
Tsaye yayi yana kallon hafsatul kiram, wani mugun tausayinta yakeji,
  Cen dai yajuyo ya wuce koto,

Koto tacika makil,
  Deezy da sauran kattinta  duk suna cikin kuliya,
  Lauyan gwaunati yatashi yana bayani sosai daga karshe yakare da cewa "wannan shari ar bata bukatar jan dogon lokaci, domin wadanda ake kara sun amsa laifinsu na yunkurin kashe wata, saboda haka ina rokon wannan koton datayi gaggawar yankewa wadan nan mugayen mutane hukunci, lauyan yadan rusuna kafin yace "nagode ya mai girma mai sharia, "yana gama fadan haka yakoma yazauna,

  Alkali yadan tsaya yana yan rubuce rubuce, kafin yadago kansa yace " abisa hujjoji da kuma kwararan dalilan da lauyan gwaunati yabayar, koto ta yankewa wadan nan mutane hukuncin zaman gidan yari shekara ukku, tare da horo mai tsanani, sannan kuma babu beli"

  Deezy ta kwalla ihu a cikin koton, tadafe kai tana kuka, cike da nadama, tayi matukar danasanin abinda ta aikata,

   Nan alkali ya daki tebur nan kaji koton tadau sautin "kotttt" kowa yamike tsaye saida alkali yafita sannan kowa yafiya,

aka ja su deezy aka wuce dasu gidan yari,

   Umar kuwa yayi godiya ga lauyan gwaunati sannan yadan ciro wasu yan kudade yabashi,  sannan yajanyo motarsa yadawo asibiti,

   Hafsatul kiram na farke yashigo dakin,
  Sukayi ido hudu, yasakar mata murmushi kafin yakarasa gurinta yace "ya jikin" tace "dasauki" yace "Allah yakara sauki " tace "ameen "

Satinsu daya a asibiti, hafsatul kiram tasamu kulawa sosai a gurin umar, duk abinda takeso siya ke mata, ita kanta mamaki take yadda taga umar yanuna damuwarsa sosai akanta,

saida hafsatul kiram taji sauki sosai sannan aka sallamesu,  suka dawo gida ..

Lurv my princess Amrah

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

Related Posts:

  • A YINI ƊAYA 19-25[10:42am, 13/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 26-33[5:18pm, 16/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 26-33[5:18pm, 16/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 34-40[12:31pm, 20/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 34-40[12:31pm, 20/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts

 
seo